*HAMOOD*

       Yanda ya fizgi motar ya matuƙar tadawa Abuu Turab hankali,a tsorace ya runtse idanunsa numfashinsa na fita heavily,can bayan wani lokaci ya fashe da azababben kuka me ƙarfi,har shiɗewa numfashinsa yake yana dawowa,bakinsa na ɓari muryarsa na trembling yana kiran sunan "Mi.. Mim.. Miiiii!" Dole ka kalleshi ya baka tausayi duk taurin zuciyarka,Hamood da zuciyarsa ke wani tuƙuƙi,yana barin ƙofar gidan ya ɗaga kanshi ya kalli mirror,yana hango yanda Yaa Umar ya fizgo Hoor ya sauke ajiyar zuciya tare da ƙarawa motarshi wuta ya bar link ɗin,dama bai da niyyar yai mata komai,just ya tsoratar da ita yasa taji shakkarsa da shayin kuma bin hanyarsa. Daga Jambulo kou gidansu bai nufa ba saboda yanda ranshi yake ɓace,yawo yai tayi a titi daga nan zuwa can ya rasa takamaiman abun yi,yana jin yanda ɗansa yake kuka yana kiran sunan Miminsa amma bai kulashi ba,duk yanda yake jin zai iya yi masa shiru har zuwa sanda zai gaji yai shiru,lokacin da kukansa ya dameshi dan kansa yai parking gefen titi,a hankali ya juyo yana kallonsa idanusa a rine da ɓacin rai yace "come my dear" ya buɗe masa hannu,girgiza masa kai Abuu Turab yayi da muryar kuka yana komawa cikin kujerar motar yace "ni.. Ni.. Gurin Mi.. Mim.. Miiiii na zan.. Jeee" yai maganar a kakkatse har sannan numfashi ya ƙi dai²ta,Hamood ya dunga kallonsa for about 2 minutes ya kasa cewa komai,can ya kauda kanshi yana sauke numfashi da calming kanshi,a hankali ya juyo ya tsare ɗan nasa da idanu yace "Wazeer!" Kasa amsawa Abuu Turab yayi saboda kuka,Hamood yace "ka fi son Mimi akan Dad?" Saurin gyaɗa kanshi Abuu Turab yayi,Hamood ya dunga kallonsa kafin ya gyaɗa kansa shima,yana sauke wani numfashin ɓacin rai yace "ka fi son zama da ita akan ni?" Nan ma ya sake gyaɗa masa kai da sauri,Hamood yai murmushin takaici kafin ya ɗauke kanshi ya tada motar suka ci gaba da zagaye gari,zuciyarshi na saƙa masa abubuwa da yawa,akan ya bar ɗanshi hannun Hoor gara koma meye ya aikata,sallah kawai yake iya tsaiwa yayi sai abincin da ya siya masa,dake ya galabaita saboda kuka bai iya yai musu ba yaci,yana gamawa babu ɓata lokaci ya fara hamma,Hamood bai nufo gida ba sai dare lokacin da ya tabbatar bacci me nauyi ya ɗaukeshi,a hankali yana kallon yanda yake sauke numfashi da ajiyar zuciya a bacci yace "let's see idan na bar ƙasar da kai waye zai kirani yace sai na dawo da kai.. I promise u that baza ka sake ganin kowa ba,ur Mom and kowa ma,sai na tabbatar na cire maka tunanin komai daga ranka,sai nai wining zuciyarka,sai na sa ka manta da kowa,except ni mahaifinka.." Daga haka ya tada motar ya nufi Tudun wuzirci,Hamood na yin parking ya sauko tare da zagayawa ya buɗe gefen da yake ya ɗaukoshi yasa a kafaɗarsa,abunka da farin mutum tsabar kukan da yayi yau idanunsa sun kumbura,haka ma fuskarsa tai jaa,banda sauke ajiyar zuciya babu abunda yake akai²,kai tsaye cikin gida ya wuce da shi,ya yi sa'a yauma Abba ba ya zaure,da alama ya