09

42 2 1
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


FREE PAGES
09

______________________________________

Mummy hankali tashe ta fara sanar da Daddy a waya, sannan ya umarce ta da ta kira Doctor kafin ya dawo.

Ta lalibo number Doctor Rasheed, ta kira shi.

Daga bisani kuma ta shiga toilet ta jika towel da ruwa a cikin roba ta zo ta zauna bayan ta kunna AC ta rage gudun iskan kaɗan, a hankali take matse towel ɗin tana ɗaurawa a goshin sa tana mishi sannu.

A hankali ya buɗe kyawawan idanuwan sa masu kama da lazy eyes ya ɗaura su akan Mummy ya lumshe su kaɗan yana cewa,"Kun dawo ne Mummy?

"Yes we are back son, and what's all this? You are having a high fever what cause it dear? Ta faɗa cike da damuwa karara a fuskar ta.

"Common Mummy, it's just a small fever and i'll be fine In Sha Allah" Ahmad ya mayar mata da amsa.

"No no no noooooo, Doctor is on his way, zai duba ka"

"Doc what, please don't start it again, i hope it's not Rasheed bacause he don't know any other thing apart from injecting people" Ahmad ya faɗa yana tura baki kamar dai wani karamin yaro.

"Hehhh Ahmaddddd, don't tell me that uptil now you still scared of Injection" Mummy ta mayar masa fuskar ta alamar mamaki tana dariya kuma.

"Ohhh noo Mummy am a big boy, yaron ki ya girma kawai daiii"... Ya wani make kafaɗa sai kuma yayi shiru yana sosa keya, Mummy kin san doctor rasheed mayen injection ne"

"Ahmad don't start it again, be quite " ta kwaɓe shi tana kara ɗanna masa towel a forehead ɗin sa, sallamar doctor rasheed ita ta sanya su yin shiru.

Ya shigo suka gai sa da Mummy sannan ya ɗan kalli Ahmad wanda yake ta hararan sa tun shigowar sa, Doctor rasheed yace,"Mummy baby boy ne bai da lafiya, ashe yana bukatar injection kuwa" Ya faɗa teasingly

Ahmad ya ɗauko wani pillow a gefen sa ya wurga masa yana cewa,"Leave I don't need you here"

Doctor yayi dariya yana cewa,"That's why you keep ignoring my calls Ahmad saboda ka tsani Injection, to injection ɗin kullin ne a keyi ai sai mutum bai da lafiya kamar dai yanzu" ya sake faɗa yana ɗan dariya

"Mummy kinga baaa, You just call him doctor mainwhile and kina jin abin da yake faɗa yanzu,Doctor basa dariya wa patirnt, and ba haka ake attending patient ba, at least you should pamper me"

Doctor rasheed ya fashe da dariya, yana daɗa buɗe firstaid box ɗin sa, yana ɗauko karamin abin test, yana cewa,"Baby boy stay calm zamu fara da test"

Duk da zazzabin na damun sa, kan shi na ciwo amma tsalle yayi ya nufi bayan Mummy yana cewa,"

"Mum please talk to him"

Mummy ta ce,"Idan baka natsu an duba ka ba, ba zan mishi magana ba, you've grown up ka zama big man amma kana tsoron allura chaiiiii Ahmadddd, stop that please" Mummy ta faɗa tana jawo shi ya dawo ya zauna very comfortable jin Mummy na son dizga shi, kumatun nan da suka ɗan lotsa ya ɗaure su, babu dariya ko kaɗan, ya mika tafin babbar yatsan hannun sa aka caka masa a hankali.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now