*SAFWA*

          Tana fita 3 houses away da gidan ta ƙarasa get ɗin gidansu,gida ne ɗan dai² na masu rufin asiri saboda kou a GRA ɗinma akwai gidajen da ake samu da yawa ba na masu kuɗi can ba,mahaifanta ba wasu shahararrun masu kuɗi bane,kawai dai su suna da son yin ɗagen rayuwa ita da mahaifiyarsu,akai kai inda Allah bai kai kaba,musamman ta fannin rayuwa suna da son shigewa masu kuɗi,asalin mahaifinta haifaffen garin Bichi ne ta Kano,aiki ya dawo dashi cikin garin Kano,sunanshi na yanka Ridwan,aikinsa koyarwa ne a jami'ar Bayero a ɓangaren Engineering,bayan sana'ar koyarwa yana ƴan buga²rsa kuma,duk dan a samu asiri ya rufu,sai dai mutane sunfi saninsa da Alh Lirwanu,matarshi ɗaya ce tak me suna Murjanatu,suna da yara 5,Safwa itace second born kuma ita kaɗai ce mace,yayanta namiji ne Muhammad Awwal,tana da ƙanne 3 dukansu maza,Bilal shi yake binta kuma shi baida hayaniya,ka ganshi baza ka taɓa cewa ɗan gidan bane,saboda sanyin halinsa irin na mahaifinsu,sam bai raina rayuwar da ya taso yaga kanshi a ciki ba,bai raina gidansu da abunda suke da shi ba,babu ruwansa da shisshigewa ƴaƴan masu kuɗin area ɗinsu,bayan shi sai Usman,sannan sai ɗan autansu Aasim. Tana buɗe ƙofa ta shiga madai²cin compound ɗinsu da bai wuce ya ɗauki 3 cars ba,ƙofar parlonsu ta ƙarasa tai sallama,ƙatuwar matar dake zaune tai himm saman kujera ta amsa tana faɗin "a'ahh! Har kun dawo daga kai ɗinkin?" Safwa data zauna ta ajiye vail ɗinta tace "sannu da gida Umma.. Ehhh mun kai" Umma tace "toh nawa ne kuɗin? Gara in san ta yanda zan amso miki kuɗin gurin Babanku in baki ki adana.. In Allah ya taimakemu kika fito a bikin nan sai ki samo mijin nunawa sa'a,na aurar dake gidan da za mu huta,muma muje inda za mu dandali arziki" dariya Safwa ta fashe da shi tace "Umma tou ai bai faɗa ba,ya ce dai zai duba kayan sai ya sanar da Baniynah.. Kuma tunda bamu da nisa,3 houses ne tsakaninmu ai zan mata maganar,kou be faɗa ba nasa tai masa maganar saboda na sanar miki da wuri" Umma tace "ehh haka ne.. Tou Allah ya kaimu" Safwa data ja wayarta ta amsa da ameen,lokaci ɗaya tana kallon parlonsu tace "wai Umma naji gidan shiru ina su Aasim?" Umma tace "na kaɗasu islamiyya tuni,suna neman samin ciwon kai sunƙi bari na samu salama" Safwa ta gyaɗa kai tace "alright! Bari na kai jakana ɗaki na sauko.. Wai ku yi batun naku ankon ne? Na ji baki ce komai ba,kou zancen kai ɗinki ma baki yi ba" Umma tace "yana nan an kawo yana ɗakina,ai ni banma bi takaina,ke dai nake so ki fita,har kuɗin makeup na sallameki tukuna" Safwa tai murmushi tace "tou ai kuma Umma kema ya kamata ki bada naki a ɗinka,bikinfa sake tahowa yake,duka baifi 3 weeks ba nake jin" Umma tace "maa sha Allahu.. Tou amma ba gulma ba,zo ki zauna muyi maganar nan" samun guri Safwa tayi kusa da Umman,Hjy Murja tace "ya batun lefe ne wai? Nifa har yanzu banji ana cewa za'a kawo ba" Safwa tace "nima dai banji ba gaskiya" Umma ta kama baki tace "tou ki tambayi ƙawayen naki mana muji yaushe za'a kawo.. Ga biki sai matsowa yake amma anyi shiru da zancen akwati,kou dai sadakar ƴar za suyi ai sai haka.." Dariya Safwa ta fashe da shi ta tashi tana cewa "kai Umma" Umma tace "wallahi abun ai da mamaki da ɗaure kai kou?" Safwa tace "haka ne kam.. Bari na ajiye na sauko" Umma tace "tou je ki kai" daga haka Safwa ta wuce saman bene,Umma dai ta kama baki tana ta'ajibin al'amarin a ranta ita kadai.

