12

38 2 0
                                    

ALMAJIRA Sabon Salo

PAID BOOK

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
'''Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.'''
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


FREE PAGES
12

______________________________________

Mummy sai yanzu zuciyar ta yake mata ba daɗi tana ganin basu kyau ta ba da suka bari son haɗa zumuncin su yayi tasiri a zuciyar su har suke son tona ɓoyayyen sirrin da ya jima da rufuwa...  Daddy kam ya kasa zaune bare tsaye yana ta zufa saboda bai zan ta ina zai fara yi ma Ahmad bayani ba, ya ɗauka abu ne mai sauki, yeah abu ne mai saukin furtawa kuma abu ne mai wuyar bayani da fahimta, bugu da kari kuma basu san wani hali ɗan nasu zai kasance a ciki ba.

Ahmad kansa ya kulle ya gaza fahimtar komai, gangar jikin sa ne ke zaune a wajan amma ruhin sa baya tare da shi, tun da kunnuwan sa suka jiye masa sabon labari shikenan ya dena motsi idanuwan sa ne kawai suke kyaftawa yana bin kowa da idanu...zuciyar sa ta daskare, duk da shi namiji ne amma sai idanuwan sa suka canja launi daga fari mai kyalli ya koma ja sosai ga hawayen da suka manne sun ki su fito su barshi ya huta.

Cikin jarumta da halayen sa na ƙasaitaccen namiji Daddy ya fara magana cikin natsuwa irin na sa na manyan mutane, ya zauna daf da ɗan nasa ya rungumosa izuwa jikin sa yana jin tsananin tausayi da dana sanin furta kalmar agare sa.

"Ahmad accept your faith, bamu faɗa maka wannan maganar don cin zarafin ka ba, bamu sanar dakai don mun gaji da kai bane, kuma bamu faɗa maka hakan don son zuciyar mu ba sai don muna son haɗa zumunci mai karfi a tsakanin mu, Ahmad ka taɓa cewa bamu damu da zaɓin ka ba kullin zaɓin mu shi muke zaɓa maka, Daddy ya ce,"Yes we admit it but mun yi hakan ne because you are our favourite son, both your Mummy and Daddy love you since from the very first day we set our eyes on you,ka maye duk wani gurbi na ɗa a wajan iyayan sa ka kuma yi kane kane a cikin zuciyoyin mu... soyayyar da muke nuna maka ma daban ne

Daddy ya ja numfashi kafin ya cigaba da cewa "Ahmad duk wani ɗa da muka haifa da cikin mu wallahi ka sani ba sai an faɗa maka ba a bayan ka yake in dai nuna soyayya ne da kulawa daga wajan iyaye., Hmm ya cigaba da cewa ba zamu taɓa manta ranar da human right suka mallaka mana kai a matsayin ɗan mu halak malak kuma muka raine ka har girman ka tare da tsare ka, da kuma kusanto ka izuwa gare mu ta hanyar yi maka dukkan abin da zai zama cigaban ka" sa'annan  zaɓa maka course, zaɓa maka mata, duk munyi hakan ne saboda bama son kayi ne sa da mu ko kaɗan.

Ahmad zuwa wannan lokacin ya durkushe kasa hawayen da suka ki fita sune suka samu hanyan tsere  masu zafi suna fita daga kwarmin idanuwan sa suna sauka izuwa kuncin kumatun sa, zuciyar sa wanda ta daskare kuma ta fara bugawa sauri sauri gudu gudu ta fara yi masa suya, haka ya chukwikuye jikin sa da hannayen sa yana son yin kuka da sautin muryar sa amma abin ya ci tura kukan ma yaki zuwa sai hawaye kawai ke fita kamar wanda akai ma mutuwa.

Mummy tayi saurin zuwa wajan sa tana tallabo ɗan nata sai taga fuskar sa lokaci ɗaya ta canza launi hawaye da majina, idanuwansa sunyi ja, abin ka da jar fata tuni itama fuskar ta canza launi izuwa launin ja ja ja haka.

A kiɗime Mummy ta ɗago tana cewa Daddy,"Daddy kalli halin da ya shiga, please kayi shiru mu lallaɓa sa, Daddy ya tallabo sa shi da Nene mahaifiyar Daddy amma ina tuni Ahmady ya sume musu sakamakon wani numfashi da yayi sama sama guda ɗaya kawai sai suka ji numfashin ya ɗauke, Hankulan su a tashe suka kwashe shi kaf gidan sai asibiti...suka mika ma likita a kayi VIP A and E da shi ana duba sa.

ALMAJIRA ✔Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin