Monday

57 6 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Monday ranar aiki ko bature na tsoron ki, yau ce monday da ko wani ma'aikacin silver constructions yake jira don jin yadda zata kaya tsakanin bako da jidda
Jidda da aka kora tafi kowa son zuwa aiki ranar

Shige da fice ake tayi da kayan furniture zuwa sama bene na uku, kowa yayi ta mamakin me akeyi a saman. Office ne da ke kusa da office din executive director ake gyarawa, a bakin kofar office din an rubuta MANAGING DIRECTOR.
Office ne aka kawata shi kamar na executive director har ma ya so ya fi nashi kyau, haka maaikatan suka dinga sintirin hawa sama domin ganewa idon su.

Umar ne ya shigo ya ci shirt dinsa da wondo har da tie, receptionists  batayi gigin kara tsayar da shi ba. Gaishe shi tayi a takaice. Yace mata ta kira secretary company din.

Sakatarorin kamfanin guda 5 ne, biyu mata uku maza. Akwai secretary building department namiji ne, se secretary engineering department shima namiji ne, se secretary Human Resources mace ce , Se chief secretary wanda namiji ne, sannan secretary executive director jidda kenan.

Ko wani secretary yana da office a jikin office din uban gidan sa, wanda akwai kofa da take linking dinsu ta cikin office din. Sannan bango daya a office din secretary glass ne duk wanda yake waje ze iya ganin na cikin office din amma akwai labule wanda na cikin office din ze iya zugewa idan baya so a ganshi.

Receptionist din ta dauko waya ta kira chief secretary Mr ruben.
Mr. ruben ya sauko jiki na rawa ya samu umar a tsaye ya gaishe shi cikin girmamawa. Daman Alh ibrahim yayi masa magana akan umar din

Umar yace ya tattaro masa wasu takardun kamfanin da ze duba don ya san kan aikin company da ma'aikatan su. Sannan yace a shirya masa meeting da heads din departments tare da sakatarorin su. Jikin mr ruben na rawa ya tafi aiwatar da aikin da aka sa shi.

ALH ibrahim da ke tsaye a sama yana ganin duk abunda ke faruwa a kasa. Ya hango shigowar umar da tsayuwar su da mr ruben. Murmushi yayi yayin da ya tuno abun da ya faru ranar juma'a.

Takardar da umar ya ajye masa a table takarda ce da take nuna tuhuma da court din America takeyi masa game da dukuyar sarah da ya hau kai ya zauna, dayar takardar tana nuna shaidar mallakar komai da maman sa sarah ta bari wanda ya hada harda Kamfanin silver construction.
Sannan takardar karshe takardar yarjejeniya ce da take nuna zasu juya kamfanin silver construction tare matsayin patners shi da babansa. Kowa yana da kashi hamsin hamsin.
idan be yarda da hakan ba sede su hadu a kotu.

Murmushi ya cigaba da yi yana kallon sa, yaronsa ya girma har yana kokarin challenging dinsa. Shi abun alfaharin sa ne yaron sa ya gaje shi, da umar yasan abunda yake ransa baze bata lokacin yi masa barazana da kotu ba.

Abinda baya so shine umar ya gudu ya koma america inda babu uwa babu uba ya kara haduwa da abokan banza rayuwar sa ta kara tabarbare wa. Shiyasa ma ya kwace passport da wayoyinsa
Shi kanshi ya fi son ya dinga zuwa aiki ko ya warke daga sauran depression dake damunsa

Lokacin meeting yayi, kowa ya hallata har da Alh ibrahim. ALH ibrahim ya bude taro da bayanin ci gaba da company ta samu sannan yayi musu bayanin company ta samu sabon managing director UMAR IBRAHIM MIJINYAWA.

Se da ya fadi sunan tukunna kowa ya gane dan ALH ibrahim ne tabbas ga kamar nan ta fito da ya fada, sai dai shi umar yana da hasken fata shi kuma baban nasa baki ne

Ya ci gaba da bayani sannan ya bawa umar dama yayi magana shima. Umar magana kadan yayi a takaice akan mahimmacin aiki da hada kai.

Bayan ya gama nashi bayanin Alh ibrahim ya tambaya ko akwai wanda zeyi magana. Abdulkareem  ya daga hannu sannan ya kalli jidda da ke gefen alhaji a takure duk a tsure take.

"Maganar secretary jidda da MD (managing director) umar ya sallama a aiki ranar juma'a, muna son jin ba'asin da dalilin sallamar ta da akayi."

Umar ya fara juye juye sannan yace
"Wacece jidda a nan"

Jidda ta tashi tsaye jiki a mace kamar wanda kwai ya fashe mata a ciki, umar ya ce mata

"Kece kikayi kokarin hanani shiga office din ED (executive director)

"Yes sir"

"Then you're fired" ya fada furkarsa a murtuke babu alamar rahma

Jidda Kallon Alh ibrahim tayi domin neman ceto amma be ce komai ba.

AK ne yace
"Kafin a kori mutum a kamfanin nan se an bi protocol, se maaikaci ya karya dokokin kamfani tukunna.
Za'ayi forwarding case dinta zuwa human resource department idan an same ta da lefi se a hukunta ta daidai da lefin ta."
( duk wannan surutun da turanci akeyi)

Yana magana idon sa kar kar a kan umar, yayi amfani da lafazin jaddadawa domin nuna masa ba tsoron sa ake ji ba. Daga zuwan sa zeyi kokarin nuna isa.

Umar da shima kallon sa yake ido cikin ido . A zuciyar sa tunani yake yi lallai wannan be san da wa yake ja ba, idan yayi tunanin shiga hurumin sa ne to tabbas zai taka masa birki dan baze sarara masa ba, idan kuma yana so su sa kafar wando daya da shi ne su zuba.

🍒🍒🍒🍒🍒

Bayan an tashi daga  aiki Ak ya dawo gidansa da ke gwarimpa, Apartment ne me kyau ya kama haya yake zama. Akwai wani yaro TASI'U da ke masa yan gyare gyare da yi masa abinci.

Ya fada kan gadonsa ya rufe idonsa, fuskar khairi ce yake ainayo wa, Allah ya san yana tsananin sonta, burinsa shine ya aure ta. mahaifiyar sa zatayi tsananin farin ciki idan taji yayi maganar aure dan burin kowa a gidansu kenan

Wayarsa ya janyo daga aljihu ya kira ILU me gadi don jin ko ya samo numbar Ummulkhairi. Me gadin ya bashi hakuri sannan ya bashi dalilin saboda anyi hutu ne kuma malaman ba zuwa sukeyi ba. Amma ze yi kokari  ya samo masa numbar.

Be ji dadin rashin samun numbar ba amma ya zeyi.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒

SarkakiyaWhere stories live. Discover now