Shiyasa na kuma nemi agajin Lawal cons...ltd saboda naga suma idea ɗin su ya yi daidai da irin wanda London suke so"

Ya tsagaita saboda ya bada kofa wani yayi magana kamar daga sama yaji saukar murya irin ta ɗan sa mafi soyuwa agare sa, Ya ilahi!!!!kallon Ahmad ya sa sai da ya zare gilashin idanun sa a daidai lokacin da Ahmad ya zake magana kawai ya keyi har ya kai aya.

Kowa ya gamsu da abin da ahmad ɗin ya faɗa waje ya hau tafi ana murnar samun nasara, shugaba dai yana daskare bai san cewa dawowan sa Nigeria zai ɗago masa da zancen ɗan sa ba da bai zo ba, ya kasa gane dalilin da ko da yaushe idan yazo Nigeria sai wani abu makaman cin Ɗan sa ya faɗo masa a rai, uhmmmmmm ya ja ajiyar zuciya ya mike yana sallamar kowa tare da kiran ɗaya daga cikin yaran nasa yana cewa kuyi magana da shi zan je gida kai na yana min ciwo.

"Okay Papa Allah ya sauwwake, idan mun gama muma estate ɗin kawai zamu dawo sai mu tattauna" cewan ɗaya daga cikin yaran mai bi ma ɗayan.

"Okay to duk yadda ku kayi is okay"

______________________________________

After one month

Ahmad ne sanye cikin shiga ta alfarma wato sanye yake da shadda ruwan toka sai kyalli ta ke yi ta bugu da hula zanna bukar asalin zanen hulunan borno masu shinning ɗinnan, hannun sa na ɗauke da wrist watch baki da takalmin sa ainahin cover black sabo dal.

Yana cikin motar sa mercedes baka wuluk sai sheki kamar yau akai mata sabon painti yana tukin sa cikin natsuwa da kwarewar sa yana kan titin Ahmadu bello way dake cikin garin kaduna ya fito daga titin badarawa ya je visiting ɗin kanin sa Nurain.

Dama ya takura wa Mummy wai shi tun da ake zuwa visiting Yaya Ahmad bai zo ba, kuma ya daɗe bai gan sa ba...shine wannan karan Ahmad da kan sa yayi masa shopping na gani na faɗa, ya kuma hana kowa zuwa because a cewar shi yana son spending time with his lil bro Nurain.

Tun da safe yaje sai yanzu karfe biyar ya bar school ɗin zai kama hanyar Abuja...yana towards gadar kawo by mistakenly ya kusan kaɗe wani baba tsoho....da salati jama'an wajan suka mai cha akan zai bige musu shugaban su, Ahmad da ya daburce  hakuri kawai yake badawa yana kokarin taimaka wa makahon tsohon wanda yaga wata karamar yarinya a gefen sa tana masa sannu cikin siririn muryar ta.

_______________________

Ina zaune ni da Anna, muna hira, sanye cikin kayan makaranta, fuskata lulluɓe cikin nikabi saboda daga makaranta nake ranar lahadi...bamu san ya akayi ba kawai ganin Baffah mu kayi a kasa warwas ya faɗi shi da Sofia, take kuma wajan ya cika da jama'a ƴan tawagar Baffah suna ta bada baki akan al'amarin.

Ta shi nayi da gudu domin zuwa na taimaka wa Baffah da Sofia da kyar na iya kutsawa na shiga har wajan *SOFIA* sannu, Baffah sannu haka na faɗa ina kokarin goya ta saboda kukan da ta ke son yi.

Sunan Sofia dana furta shi ya sanya shi dakatawa ya dan juyo baya kaɗan sai yaganni lulluɓe cikin hijabi da nikab har da safan hannu, already na riga da na goya Sofia na rufe ta cikin hijab ina kokarin taimakawa Baffah ina yi masa jagora zamu bar kan titi mu koma bakin dakalin hanya.

Ahmad na tsaye ya kasa yin komai saboda jin zazzakar muryar da zai yi wuya ya manta da mai ita, ya kalli yarinyar da ya san ita ce mai muryar sai yaga alamar babu ciki a jikin ta kuma ta ɗan kara tsayi sai zuciyar shi ya bashi ba Hadiza bace.

Amma sai ya tsinci kan shi da zuwa wajan Anna tsabagen ganin kammin sa baro baro a fuskar Anna, amma bai kawo komai a ran sa ba ya durkusa har kasa yana gaishe da su yana daɗa basu hakuro akan abin da ya faru saboda Ahmad mutum ne mai tausayin talaka har cikin zuciyar sa.

