Na ce,"Ina kuma? na faɗa fuska ta cike da damuwa kuka ne kaɗai ya rage nayi saboda idanuwa na sun riga da sun yi ja tsabar na kagu na koma wajan su Anna.

Na wai ga na ce,"Ba su Anna suna ciki ba, ina zan raka ka dare fa yayi"

Na ɗaga hankali ne kasancewar nasani tabbas na sake da shi duk da bamu wani jima ba, amma na rasa ya a kayi na saba da shi a cikin kwanaki kalilan, ban fa san ko shi waye ba, amma dai zan iya bada shedar mutumin kirki ne tun da ban taɓa ganin sa yana chutar da wani ba.....ina tsaka da wannan tunanin naji Ya ce

"Idan kin gama tunanin ki zo muje dai" ya faɗa yayi gaba abin sa, sai na tsinci kai na da bin bayan sa har muka isa in da motar sa take, ya buɗe min na shiga ya zagaya shima ya shiga.....Zuciya ta na ta min kashedi idan ya min wani abu fa, zuciyar tawa fal da tsoro hakan ya sa nayi shiru ko kyakkyawan zama ban yi ba a kujerar.

Muna ta tafiya babu mai yiwa kowa magana, a daidai wajan masu sai da fruit a bakin hanya irin fresh ɗin nan, ma su kyau, muka tsaya ya fita ya siyo Tuffah, Abarba, Ayaba, Lemo da sauran kayan marmari, ya jido su da yawa kamar hauka, nayi niyan zuwa na taimaka masa sai naji yace min,"No need ke sarauniya ce ƴar buzuwa na" ya faɗa da zolaya ya cigaba da kwaso kayan har suka gama ya tuka motar....Ni dai ban kula sa ba ina zaune kamar gun ki.

Muka sake zuwa wani Super market nan ma yace min na zauna kawai ya kunna min karatun alkur'ani, ina ta saurara har na fara gyangyaɗi ma cen naji ana ta loda kaya a motar na buɗe ido sai naga yana shigowa yana ce musu sai da safe, ban ce mishi kala ba, Amma na lura da yanda ake ta faman kiran wayan sa an masa miss call ya kai sau goma ko ma fiye da haka kuma bai ɗaga kiran ba...

Muka koma asibiti na fito ma ban tsaya taya sa kwashe kayan ba saboda ban san ko na su waye bane.

Ahmad ya gane Khadija na tsoron sa yanzu tun da har taki yi masa magana yana kallon ta ta wuce ta shiga ɗakin da aka kwantar da Anna, rabuwa yayi da ita kuma dama bai isa ya sanya ta kwashe kayan nan ba saboda suna da nauyi...dole ta sa ya nemo wasu sojoji ya nuna musu ɗakin sukai ta shigar da kayan.

Shi kuma yana tsaye jikin motar sa, yana kokarin ɗaga kira an sake kira kenan a karo sau ba a dadi.

*************
Ina shiga na iske Anna zaune tana hira da Baffah, Sofia kuma na zaune daram a cinyar Anna tayi bacci.

Murmushi nayi na faɗa jikin Anna da sauri na rungume ta ina cewa "Lahhh Alhamdulillahiii Anna na ta samu lafiya"

Baffah ya ce,"Ina kika shiga ne tun ɗazu Hadiza? abin ka da mahaifi kenan dole ya tambaya ina ta shiga

Na ce,"Baffah ina waje ni da Yaya Ahmad, na jira shi yaje masallaci ya dawo shi ne na shigo yanzu"

"Ohhhooo, ina yake?

Baffah ya tambaya a daidai lokacin da naga sojoji suna ta shigowa da kaya niki niki a hannun su, manya manyan ledoji bakake, zasu kai goma ko ma fiye da haka, na yamutsa baki cikin rai na ina cewa ko miye waɗannan kuma ohoooo

Na ce wa Baffah ,"Yana waje na bar sa" na faɗa ina wai gawa kofar shigowa in ga ko ya shigo, ai kuwa ya shigo yana tsaye yana kare min kallo hannyen sa na saman kirjin sa ya nannaɗe su.

