Na fito daga cikin motar ina tafiya kamar wacce kwai ya fashe wa a ciki sai naci karo da Baffah yana ta kokarin faskara manya manyan itace guda uku har ya gama ma yana na karshe, na ce mishi,

"Ga Mahaifi kuma uba, sadauki wanda ya san darajar ƴaƴa da mutane, shine taurarona Baffah"

Ahmad ya kura masa idanu yana jin wani abu a cikin zuciyar shi, tausayin dattijon ya kama sa, sai ya tuna kamar shi ne dattijon da ya taɓa bigewa a gadar kawo.

Ya tsugunna har kasa ya gaishe da Baffah, Baffah ya amsa yana ajiye gatarin hannun sa yana cewa "Hadiza wane ne?

"Baffah bako ne"

"Ohhooo to shiga da shi ciki gani nan shigowa ko"

Na shiga ina sallama na samu Anna
tana ta faman zarge zogale a tsakar gida zaune saman tabarmar kaba ita da Sofia.

Ahmad dai tafiya ya ke yi amma kamar an zare mishi rabin kuzarin sa daga jikin sa ganin Anna kawai yasa jikinsa sanyi lokaci ɗaya yana jin wani sabon abu cikin zuciyar sa...da kyar ya tattaro kuzarin sa da karfin halin sa ya tsugunna har kasa yana gaishe da Anna.

Anna ta amsa cike da fara'a tana cewa"Hadiza bako ne? ɗauko min tabarma a ɗaki mana"

Na riga da na ɗauko shimfiɗa masa nayi, na koma kusa da Anna ina raɗa mata zance a kunne ta ce,"Auuu shi ne to toooo barkan shi da zuwa, a ina kika gane shi Hadiza?

Na bata labarin yadda na gan shi, ta gyaɗa kai tana kara gaishe shi cikin girmamawa, tana cewa,"Zuciya ta ta amince da kai, tana shai da mun kai ɗin mutumin kirki ne, duk da bana iya ganin fuskar ka amma na karanci halayen ka"

Ahmad yayi murmushi yana daɗa jin soyayyar dattijuwar da aka kira da Anna a cikin zuciyar shi.

Baffah ya shigo rike da gatari a hannun sa duk ya yi zufa ya galabaita saboda aikin faskaren da yayi, Ya ce, "Anna na faskara itccen ba sai kin nemo wanda zai miki ba"

Anna ta jinjina kai tana cewa sannu Baffah ai dama zuwa kayi ka faskara itacen, sannu Allah ya saka da alkhairi.

"Haba mana Anna sai kinyi godiya, tsakanin mu babu godiya" cewan Baffah...,  Baffah ya tafi wajan Sofia wacce take ta faman cin dafaffiyar gyaɗa ya ɗauko ta ya dawo kan tabarmar bakon yana cewa,"Hadiza ya baki kawo masa ruwa ba kuma"

Ina tsaye na rasa tunanin me na keyi ban kawo ma bakon ruwa ba, kuma ma ya a kayi baffah yasan ban kawo masa ruwa ba, na ta shi na ɗauko moɗar ruwa wankakke mai tsabta na ɗebi ruwa na kawo masa.

Gefe na koma jin yadda ya sake da Anna da Baffah, Sofia na saman cinyar sa yana mata wasa yana cewa,"Lokacin dana gan ku ai na ɗauka jaririya ce, to amma me yasa ba ta tafiya Khadija?

"Nima ban sani ba haka aka haife ta" na bashi amsar tambayar sa

Ya jinjina kai, ya matso daf da Anna yana cewa,"Anna kawo zogalan nan na taya ki zarge wa, kina damu ai ba zaki sha wahala ba"

Kallon sa kawai Anna ta keyi tana jin wani abu na mata yawo a jiki sai taji Yaron ya shiga ranta matuƙa, hakanan suka gyara zogalen tare da ita mu kayi miya da tuwo.

Ahmad da Baffah suna ta hira har suka je masallaci sallan magriba suka jira a kayi isha'i sannan suka dawo a lokacin hasken farin wata ya haskaka ko ina na tsakar gidan namu gefe ɗaya saman baranda kuma Anna ta mana shimfiɗin tabarma ta kunna mana fitilar kwai ima gefe tana mun karin Alkur'ani.

Sosai Ahmad ya jima yana mamakin waɗannan makafi masu baiwa makanta kai ka rantse ba makafi bane, saboda yadda suke aiwatar da al'amuran su ba kaman na makafi suke yi ba, su fa komai nasu idan za suyi sai ka zata ko suna gani ne nan fa ashe basa gani.

Ahmad na gefe yana sauraron sautin muryar Anna tana karanto suratul mulk har ta kai karshe....sai abin ya bashi sha'awa yana son karatun alkur'ani amma shi iyayan sa basu wadata shi da karatun addini ba amma a hakan ma yana gode ma Allah saboda haɗɗar Alkur'ani gareshi sittin ya haddace kuma yana yawan muraja'a da kansa ya koya kuma da kansa yayi haddan sa,

Sai dai yana tantama ko iyayan sa sun iya karatun addini, asalima zai iya kirga sau nawa Mummy tayi karatun Alkur'ani a gaban sa, kuma ma kaman iyakar ta izifi biyar ne kuma da littafi sauran surorin kuma ba lallai ne ta iya ba....ya share zufan da ya keto masa yana kwaɗaituwa da ya san labarin makafin nan amma ina ya san ba zai samu hakan yanzu ba.

Anna ta kawo masa tuwon shinkafa miyar zogale da gyaɗa, sa'annan ta kawo masa fura wanda ya sha nonon kindirmo Ahmad kam ban da albarka babu abin da yake sanya wa Anna saboda wallahi yana son tuwo sai dai bai taba shan miyar zogale ba asalima  shi miyar ma bai taɓa jin daɗi da zakin miyar tuwo irin wannan ba...haka ya cinye ya siɗe tas, ya sha fura ya sha ruwa yayi gyaza yana godewa ubangiji yana godewa Baffah da Anna.

Karfe goma dai kowa na jin bacci Baffah ya lura kaman Ahmady ba tafiya zai yi ba, sai Ya umarci Anna da Hadiza da su gyara musu wajan kwanciya shi da bako.

______________________________________

To fah Ahmady lafiya dai, bako ya samu waje, readers ku wullo mun shi waje don Allah, haka ake rayuwa ne?


ALMAJIRA SABON SALO littafine da ni ke da yakinin duk wani masoyi na idan ya karanta shi ba zai yi dana sanin karantawa ba.

Na san you guys will always patronize me and stand by me saboda duk mai son ka yake kaunar ka kuma yake amfana da kai, Na san ba zai ji kyashin kai ma ka karu da shi ba.

200 naira kacal zaku biya dan samun shiga whatsapp group din da zan rinka posting in Allah ya yarda.

3119736620
Fadila Ibrahim
First bank
Sannan ku turo da shedar biya ta wannan layin

07031086858

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now