Episode 1

542 26 1
                                    

*KWARYA TA BI KWARYA*

*NA SADNAF*

*BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM*

*PAGE 1*

*Past*

Iska mai k'arfi da kwanun gidan dake ta Kara yasa Sulaiman dake kwance a Gefen Hanne mik'e wa da sallati a bakinsa.

dan Karamin cocilan dake gefen gadon ya lalubo ya kunna dan sosai iska ke buga dan Karamin window nasu kafin ya kunna cocilan din Hanne dake kwance a gefensa ta tashi zaune itama bakinta d'auke da sallati tana "Abban Ameera Allah yasa ba ruwan sama za'ayi ba."

Rufin kwanun dakin dake dagawa saboda iska yasa ta sake sakin sallati a daidai lokacin da sulaiman ya kunna cocilan din  ya haska su Ameera dake kwance a kasa ya Kalli Hanne Yana "Tashi ki mai dasu kan gado bari na fita waje na d'auko bokitan da zamu tari ruwan"

Yayi waje Yana Jin kamar yayi kuka dan tunda aka shiga damuna basu da wani kwanciyar hankali idan dai za'a yi ruwan dare dan rufin dakin ba Karamin yoyo yake ba dan idan har akayi ruwa da yawa  haka dakin zai cike da ruwa har sai ya kusa tadda gadon su dake jikewa jagab da ruwa.

Idan baya nan Hanne ke fama da kwashe ruwan tana zubar wa a waje.

Yanzu haka fadi tashin da yake na yadda zai samu kudi ne ya canza Kwanun gidan.

  burinsa kullum bai wuce Allah ya kawo masa hanyar da zai samu kudi da har gobe ya kasa samun kudin da zai ishe shi ya siyi kwanun da zai rufe dakin.

Ko da ya fita kamar iska zai d'auke shi dan saboda karfin iskar har bokitan dake ajiye a gefe sunyi nasu wajen ga kasa daya cike masa ido saboda karfin iskar kafin ya Kai hannu ya d'auko bokitin dake wajen k'ofar fita.

Iska ta d'auke kwanun rufin dakin nasu sallati yake da k'arfi kamar yadda Ya Jiyo Hanne na "Shikenan Abban Ameera asirin mu ya tonu"

Bokitin hannun sa ya saki  ya cigaba da sallati ya koma cikin dakin da sauri a daidai lokacin da ruwan Saman ya sauko da balain karfin sa.

Yana Isa bakin kofa yaji Ihun su Ameera dan ruwan kamar har da kankara hannu ya sa ya karbi Sadeeq daga hannun Hanne da su Ameera suka rike kafarta gam dan ruwan Saman ba Karamin jibgar su yake ba ta kuma tsaya cak bata motsa ba balle ta samu mafaka dan iya dakin nasu ke da rufin kwanu dan Karamin kitchen din nasu da bandaki ba wani rufi.

Gashi wajen karfe biyu ne na dare balle su nemi wajen da zasu fake.

Hanne sai kuka take a cikin ruwa tana rungume da su Ameera dake ta tsalla ihu kamar yadda shi ma ya rungume Sadeeq ya b'oye shi a kirjinsa.

Ba gidan da zasu  iya zuwa a yanzu su fake dan ko sun buga gidan makotansu ba lailai suji su ba.

Yadda ruwa ya cike dakin  yasa ya cewa Hanne ta dora su Ameera kan gadon dan a cikin ruwan suke tsamo tsamo.

Tana dora su akan gadon ya bud'e wadrobe dinta mai k'ofa biyu ya jawo wani zanin gadon ta da yasan ko ya rufe su jikewa zasu yi amma haka ya d'auko zanin gadon mai kauri kamar towel ya rufe su Ameera,da Yana rufe su ruwa ya jike zanin gadon.

Hanne na kuka zaune a saman gadon kamar yadda shi ma ya zauna a gadon  rungume da Sadeeq da bai fi shekara uku ba ruwan yayi ta dukan su tsawon awa daya kafin ruwan ya fara tsagaitawa iska da sanyin ruwan yasa hakoran su haduwa suna rawar sanyi.

Ruwan na d'aukewa hannu na rawa ya bude wadrobe din ya hau lallubo kayan su Ameera da ya samu basu jike sosai ba ya mik'awa Hanne da idonta ya kumbure saboda kukan da ta sha,baya san ma yi mata magana dan gani yake shi ma zai iya fashewa da kukan dan a yanzu sai dai su tafi gidan gwaggo Mahaifiyar sa da yake b'oye mata halin da yake ciki a yanzu ita kadai ce zata iya taimaka musu.

KWARYA TA BI KWARYA Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin