Wallahi bata tsoro nake ba, ban ma san miye tsoro ba a wannan lokacin ni dai buri na nayi nesa da azzaluman mutane...ina tafiya ina tsine musu albarka.

Wayewar gari tangarau a idanuwan *HADIZA* Daga lokacin na fara fuskantar matsalolin rayuwa, Wani kauye na samu kai na a ciki, na zauna na huta na awa ɗaya daga bisani na kara ɗaukar hanya sai da na isa babban gari wato garin Bakura anan rayuwar mu ta cigaba.

Bayan faruwar wannan al'amarin da wata ɗaya sai na fara rashin lafiya, amai da kasala da yawan bacci...ban san abin da ke damu na kenan ba ni dai kawai naga bana da kuzarin ɗaukar Sofia ko na goya ta....Kimanin watanni biyar ina fama da laulayi ashe ciki nake da shi, kammani na ya fara canjawa ciki ya fara girma....ranar da aka sanar dani ina da ciki wata biyar kaman zanyi hauka haka naji....amma daga baya sai na rungumi kaddara kuma muka cigaba da rayuwar mu kamar yadda muka fara.....Muna zaune lafiya a garin shine watarana suka kawo ma garin ziyara sanadin barin garin kenan nazo nan Kaduna ko zan samu mafaka....na ɗan tsagai ta ina share guntun hawaye na.

Anna kunji labarin mu, Anna ma hawaye ta share ta ja gutun majina tana cewa sannu Hadiza lallai kinyi kokari kin fuskanci ukuba ta wahalar rayuwa, ki cigaba da addu'a wata rana Allah da kanshi zai shafe miki komai kiji kamar babu abin da ya faru dake.

Nayi murmushin karfin hali ina cewa ,"Allah ya sa" Na ɗauki Sofia wacce ta jima da yin bacci ina cewa "Anna ku shigo mu kwanta dare yayi sosai karfe Shabiyu fa"

"Anna ta ce,"To Hadiza , "lallai mun cinye lokaci wajan labari bari mu shigo" ta faɗa tana takawa a hankali Na zo na taimaka musu suka shigo suka nufi uwa ɗakan su, suna min sai da safe., na kara sa kulle kofar falon na sanya sakata da kwaɗo saboda kofar waje a buɗe take kuma rayuwar yanzu komai na iya faruwa, da su Anna a buɗe suke kwana zuwan mu gidan na siyo kwaɗo kullin sai na makala idan zamu kwanta haka ma idan zamu fita sai na makala.

"Na kwanta ina jin ɗan ciki na na motsi da sauri sauri abin har yabi jikina, na saba da motsin nasa, fata na dai Allah ya sauke ni lafiya"

Washe gari

Yau tun da asubahi na gama mana komai na aikin gida, nayi abinci na ci sannan na shirya na zumbula dogon hijabi, ba tare da na musu sallama ba na kama hanya kai tsaye kofar makarantar nan mai mashin ɗin daya ɗauko ni ya tsaya sai dai a rashin sani mun tsaya daidai kan hanya bayan wata mota ce wadda ta tura mu muka faɗa cikin kwata na buga ciki na da karfi na kuma buga goshi na yayin da tuni jini ya fara biyo kafafuwa na, kai na kuma yana sara min.

Babban mutum ne da iyalan sa su suka yi sanadiyar hatsarin sune naga sun fito hankali tashe sun tsorata da ganin halin da nake ciki......cikin kankanin lokaci aka fito dani ana kokarin sanya ni a mota saboda sun lura na buga ciki na ga kuma jini, amma ina tuni na suma.

4hours after

Na farka da kyar nake iya lumshe idanu ina buɗewa a hankali har na buɗe tangaran lokacin dana shafa cikin jiki na sai naji wayam, kamar ma ba a taɓa halittan wani ciki a wajan ba, tsabagen ya shamule ba komai amma kuma kasan mara na kaman an ɗaure da wani abu.

Kai na naji yana ɗan sara min, take likitoci suka shigo suna min sannu, bayan yamin wasu ƴan tambayoyi.

"Ya ce, "Ke matar aure ce?

"Na ce "Aa"

"To ina iyayen ki?

"Nace suna rafin guza" okay zamu iya kiran su yanzu ki bamu lambar wayar su?

"Nace "Ba su da waya, likita ina cikin dake jikina wai? Na tambaya da sauri"

"Ya share zufan daya keto masa duk da sanyin AC da yake ratsa ɗakin  majinyaci, sannan ya ɗaga kai yana yi ma wata magana Ya ce,"Nurse please"

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now