😢😭 2

42 2 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Khairi bata farka ba se bayan awa guda, ganin ta tayi a kwance a kan gadon asbiti ba kowa a dakin. A hankali ta tashi tana tunanin me ya kawo ta asbiti kuma? Nan da nan tashin hankalin da ya faru ya dawo mata, to amma ba kowa a dakin ko de mafarki take.
Jin hayaniyar da tayi a waje ne yasa ta tsige karin ruwan da ake mata ta nufi waje da gudu. Tana fita daga dakin taga yan uwanta ana ta koke koke a corridor, Habawa nan da nan ta tabbatar ba mafarki take ba.
Da gudu ta kwasa tayo dakin da umar ke kwance dan dama kawantar da ita akayi a dakin da ke kusa da na umar din.
Tana shiga ta tarar da mutane da yawa amma umma da abba ta iya ganewa a dakin.
Umma na zaune a a kusa da  gawar umar da aka lullube da zani tana kuka. Ganin umar a kwance a lulube ya kara wargaza mata lissafi Tayo kan sa da gudu, se a lokacin mutanen dakin suka lura da ita.

Ta rukunkume shi gaba daya tana wani irin kuka me gunji. Yau umar mijin ta ya rasu? An rufe babin shi a doron kasa ake nufu? Inalillahi wa inna ilahi rajiun .
Haka yan uwa aka rufe ta ana bata hakuri, babu wanda be zubda hawaye ba a dakin.

Wani irin kuka take me cin zuciya, ba'a taba yi mata mutuwa da ta taba ta ba haka da wayon ta. Iyayen ta da yan uwanta duk suna nan, kakansu ma da ya rasu batayi wayo ba lokacin. Bata taba sanin mutuwan na kusa da kai yana da azaba ba se yau.

Dakin ya rude da koke koke, yan waje ma suna ta yi. Kafin kace kwabo dangi an hadu an cika asbitin. Kana ganin Alh ibrahim kasan dauriya kawai yake,  idanun sa sun kumbura sunyi jawur, shi kadai yasan me yake ji a cikin zuciyar sa. Ya kasa tabuka komai ya samu wani lungu ya zauna Yana facing bango.

Duk wanda yaga Alhaji da kahiri se ya tausaya musu a wannan halin.  Shi kadai ne d'a a wajen Alh ibrahim ita kuma khairi amaryar sa da basu shekara da aure ba.

Abba ne yayi kokari ya shirya tafiya da gawar gida saboda Alh baya cikin hayyacin sa.
Ko da aka kawo gawa family house dare yayi se aka yanke shawarar washe gari da safe zaayi mishi sutura a kaishi makabarta.
Kwana akayi a gidan ana koke koke, khairi tare da gawar umar ta kwana a dakin iya falmata. Yadda taga rana haka taga dare ba abun da take ma umar se addua. Ta fita daga hayyacin ta gaba daya. Ita kanta abar ayi wa kuka ce.

Kafin gari ya waye zance ya isa  company A abuja, duk ma'ikatan company sun shiga wani irin shock da labarin MD ya rasu!! labari ne da ma'aikata da yawa sun kasa yarda da shi, number 1  a ciki shine Abdulkareem, se jidda sannan su intisar suka biyo baya.

Ak da umar were never on thesame page amma mutuwar umar ta girgiza Abdulkareem, be taba kawowa umar mutuwa ba, be taba sanin ma bashi da lafiya ba. ji yake kamar wani dan uwansa ne na jini ya rasu.
A Ranar hutu aka bayar a conpany na kwana uku aka tsayar da duk wani abu da akeyi. Babu wanda yasan umar bashi da lafiya, sun de san tun bayan auren shi be kara dawowa company ba bare su san bashi da lafiya. Kawai de Tun wata 2 zuwa 3 aka dena gane kan Alhaji ibrahim saboda kullum yan cikin tafiye tafiya sannan baya damuwa da aikin company, ya sakar ma directors dinsa ragamar komai.