fita babu jimawa,sai mutanenshi kawai suna ta hira,part ɗinsa Hamood ya wuce ya buɗe ya shiga,a parlour bayan ya rufe ƙofar da key ya kwantar da Abuu Turab ya nufi hanyar bedroom ɗin ɗan nasa,kayanshi ya shiga haɗawa cikin luggage da sauri²,yana yi yana kallon agogon dake ɗaure wrist ɗinsa,yana gama packing up kayan ya tashi ya fita da su parlour,sannan ya koma master bedroom ɗinsa yai wanka ya shirya cikin farin long sleeve da black trouser,kou da ya fito yaga har sannan yana bacci,a hankali ya ƙarasa ya ɗaukeshi,ɗayan hannunshi kuma luggage ɗin kayansa,ya tsaya bakin ƙofa ya rufe gidan then ya nufi ɓangaren Daada,dai² zai shiga ɓangaren ya haɗu da Salisu,ya kalleshi a hankali yana ɗan tsayawa,Salisu ya ɗan rusuna yana faɗin "barka da fitowa ranka shi daɗe,kawo jakar na riƙe maka" Hamood na kallonsa fuskarsa ɗaure yace "yawwa Salisu,Isiyaku fa?" Salisu yace "yana waje ranka shi daɗe,a kira maka shi ne?" Hamood ya ajiye luggage ɗin hannunsa yace "no! Karɓi Wazeer ka kai masa shi,kace ya jirani ina nan fitowa yanzu" da sauri Salisu ya karɓi Abuu Turab da Hamood yake miƙa masa,yace "ranka shi daɗe kawo akwatin" Hamood yace "no jeka kawai,bari na shiga gurin Daada na fito" Salisu yace "tou ranka shi daɗe,a fito lafiya" daga haka ya tafi da Abuu Turab dake ta bacci,a gaggauce Hamood ya shiga da sallama,Daada dake tare da hadimanta suka amsa suna yi masa barka da shigowa then suka tashi suka basu guri,ya ƙarasa ya zauna fuskarshi babu walwala sosai suka gaisa,a hankali yana kallon Daada yace "Daada i'm leaving now" Daada ta ɗago tana kallonsa tace "zuwa ina?" Yace "zan koma America" kallonsa ta dunga yi kamar bata gane me yake cewa ba kafin tace "toh ka yima Abbanku sallama?" Yace "a'a" tace "toh sai ka jira har ya dawo ai ba nisa yayi ba" girgiza kanshi yayi yace "zan kirashi in sha Allah,ai na ga baya nan kuma few minutes ya rage jirginmu ya ɗaga" Daada tana gyaɗa kanta tace "toh shi kenan.. Allah ya tsare ya saukeku lafiya" ya amsa kafin ya tashi yana sake kallon agogon dake ɗaure wrist ɗinsa,ya ƙarasa gabanta yace "na barku lafiya" ta amsa tana dafa kanshi tace "Allah yayi muku albarka" ya amsa tare da ajiye mata kuɗi masu ɗan dama sannan ya miƙe ya nufi ƙofa cikin ɗan sauri,Daada ta bishi da addu'ah tana cewa "idan ka sauka ka kiramu kaji kou?" Yace "in sha Allah" daga haka ya fice ya bar gidan. A ƙofar gida ya samu Isiyaku da Salisu tsaye suna hira,ganinsa yasa da sauri Isiyaku ya taho ya karɓi akwatin hannunsa ya koma ya buɗe booth ya saka sannan ya buɗe masa motar,dai² lokacin Hamood ya karɓi Abuu Turab daga hannun Salisu yana faɗin "thanks" sannan ya shiga mota,sai da ya sallami Salisu sannan Isiyaku ya rufe,ya koma ya shiga mazauninsa ya tada motar yana tambayar Hamood dake rungume da ɗansa yace "yallaɓai ina muka nufa?" Hamood dake ta kallon ɗansa yace "take us to airport" Isiyaku ya amsa ya tada mota suka ɗauki hanya.

WAZEER!Where stories live. Discover now