*MUNIBA*

            Kiran sallar maghreeba shi ya tashi Muniba da Baniynah sukai bedroom ɗinta tare,suna shiga Muniba ta ajiye tsadadden Z flip wayarta irin na Baniynah sak da vail ta wuce bathroom ta ɗauro alwala,Baniynah ta tashi ta shiga tayo alwala also ta fito,kusan tare suka tada sallah,suna idarwa bayan sun yi azukarul-masa'a,Muniba ta tashi ta ɗauki wayarta dake ajiye tana faɗin "Sweet! Bari naje naima Mama sallama zan wuce gida,kafin Mami ta kirani taji ban tafi ba" Baniynah tace "alright! Muje na rakaki" tare suka fito bedroom ɗin suka isa ɗakin Mama,sai da suka fara yin knocking kafin Muniba ta buɗe ƙofar ta shiga da sallama,fuskarta ma'abociyar fara'a a sake,Mama na kallonta da murmushi tace "ba dai tafiya za kiyi ba?" Muniba ta durƙusa kusa da Mama dake lazumi tana faɗin "ehh Mama zan tafi" Mama tace "a'ahh! Amma dai kya bari kiyi dinner kafin ki wuce kou? Ki bari idan akai isaa sai ki tafi" Muniba tai murmushi tace "gara naje gida Mama,idan Mami taga shiru za ta kirani,kuma bance mata zan jima ba" Mama ta gyaɗa kanta tace "ehh haka ne.. Tou shi kenan ki gaida Mamin kafin muyi waya,kice mata kawo kayan nan sun yi magana,maza ne za su kawo ranar Friday.. Kou da yake ma dai idan an idar da sallar isha yanzu zan kirata muyi maganar,batun kayan anko zan kawo mata da kaina" Muniba na murmushi tace "tou in sha Allah" Mama tace "Baniynah! Kije dining akwai abu na nan a leda na ajiye,ki ɗaukoma daugher" dariya Muniba ta fara tace "Mama abun kaiwa baki ne?" Mama tana girgiza kai tace "a'a na kaiwa ƙeya ne,ke dai kin zama acici daughter,ana yin magana za ki fara tambayar abun ci ne? Me kike son ki zama?" Baniynah tace "acici mana" Muniba tai dariya da ya bayyana kyawawan jerarrun fari tas ɗin haƙoranta tace "na gode Mama.. Allah ya saka da alkhairi" Mama ma tai dariyar tace "nice da godiya daughter,kin cece ni kin bani hutu yau.. Allah yai miki albarka" Muniba ta amsa da "ameen.. Sai da safe Mama" Mama tace "ki gaida gida,a gaida Abba da Khalifa" Muniba na dariyar shaƙiyanci tace "surukinki?" Mama tace "a'a ni ɗa nake yi da shi wallahi" Muniba tace "zai ji in sha Allah" daga haka suka fita ita da Baniynah,dai² bedroom ɗin Khalidah Muniba ta tsaya tai knocking kafin ta buɗe kofar ta ɗan leƙa tana faɗin "Yaa Khalidah sai da safe na wuce gida" Khalidah dake waya da fiance ɗinta,maganarta ƙasa² kamar ba ita kaɗai ce a ɗakin ba tace "Sweetheart! Tun yanzu?" Muniba tace "wallahi ban ce da Mami zan jima bane,kuma gashi har anyi maghreeba" Khalidah tace "ohh! Tou ki gaida gida,a gaisar min da Mami da Yaa Khalifa" Muniba tace "za suji in sha Allah.. Bye" Khalidah tace "ok bye.. Sai mun yi magana anjima" Muniba tace "alright!" Sannan ta wuce tabi Baniynah data tafi downstairs tuni,tsaye ta ganta da leda a hannu tana jiranta,suna fita balcony sai ga wani kyakkyawan matashi da kana kallonsa za kaga kamar da yake da Baniynah,dukansu suka saki fuska ganinsa,Muniba tana ɗan murmushi suka haɗa baki ita da Baniynah gurin faɗin "Yaa Mubasshir sannu da zuwa" tsaiwa yayi yana buɗa idanuwa sosai yace "a'ahh! Ƙanwata kin zo amma babu wanda ya kirani ya faɗa min?" Tai murmushi tace "good evening Yayanmu" yace "evening.. How are u? Ya gida dasu Mami?" Tace "suna lafiya" yace "ba dai har tafiya za kiyi ba" Muniba ta gyaɗa kanta tace "ehh wallahi ai na jima" yace "alright! Ki gaida gida da Mami tou,in sha Allah zan shigo gaisheta" Muniba tace "Allah ya kawoka lafiya" ya amsa sannan sukai sallama,yana tafiya suka ƙarasa parking lot,motar data zo ciki ta buɗe ta shiga driver seat,Baniynah ta miƙo mata ledarta,ta karɓa tana cewa "thank u dear,sai na isa gida ma yi magana online" Baniynah tace "alright! Allah ya kaiki lafiya,sai mun yi waya anjima" Muniba tace "ameen.. Thank u" daga haka taiwa motar key,Baniynah na ɗaga mata hannu taja ta bar gidan.