Anna ta juya ta in da take sauraron muryar sa, ta ce,"Bawan Allah kar ka damu tsauyayi ne ai, kayi tafiyar ka kawai"

Tana kai wa nan ta ce,"Ku tashi muje gida baran ma ya isa hakanan, muje gida mu huta"

Yana tsaye sai a lokacin ya lura da fuskar Baffah sosai yaga kammin sa kuma a fuskar Baffah, ya ce haka kawai sai kaga mutane baka san su ba amma kaga suna kama dakai yanzu dai kamanni na, kuma kamar ma ni kaɗai nake ganin hakan tun da mutanen wajan duk basu lura da kamannin ba....ya taɓe baki ya nufi motar sa yana cewa "ina ta ɓata lokaci gwara dai na koma gida, yayi maza ya shiga mota ya bar wajan.

Muna isa gida na haɗa murhun itace na ɗaura ruwan zafi yana tafasa na haɗa ruwan wanka bokiti biyu na kai ɗaya bayan gida na samu Baffah nace yazo yayi wanka ya ɗan ji daɗin jikin shi, da kyar ya yadda da kai na nayi masa jagora izuwa bayan gidan na dawo nayi ma Sofia wanka a waje na mulke ta da mai da rub ina gama mata tayi bacci na shimfiɗe ta bayan nayi mata addu'a na fita tsakar gida na iske Anna nata kiciniyar tsane shinkafa wanda ta ɗaura bayan na sauke ruwan wanka, Na kama mata muna yi muna hira har muka gama.

Muna zaune misalin karfe takwas Anna tace "Ɗauko littafan ki ko wanne ki faɗa min sunan sa sai na miki kari"

Ni kam ina mamakin yadda Anna zata koya mun karatu, jiki a sanyaye na ɗauko jakar tawa na zauna ina lissafo mata sunayen littafan ta ce,"Mu fara da littafi mai girma wato alkur'ani.

Na buɗe karamin izu goma ina buɗe surartul muzammil ina cewa ,"Anna suratul muzammil mu kayi yau.

"Kin buɗe? ta tambaye ni

"Eh na shirya" Duk zuciyata ta kasa yadda cewa Anna zata iya min kari.........Ban dena tunani ba sai na ji siririyar muryar Anna tana jero kira'a fiye da yadda malamar mu take karanto mana, na sake baki ina kare wa Anna kallo daka ta keyi ma'ana hadda ta keyi na kalle ta na sake kallon ta sai naga kamannin ta na kyawawan mata fulani ya fito reras sai naga kaman na taba ganin mai irin fuskarta saboda yau ne na fara kura wa Anna idanu ina kallon fuskar ta duk tsahon kwanakin da mu kayi tare da su.

Har ta kai karshen sura bana biye da ita na faɗa zurfin tunani, sai da ta min magana kafin na dawo daga dogon zangon tunanin dana tafi.

Tana yi ina maimaitawa har muka gama na sake na karanta da kyau sau biyu sannan muka bar shi na ɗauko al'arabiyya ina jin ta tana ta min kamar tana gani, abin ya bani mamaki ni dai na kasa fahimtar komai saboda mamaki ya cika min kwakwalwa da zuciya da gangar jiki na.

Baffah da Sofia tuni suna ɗaki sun tsufa da yin bacci, Anna na gama min ta ce ,"Tashi muje muma mu kwanta dare nayi gobe ma rana ne In Sha Allah zamu cigaba"

Na ce,"To Anna Allah ya kai mu"

"Ameen ta amsa tana kokarin ahiga ɗaki da bisimillah a bakin ta tana addu'a"

______________________________________
ABUJA

"Daddy please ka fahimtar da ni wace Nadiya kuke son na aura???? kai ya kulle Mummy na shiga ruɗani kalaman ku, NADIYA kanwa ta fa kuke nufi" Ahmad ya kara sa maganar cike da ruɗani.

Mummy sai yanzu zuciyar ta yake mata ba daɗi tana ganin basu kyau ta ba da suka bari son haɗa zumuncin su yayi tasiri a zuciyar su har suke son tona asirin da ya jima da rufuwa...  Daddy kam ya kasa zaune bare tsaye yana ta zufa saboda bai zan ta ina zai fara yi ma Ahmad bayani ba, ya ɗauka abu ne mai sauki, yeah abu ne mai saukin furtawa kuma abu ne mai wuyar bayani da fahimta, bugu da kari kuma basu san wani hali ɗan nasu zai kasance a ciki ba.

______________________________________

ALMAJIRA SABON SALO littafine da ni ke da yakinin duk wani masoyi na idan ya karanta shi ba zai yi dana sanin karantawa ba.

Na san you guys will always patronize me and stand by me saboda duk mai son ka yake kaunar ka kuma yake amfana da kai, Na san ba zai ji kyashin kai ma ka karu da shi ba.

200 naira kacal zaku biya dan samun shiga whatsapp group din da zan rinka posting in Allah ya yarda.

3119736620
Fadila Ibrahim
First bank
Sannan ku turo da shedar biya ta wannan layin

07031086858

Madallah.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now