Rashin lafiya

47 3 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Tun tana kuka kullum har ya kai ga hawayen ya dauke se kukan zuci. Babban bakin cikinta shine yadda bata samu damar sallama ko bankwana da Abdulkareem ba, a kullum tashin hankalin ta shine me Ak yake tunani game da ta? a wani yanayi yake ciki? Dole ze kullace ta a ranshi saboda wannan yaudarar da aka masa. se de tayi fatan Allah ya sa wata rana ya iya yafe mata.

Tunda aka kawo ta gidan umar bata taba shaawar fita ba ko taji tayi missing gidan su saboda har a lokacin ta kasa yafe musu.

Haka suka ci gaba da rayuwa a gidan nasu babu me kwanciyar hankali. Har bashariyya me aiki Allah Allah take ta gama aikin ta ta bar musu gidan saboda gaba daya atmosphere din gidan babu walwala ko jin dadi

A kwana a tashi khairi tayi kwana 10 a gidan ko kafar gida bata taka ba, Tana nan a cikin gidan kamar prisoner. Har lokacin bata bari sun hadu da umar ba, shima kuma baya son takura mata yafi so se ta huce sannan ya same ta suyi magana.

Yau wajen karfe 11 na safe ya fito ze fita gurin me gadi suyi hira yadda ya saba ya tarar da bashariyya a farfajiyar gidan tana tsinkar na'a na'a a. Tana ganin umar ta rusuna ta gaishe shi

"Ina kwana yallabai"

"Lafiya kalau bashariya, ummulkhair ta tashi lafiya?
Ya tambayi bashariyya dayake kusan kullum se ya tambaye ta ya khairi ta tashi.
Bashariya ta danyi shiru sannan tace

"Wlh anty ba lafiya tana kwance a daki. Yanzu ma shayi zan dafa mata na na'a na'a. Ta kasa cin komai shine tace in dafa mata shayin ko zata iya sha"

Hankalin umar ya tashi, be tsaya kara yin magana ba yayi cikin gidan da sauri.

Khairi tana kwance taji kamar an wullo mutum cikin dakin, a tunanin ta bashariyya ce tun da tasan tun ranar farko da aka kawo ta umar be kara zuwa kofar dakin ta ba. a kwance take ta rufa da bargo har kai dan haka bata ga wanda ya shigo ba.

A hankali ya tako ya zo har gabon gadon ta ya dan rusuno. Kanshin turaren sa ne ya buge ta duk da tana cikin bargo, Kashin turaren sa baya buya

Cikin hanzari ta yaye bargon saboda razanar da tayi.
Tana budewa sukayi ido hudu,
Kallon ta ya saki baki yana yi saboda yadda yayi missing dinta, sanye take da kayan bacci riga me buttons da wando duk na silk. Ta rame tayi wani fari se idanuwa, ka kashin wuya ya kara fitowa yayi rankwal ba kyan gani. Kallonta ya shagaltu da yi na seconds dan ya manta ma me ya kawo shi dakin.

Yadda taga yana kallon ta ne yasa ta tsargu. Da ta tuno a yadda ta ke ba shiri ta janyo bargon ta rufe jikin ta, ko nace ta rufe kirjin ta. Kirjin da ba wani abun arziki bane a jiki

Ta so ta fara masifa amma ta kasa, Ko dan ciwon da takeyi ne oho. ta kula shima ya dan rame amma wannan ba matsalar ta bace. Kallon banza ta bishi da shi, Shi kuwa be san kallon banza ma take masa ba.

ya zauna a gefen ta a kan gadon tare da kai hannu ze taba jikin ta, khairi na ganin haka tayi saurin jan baya
"Lafiya mallam? Me ya kawo ka daki na?

" bashariyya ce tace baki da lafiya shine nazo na duba ki"
Ya fada yana dar dar

"Lafiya ta kalau zaka iya tafiya"
Ta fada tare da kara hade rai.

Ya kara kai hannu ze taba goshin ta ta kai masa duka da yunkurin make hannun sa daga taba ta da zeyi.

Tana dukan shi ya rike hannun nata kuwa. Ji yayi hannun ta zafi radau alamar zazzabi ne a jikin ta. Nan da nan hankalin shi ya kara tashi.