Da kyar ya iya karasowa in da muke, babu kuzari a tattare da shi, fuskar sa babu annuri ya karaso yana cewa ,"Baffah ga komai da komai da zaku bukata, ga kuma kuɗi" ya mika wa Baffah bandir ɗin ƴan dubu ɗaya, yana cewa "Dubu ɗari uku ne Baffah duk abin da kuke bukata ku cire a ciki kuyi anfani da shi, don Allah bana son baran nan"

Baffah kamar yana kallon Ahmad abin ya ba shi mamaki, Ya ce ,"Ɗan nan mun gode da ɗawainiya sosai Allah yayi ma rayuwar ka Albarka, amma kuɗin nan sun yi yawa ka rage su dan Allah"

Anna ta ce,"Yaro mun gode sosai wannan ma da kai mana ya isa wallahi muna godiya, ka bar kuɗin ka kaji, kar ɗawainiyar yayi yawa"

Ya sunkuya har kasa, muryar sa kasa kasa, fuskar sa dai babu wani fara'a Ya ce," Baffah kuna mai da hannun kyau ta baya, Don Allah kuyi hakuri , kuma kun sani babu kyau, kuɗin nan fa zasu muku anfani, ba wai na rai na sana'ar baran dankuke zuwa bane, Anna kawai ina son ku dena zuwa ne kuma ga shi baki da lafiya" ya faɗa yana kara sassauta murya

Da kyar Baffah ya kar ɓa, yana shi mishi albarka yana cewa ,"Yaro kai ɗan wani gari ne tun da kazo bamu samu mun tattauna ba"

"Baffah ni da Iyaye na ma zauna garin abuja ne, kuma a cen nake aiki, sana'a ta zane wato Arc............

Bai karasa ba sai naji Baffah yayi saurin cewa Arctecture?

Ahmad yayi saurin amsa masa da ,"Eh Arctect ne ni da Mahaifi na, Wanda ma muna da campanin zana abubuwa da dama"

Baffah yayi saurin cewa ,"Allah ya taimaka Ahmad, amma kwakwalwata tana son tunano min da wasu abubuwa da nayi a rayuwa ta da jimawa nima ina ji a jikina kamar nayi zane,.........Baffah ya tsagai ta.

Ahmad ya na tsugunne sai da ya ɗago kai da sauri ya kalli Baffah Ya ce,"Da gaske Baffah shin miye sunan ka na asali wai?

"Anna ganin abin na su na yin zurfi sai ta kaste su da cewa "*Baffah*" Baffah shine asalin sunan sa".

Ahmad karar wayar sa ya sashi yin shiru ran shi na daɗa dagule wa, ya duba wayar yaga still Mummy ce, ita in ta fara kiran waya shikenan ta dunga kenan, ita ce dama take ta kiran sa akan lafiya taga yayi kwana biyi bai dawo ba, sannan ta faɗa masa cewa idan har bai dawo yau ba to zai gansu a kaduna gobe, ko a ina suke zasu nemo sa, Dole ta sa yau zai kama hanyar Abuja da daddaren nan.

Ya ce,"Baffah Iyaye na suna son gani na, yan zun nan zan kama hanya, amma bayan kwana biyu zan dawo ko dankuwa an sallame ku zan same ku a gida...ya tsagaita.

______________________________________

ALMAJIRA SABON SALO littafine da ni ke da yakinin duk wani masoyi na idan ya karanta shi ba zai yi dana sanin karantawa ba.

Na san you guys will always patronize me and stand by me saboda duk mai son ka yake kaunar ka kuma yake amfana da kai, Na san ba zai ji kyashin kai ma ka karu da shi ba.

200 naira kacal zaku biya dan samun shiga whatsapp group din da zan rinka posting in Allah ya yarda.

3119736620
Fadila Ibrahim
First bank
Sannan ku turo da shedar biya ta wannan layin

07031086858

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now