Shugaban ya cire glashin dake manne a sashin idanuwan sa, ya kalli Daddy da kyau sannan ya gyaɗa kai, daga bisani kuma ya ce,"Ba wai nazo tayar maku da hankali bane Lawal ina son nayi bincike ne dama don na sani, ka kwantar da hankalin ka kuma In Sha Allah zamu tsanan ta bincike da yardar Allah, ranar dana fara ganin sa ai na ɗauka ba ɗan ka bane, daga baya ne naji labarin kai ne mahaifin sa, sai abin ya ɗaure mun kai, amma duk da haka na bukaci da na zo gani ga ka na tambaya ko hankali na zai kwanta"

Daddy ya kara basu hakuri, yana ta basu baki har dai daga karshe suka tashi suka tafi, Papa ya sanar da Daddy cewa ba lallai ya koma London da wuri ba, wannan karan yana son ya neme Ɗan sa Ibrahim.

Daddy ya ce,"In Sha Allah nima zan taya ku binciken aboki na Allah ya sa muyi nasarar samun sa" Kuma In Sha Allah zan shigo estate ɗin nima" Daddy ya mayar musu da amsa. suka tafi shi kuma ya shiga cikin gida yana sanar da Mummy abin da ya faru.

*Gaskiya I don't know why Daddy lied to Papa, maybe is because of there selfishness , Lallai suna son rayuwa da Ahmady amma in my opinion ya kama ta Daddy ya sanar da su cewa ba shi ne mahaifin Ahmad na gaskiya ba, ya kamata ya sanar da su sun yi adopting Ahmad ne from orphanage, ko ya kuka ce readers?* amma dai mu cigaba da bibiyar labarin bamu san me zai faru nan gaba ba.*

______________________________________
KADUNA

Tun da ya kwanta bai rintsa ba saboda bai taba kwanciya a irin wannan muhallin ba,zuciyar sa na ta masa was wasi, To wa ma ya aike sa ya ce zai kwana anan, wata zuciyar kuma ta ce ka manta sun maka karamci tun da kana son khadija kuma yanzu sune iyayen khadija wanda sai ka bi ta karkashin su ka yi ladabi kafin ka samu auran ta.

Zuciyar tashi ta faɗa kogin tunani barkate, wata zuciyar kuma tace *To kana tunanin su Daddy zasu amince da auran ALMAJIRA?

Cak tunanin ya tsaya anan adaidai lokacin da yaji Anna tana tashin Baffah ya tashi yayi alwala, Anna ta shimfiɗa masa sallaya ta koma ta kwanta shi kuma ya fuskanci alkibla ya fara jero sallolin nafila, idanuwan sa biyu ya sauke su akan wata wanda ya haska ko ina, ya duba wayar sa sai yaga karfe biyu da minti uku, yana yin sallar dare amma gaskiya sai yafi wata biyar a shekara bai yi ba idan ba lokacin ramadan ba, shima ya tashi ya ɗauro alwala ya tsaya a gefen Baffah kasancewar sallayar babba ce.

Ahmad tun yana yi yana gyangyaɗi har ya bingire gefe guda sai bacci, Baffah da kan sa ya gyara masa kwanciya bayan ya sallame ya zauna yana tasbihi yana kare ma fuskar Ahmad kallo tamkar shi daya yana saurayi amma bai da wata shedar da zai ce Ahmad jinin sa ne babu...ya cigaba da sallar sa.

Kiraye kirayen sallar assalatu kunnuwan Ahmad suka jiye masa adaidai lokacin da bacci yake masa daɗi, sa'annan yaji kiran Baffah yana cewa ka tashi muyi haramar zuwa masallaci sallar asubahi.

Ya tashi yana mustsuka idanuwa ala dole bacci bai ishe shi ba amma kuma ganin yadda suke rayuwan ta su abin sai ya bashi sha'awa saboda mene yaga yadda suke bama addini muhimman cin sa, suna bama addini lokacin sa, sunayin sallah akan lokaci,
Yau da fari ita ce rana ta farko da ya ga mahaifi yana tashin ƴaƴan sa domin zuwa sallar asubahi, abin ya burge sa yadda yaga Baffah ya tashi su Anna, yayi fatan da ma ace Daddy da Mummy zasu kasance haka da ya matukar jin dadi, ya manta yaushe rabon Daddy yaje masallaci sallar asubahi duk dama masallacin a cikin gidan mu yake kuma Daddy ne ya gina amma baya zuwa jam'i, Ahmad abin ɗaure masa kai yake yi.

*Shin wai me yasa wasu masu kuɗin basa ba ma addini lokacin sa, me yasa masu kuɗi suke yin abin da suka ga dama, me yasa masu kuɗi suke ganin kamar basu da damuwa, ko dan suna ganin cewa su Allah ya wadata su da komai na more rayuwa shi yasa basu da lokacin zama su fuskanci mahallincin su, amma sam hakan bai kamata ba....shi karan kan sa bai isa yace baya wasa da sallar sa ba, amma tun da ya shigo rayuwar bayin Allahn nan tun bayan la'asar jiya da yamma bai sake barin kowacce salla lokacin ta ya wuce ba, ba kamar kwanakin baya ba da yakan haɗa sallah guda huɗu yayi su a lokaci ɗaya.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now