*HAMOOD*

           Su Yaa Abuye suna fita ya ɗago kanshi ranshi a matuƙar ɓace yana kallon Daada yace "wallahi Daada idan ta dawo ba da yahuna ba,ni i don't want her anymore.. Bazan iya sake zama da matar da tai silar mutuwar ƴata ba.. Haba dan Allah! Wane irin sakaci ne wannan ace kina matsayin uwa amma just 2 kids su gagareki ki iya kula da su,yarinya ƙarama 3 yrs ta rasa ranta saboda sakacinki,wace irin uwace ita?" Daada dai kallonshi kawai take ta ƙi cewa komai,yanda tayi kamar wanda ta daina magana kwata²,can ya kalleta yana tashi zai fita yace "na fita Daada" Daada ta sauke wani nauyayyar ajiyar zuciya kafin ta buɗe baki tace "toh! Idan ka fita sai ka tsaya gurin Abban naku ka sanar masa bai isa ba,hukuncin da ya yanke bai yi maka ba,ka gaya masa duk abunda ka faɗa min ka ji kou?" Juyowa yayi yana kallonta,Daada ta haɗe girarenta tace "ka tsaya kana kallona haka,na faɗi wani abu ne kuma? Kaje ka sameshi ka sanar masa kada ka mance" yace "Daada amma" da sauri cikin faɗa tace "ka ji na ce wani abu a cikin maganarku?" Ya girgiza kanshi yace "a'a!" Tace "toh fitar min a nan kafin na saɓar maka,mara hankalin yaro kawai,kai tunda kake a gidan nan ka taɓa jin kou yaji wata ta yi bama ni ba? Bare kuma har akai ga maganar saki?" Yai shiru yana ta kallonta,tace "kou ka dawo da matarka kou kuma ka san nayi,ni bazan iya wannan fitinar ba,idan kuma ka bijirema maganar mahaifinka wallahi ba da yahuna ba.. Sakaran yaro kawai mara hankali,kana da mace kamar wannan Allah na tuba me zai kaika rabuwa da ita? Yarinyar dake son iyayenka take girmamasu kamar nata,kana ganin dai matar Yayanka Isma'il,ina ce sai mu kwana nawa bata leƙo nan ta gaisheni ba,amma Hooriyah fa? Kullum sai ta shigo min,ƴaƴan nan nata duk da ƴan fici² ne amma sai ta turosu suzo su gaiahemu duk safiya,wannan bai isa gwada maka macen ƙwarai bace? Kawai daga faruwar abu wanda ita kanta bata sani ba sai kace ka saketa,tou kaji da wai idan har kaƙi dawo da ita,wallahi ba baki nai maka ba amma da wuya ka samu mace kamarta" kallon Daada ya dunga yi daga inda yake zuciyarsa na zafi,lokaci ɗaya yace "Daada ina Wazeer?" Daada tace "yo jariri ne shi kou kuwa zan mayar da shi ciki na ɓoyeshi?" Ya dunga kallonta yana juya batun a ransa,lokaci ɗaya ya fice ya nufi gidansa,knocking door ɗin ya dunga yi,ya kai kusan 3 minutes a gurin yaka kallon ƙofar kafin ya ciro key ɗinsa yasa,yanda yaji mukullin ya shige yana murɗawa ya buɗe ya shiga ya dunga kallon parlon da yai shiru babu kowa,zaunawa ya ƙarasa yayi saman kujera ya ciro wayarshi ya shiga kiran layinta,lokaci ɗaya ta ɗauka da sallama jikinta a sanyaye,da huskey voice ɗinsa yace "ina kika kai min yaro?" Yai shiru yana saurarenta,lokaci ɗaya ya tashi yana kallon agogon dake ɗaure wrist ɗinsa yace "ok! I'm coming to ur house.." Daga haka bai jira jin abunda za tace ba ya katse wayar tare da turawa cikin aljihunsa ya fita.

*HOORIYAH*

        Da safe tana tashi ta cire kayan jikinta ta shiga toilet,sai da tai wanka ta dawo ta zauna sannan ta fara tunanin kayan da za tasa,sai yanzu tunanin tahowarta haka ya tsaya mata a rai,ta shiga tuhumar kanta me yasa tai gaggawa bata tsaya kou kaya ta ɗauko musu ba ita da Abuu Turab? Tou kou dai Suwaiba za ta kira ta aika taje ta ɗan haɗo musu kayansu da za su buƙata nan kusa? Amma kuma su Yaa Abuye ai sun ce za su je gidan,kou dai tayi haƙuri har zuwa sanda za su dawo ne? Gyaɗa kanta tayi kafin ta tashi ta ɗauki rigarta ta mayar,duk sai kallon kanta take tana jin wani iri saboda bata saba maimaicin kaya ba,a haka ta fita parlour yin breakfast,Abuu Turab dake zaune ya ɗago yana kallonta,kamar bazai mata magana ba yace "Mimi ki canja min wasu kayan wannan na jiya ne Mama tasa min" kallonshi tayi lokaci ɗaya ta zauna kusa da shi tace "be patient my dear,za'a kawo maka wasu kayan,bari su Uncle Abuye su dawo" a hankali ya gyaɗa kanshi yace "ok!" Daga haka ya mayar da hankalinsa kan abincinsa,nan itama ta samu ta ɗan ci kaɗan shima gudun faɗan Mama ne yasa taci,lokaci² take ɗaga kanta ta kalli agogo. Around 1pm tana zaune zuciyarta na ɗan bugawa Yaa Abuye ya kira Mama suna hanyar dawowa idan sunyi sallar zhuhur za su shigo,daga yanayin muryarshi ta fahimci wani abu yana faruwa me daɗi,nan suka zauna jiran isowarsu,sai kuma ga kiran Hamood ya shigo wayarta,sanda gabanta ya faɗi ta daure wayar na daf da katsewa ta amsa da sallama,maganar da yai mata ya jefa zuciyarta cikin waswasi,bai kuma jira tace komai ba kawai ya katse kiran,shiru tayi tana kallon Abuu Turab dake kwance jikinta yai shiru yana kallon TV dake kunne. Kamar wanda ya taho a iska,cikin few minutes ya sake kiranta,tana ɗauka yace "i'm outside.." Daga haka bai jira tai magana ba ya katse kiran,da farko shiru tayi ta rasa abun cewa,lokaci ɗaya tayi ƙarfin halin kallon Mama tace "Mama zanje yana kirana wai yana waje" Mama dake amsa sallamar su Yaa Abuye tace "toh! Sai kin dawo" daga haka ta ɗan kalli Abuu Turab tace "Babana kwanta bari naje gurin Dad na dawo" gyaɗa mata kai yayi ya sauke kanshi ya kwanta saman kujerar yai shiru,da ɗan sauri Hoor ta tashi ta shiga ciki ta ɗauko hijab ɗinta ta fita. Tana buɗe get ta ɗan leƙo kaɗan,tsaye ta hangoshi jikin wani sabuwar mota yayi folding hannayensa a saman ƙirjinsa fuskarsa ɗaure yana kallon cikin line,da ƙyar ta daure ta fita ta dunga ɗaga ƙafafuwanta tana nufar inda yake,tana isa ta tsaya ɗan nesa da shi kaɗan tare da yin sallama "assalamu alaikum.." Juyowa yayi ya kalleta ya amsa,suna haɗa ido tai saurin ɗauke kanta tana kallon wani wajen,a dake yana ƙare mata kallo yace "where's my son?" A hankali jikinta a sanyaye tace "yana cikin gida" lokaci ɗaya ya gyara tsaiwarshi yace "ok! Gurinsa nazo,ina son ganinsa" gyaɗa masa kai tayi tace "ok!" Sannan ta wuce gidan,tana shiga ta samu Mama na faɗin "alhmdllh! Amma na ji daɗin wannan lamari,Allah ya tsare ya kaɗe fitina.." Su Yaa Mansoor suna ta murmushin da ya ɗaure mata kai,a hankali ta furta "Abuu Turab!" Tasowa yayi da sauri yace "yes Mimi" da hannu ta yafitoshi tace "zo Dad na kiranka" a hankali ya gyaɗa kanshi yace "tou Mimi" tana tsaye yasa takalminsa ya taho,ta kama hannunsa suka fita gidan,tun daga nesa Hamood ke kallon ɗansa,suna isa kusa da shi ya miƙa masa hannu yana faɗin "come here My boy" tafiya yayi babu musu,Hamood na kama hannunsa kawai ya juya tare da buɗe mota ya ɗagashi yasa ciki yasa masa seat belt ya rufe then ya zagaya driver side zai shiga,da wani irin shock Hoor dake tsaye kamar statue tana kallonshi lokaci ɗaya tace "Hamood! What are u doing? Ina za kaje da shi baka sanar min ba?" Juyowa yayi yana sakar mata wani kallo yace "i'm leaving with him.. Kina zaton na dawo miki ne? Na zo nan ne for his sake,saboda na karɓeshi daga hannunki,na nisantashi daga gareki kada shima ki kashe min shi,not for u" daga haka ya buɗe motar ya shiga...


         #Wai me Hamood yake nufi ne jama'a? To bari dai muga zuwan da dawowar,amma dai ya fara wuce makaɗi da rawa..

*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*

   _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
   _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176  domin karin bayani,  maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa,  yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka   fara amfani da   maganin zaki ga sauyi,  domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari  2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

*Infection*
    _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye!  infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_

    _Muna sayar da supplement gangariya  irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*



#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.

WAZEER!Où les histoires vivent. Découvrez maintenant