Dai dai lokacin bashariyya ta shigo dakin kanta tsaye saboda bata taba tunanin ganin umar a dakin ba.
Ganin umar tayi a zaune kusa da khairi gashi rike da hannun ta

Ba shiri ta fara i'ina
"Daman....... Ummmm .... Shayin .... Na kawo"

Kunya ya kama khairi ta kasa magana
Hankalin umar a kwance yace mata
"Ajye a kan table din"

Da sauri bashariyya ta ajye ta fara neman hanyar waje
Umar ya kira sunan bashariya wanda yasa Ta tsaya chak ba tare da ta juyo ba

"Samo min towel da ruwa a bowl"

Bashariyya ta fita da sauri ta basu guri, a ranta tana ta mamakin iyayen gidan nata. Mutanen da saboda kiyayya basa zama guri daya hasali ma wasan buya buya suke a gidan.

Bashariyya na fita khairi taji kamar an kara mata wani karfi, cikin karfin hali da dagiya ta fizge hannun ta tare da tura shi da karfi don ya matsa daga kusa da ita.

"Dan Allah ka fita daga dakin nan"
Ta fada jiki ba kwari, da kyar ma take magana saboda ciwon da take ji. Stress din kwana biyu da ta shiga da kuma malaria da ke jikin ta ne ya tasar mata.

Shiru yayi ya ci gaba da kallon ta har bashariya ta shigo da katon bowl da towel me kyau a dayan hannun.

Umar ya karba ya ajye a kan gadon, ya saka towel din a cikin ruwa ya matse sannan ya kara matsowa daf da ita ze daura mata a goshi
Khairi ta ci gaba da harara sa amma ko a jikin sa. Burin shi a lokacin shine yaga ta samu lafiya. Ya diga shafa mata towel din a fuska zuwa wuyan ta, hannayen ta da kafafun ta
Tana ji tana gani amma ta kasa hana shi saboda ciwo.
Ya ci gaba da yi mata towel bath hade da massage, nan da nan zazzabin ya fara sauka, bayan lokaci kadan bacci ya kwashe ta.

A hankali ya zame ya kwantar da ita sannan ya fito ya tafi pharmacy ya siyo mata magunguna.
Ya biya ta dominos ya siyo mata kayan ciye ciye sannan ya dawo gida.

Da ya dawo ma baccin take. Ya zauna a kujera 1 seater da ke dakin yana kallon His little fragile wife a kwance, a ko wani yanayi kyau take masa. hatta baccin ta abun kallo ne, saboda bacci ne take yin sa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali
Se bayan awa 1 ta tashi daga baccin, tana tashi ta ganshi a zaune yana facing dinta.

Ya tashi ya kawo mata maganin da ya siyo, ya ballar mata maganin ya mika mata tare da ruwa, ba musu ta karbin maganin ta sha. Ya fito da kayan ciye ciyen ya bata tace baza ta ci ba, sai dai ta sha tea.

Tea din da bashariya ta kawo mata ma bata sha ba. Ya kira bashariya yace ta kara hada mata shayin.
Bayan ta sha shayin ta kara komawa bacci

Haka umar yayi ta kula da ita har dare. Lokacin da bashariya ta tafi gida ma haka Ya shiga kitchen ya soya mata egg da tea me kauri ganin bata ci komai ba through out
Yana dawowa ya tarar bata gadon se karar famfo da yaji a toilet wanda ya tabbatar masa tana ciki. Ya ajye mata karamin tray din abincin sanna ya fita daga dakin

.se Bayan minti 30 ya koma dakin.
A zaune ya ganta a jikin mirror daure da towel tana shafa cream Daga gani wanka tayi.
Gashin ta bakin kirin ya sauka har wuya. Shekin fatar ta ta dauki hankalin sa. Jin shi yayi wani yammm ganin zara zaran kafafuwan ta, tunda towel din a cinya ya tsaya.

Tana ganin shi ta hade rai ko batayi magana ba ya gane me take nufi. Sum sum ya juya ya bar dakin ko shima ya samu saukin yanayin da yake ji yana tsarga masa

Khairi ta gama shiryawa a cikin light bubu irin na zaman gida sanna tayi sallolin da ake binta, bayan ta idar Ta janyo soyayyaen kwai da tea da umar ya ajye mata ta ci.
Ta ji karfin jikin ta sosai zazzabin ma ya sauka.
Tana gama ci ta kashe light din dakin ta haye gado ta kwanta.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now