Mutanen Alh ibrahim na Abuja suka dinga booking flight zuwa kano saboda su samu jana'iza.
A can gidan Alh ibrahim a Abuja suma sun shiga tashin hankali bare hajiya binta wadda ta shiga cikin rudani, ba abun da takeyi se kuka. Bayan dawowar su umar daga Us taje  ta gaishe shi amma tun daga nan bata kara ganin sa ba se labarin mutuwar sa suka ji kwatsam.
Matar Alhaji kuwa kukan munafurci tayi wanda be kai  har zuci ba, ita murna ma take saboda babu magaji. Abuda ya rage mata shine ta kwashi rabon ta tun kafin Alhaji shima ya mutu tunda tasan yan uwan sa ne zasu fi gadar sa. Se kace tasan gawar fari. Suma da safe suka shigo jirgi se kano.

Kafin lokacin jana'iza unguwar ta cika makil, mutum zeyi tunanin wani  babban dattijo sannanne a gari ne ya mutu. Baza kayi tunanin umar ne wanda be fi shekara daya a garin ba dan Ya tara jama'a sosai. Dangi na uwa da uba duk sun hallara, ga kuma tarin Abokan Arzuki da Abokan kasuwancin Alhaji, Ma'ikata da directors na company duk sun hallara. Abdulkareem ma baa barshi a baya ba da sassafe ya bogo mota se kano

Anyi janaizar umar karfe 11 na safe, mutane da dama sun sallace shi. Sheda daya da umar ya samu shine na kyauta da sadaka boyayya. Ya wakilta wani kanin umma yana masa duk charity work a sirri ba tare da sanin kowa ba. Yayi amfani da dukiyar sa wajen temakawa marayu da gajiyyayu. An gina masallatai da makarantu, boreholes kala kala a unguwanni da dama duk a boye ba tare da mutanen da yayi wa aikin sun san sunan sa ba, sai dai ace wani bawan Allah ne ya gina kuma baya so a bayyana sunan sa Addua kawai yake bukata.
A unguwar su kakanin shi kuwa haka yasa  sa a bi layi cikin dare ana ajyewa mutane kayan abinci se dai a tashi da asuba kowa ya gani a kofar gidan sa

Se bayan mutuwar sa sannan abubuwan Alkhairan nan suka fito. Mutanen da basu taba ganin shi bama sun zubar masa da kwalla da suka samu labarin  shine bawan Allah da yayi musu abubuwan Alkhairi

A cikin family house kuma Abun baa cewa komai. Gida ya hadu babu masaka tsinke, masu kuka nayi masu jinami nayi, Abun de abun tausayi.
Haka yan gaisuwa sukai ta shiga suna fitowa suna adduan Allah ya jikan mamaci yasa ya huta.

Kowa ya tausaya wa khairi matuka saboda rayuwar auren su batayi tsawo ba.
Magana ma khairi bata iyawa se kallo kawai, a zuciyar ta tana tuno wulakancin da tayi masa a baya, Ashe ba me nisan kwana bane. Ta shiga kogin nadama wanda bashi da amfani a lokacin. A iya zaman da sukayi na watanni umar miji ne na gari wanda ya nuna mata tsantsar soyayya sannan ya kula da ita iya karshen karfin sa, mutum ne wanda baya son bacin ranta kwata kwata. Umar yana da strong personality with a soft heart

Har cikin gida tawagar su Abdulkareem suka shiga yin ta'aziya. Babu wanda ya iya gane shi ma daga umma har khairi saboda tashin hankali, ansa gaisuwa kawai umma take ba tare da ta san wa ke yi ba, khairi kuwa se ido, zakayi tunanin kallon ka take amma a zahiri ba lallai ta san da mutum a gurin ba ma don hankalin ta yana wani wajen.

A zaune ya ganta mutane zagaye da ita, kallo daya yayi mata ya kau da kai saboda zuciyar sa baza ta iya jurar ganin ta a wannan yanayin ba, ta kode tayi jaa fuska da idanu duk a kumbure. Ta tsurawa wani guri ido alamun she is lost. Tun ana i gobe aurenta da ya ganta be kara sata a ido ba se yau

Tawagar su Abdulkareem suka tsugunna sukayi gaisuwa. Matan gurin suka answer adduoin da sukayi sannan suka tashi. Jikin Abdulkareem yayi sanyi matuka ganin ummulkhair a cikin yanayin tashin hankali haka. Ji yake ina ma ze iya dauke mata damuwa da bakin da radadin da take ji. Ina ma ze iya sharing burden dinnan tare da ita.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now