*WAZEER*

     Yana gama magana da Safwa bayan ya katse kiran ya ɗan lumshe idanunsa,kamar wasa bacci ya ɗaukeshi a gurin,ba shi ya farka ba sai ana kiran maghreeba,a kasalance ya tashi jikinsa duk yai nauyi,bedroom ɗinsa ya wuce kai tsaye ya buɗe,gidan yana nan dai kamar shekarun baya,sai dai yanzu an sake komai na part ɗin tun daga kan paint har furniture,tun zuwansu Dad yasa akai gyara tare da canja musu komai,suna da me aikinsu namiji dake musu shara da goge²,girki ne dai kawai ba ya yi,wani lokaci gurin Daada suke cin abinci kou su siya eatry idan abincin gidan bai musu ba,wanka da alwala yai saboda ya samu jikinsa ya saki,ya fito cikin shirinsa hannunsa riƙe da keys na gidan da na motarshi,rufe gidan yayi kafin ya wuce ya fita masallaci,bayan an idar da sallah yana fitowa masjid,Dad da yake bayanshi baima kula da shi ba saboda yana sauri yaje gurin Mimi ya kirashi "Wazeer!" Muryar Dad yasa yai saurin waigawa yana faɗin "yes Dad" Dad yana kallonshi bayan ya gama fitowa masallaci yace "where are u going?" Ɗan sauke numfashi yayi strictly yace "zanje gidan grandma ne" Dad yana kallonshi yace "me ake a can ɗin?" Wazeer ya kalli Dad kafin ya ɗan girgiza kanshi yace "nothing.. Just want to go and see my Mom" kallonshi Dad ɗin nasa ya ɗan yi kafin ya saki siririn tsaki yace "ok! Tunda babu abunda ake muje gida za muyi magana.." Wazeer ya ɗan waro ƙananun idanunsa,bai dai ce komai ba yabi mahaifin nasa suka wuce gida,suna shiga gida Dad ɗin nasa ya wuce part ɗinsu yana biye da shi a baya,ya zauna saman kujera ya ɗauki ƙafarshi ɗaya ya ɗora kan ɗaya,yana kallon Wazeer da ya zauna opposite da shi yace "maganar service ɗinka,na gama duk abunda ya dace kuma na samu an barka a nan Kano,da kun fito camp kullum za kaje ka dawo gida ba sai ka kwana ba,kafin ka gama in sha Allah zan nemar maka BUK kai joining PhD" shiru Wazeer yayi yana ta sauraren Dad ɗin nasa,a hankali ya gyaɗa kanshi yace "ok Dad" Dad yace "get set ranan Monday za ku shiga camp,sai ka sanar min duk abunda kake buƙata kafin lokacin,Allah ya taimaka ya bada sa'a" rasa bakin magana Wazeer yayi,a tarihin rayuwarsa bai taɓa yiwa mahaifin nasa musu ba,shi mutum ne dake da biyayya,ba ya gajiyawa da amsa duk wani umarnin da mahaifin nasa zai bashi" Dad yace "shi kenan na sallameka" gyaɗa kanshi Wazeer yayi kawai,haka nan duk jijiyoyin jikinsa sukai sanyi,ba abun ya tashi ba yace zai fita,ya san Dad zai bi ƙwa²f dan bai manta tsakin da yayi masa ba da yace zai je gidansu Mimi,haka yaita zama ya kasa tashi,Dad ya ɗauki remote ya shiga canja channel,kamar bai yi wata magana ba...

          #Yau dai na sallameku da wuri.. Kafin a fara cigiyata.. Me Dad yake nufi ne? Shi kenan ɗa bazai je gurin mamarshi ba? Shi haka akai masa?



*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

   _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
   _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa,  yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

*Infection*
    _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_

    _Muna sayar da supplement gangariya  irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*



#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.

WAZEER!Where stories live. Discover now