Mahaifiya ta Sunan ta FATIMA BUZU sanadin Mahaifin ta saboda sunan sa kenan *BUZU*, Kawayen ta da wasu ma ko in ce kowa ma *BUZUWA* ake kiran ta da shi.

Haifaffiyar garin In-gall ce asalin su buzaye ne, Baban ta da Maman ta duk sun rasu, tana zaune da Kakar ta wacce ita kaɗai ce ta rage mata duk faɗin duniyar nan, Kakar ta tana sana'ar Chukwi da Nonon rakumi saboda Mahaifin Ummu na ya rasu ya bar Rakuma sama da guda ashirin duk gadon Ummu na ne.

Babban kasuwan garin Ingall kasuwan da Mahaifin mu yake kasa kayan sana'ar sa su dangin turarukan sudan, da humra na sudan, turaren wuta, kayan lalle, sarka da ɗan kunni, agogo da abin hannu, jigida da sauran su, suna da yawa.

Wannan ita ce sana'ar Mahaifi na.

MAFARIN HAƊUWAR SA DA UMMU na.

Gefen shagunan su akwai ƴan mata sama da goma masu tallan *chukwi* da Nonon rakumi.

Cikin ƴan matan dake sana'a a wajan a ciki Mahaifi na yayi tozali da Mahaifiya ta, karamar cikin su alokacin don ba ta da jiki sai dai irin murjajjan jikin nan irin na buzaye, Fara ce tas kaman ka tsungule ta jini ya fita.....Idan aka zo fannin kyau, to mahaifiya ta kyakkyawa ce ajin farko, kyan ta da natsuwar ta shi yake sa mazan kasuwan suyi ta zolayan ta wasu kuma suna son ta amma tsarin rayuwar ta bata kula kowa.

Kamar da wasa Mahaifi na ya fara cusa kanshi wurin Ummu na, tun tana masa wulakanci, kullin rashin mutincin yau daban na gobe daban, daga baya sai ya dena mata magana a kasuwa....Rana musamman yake warewa ranar da bata zuwa kasuwa shi kuma zai kulle nasa shagon ya shirya tsab cikin shiga ta alfarma har da tsaraba yaje wajan Ummu na.

Tun bata fita har dai Kakar ta ta yi mata nasiha ta fara saurarar shi...Allah cikin ikon sa soyayya mai karfi ya shiga tsakanin su da Ummu na sai kaka ta nemi ganin iyayen sa Mahaifin mu saboda ta lura yaran suna son junan su.

Amma sai Mahaifi na ya ce bai da kowa shi kawai a ɗaura musu aure, Yayi alkawarin zai kula da Buzuwa kamar yadda suke kiran ta, kuma yayi alkawarin anan Ingall zata zauna su karaci rayuwar su tare.....Jin haka sai Kaka ta amince kuma ta bashi auran Ummu na.

Ana haka sai ta kwanta rashin lafiya tun ma kafin a fara maganar aure, ashe ciwon ajali ne ko wata ɗaya ba tayi tana jiyya ba, Allah mai kowa da komai ya ɗauki ran abin sa.

Bayan rasuwar ta da wata ɗaya, Mahaifi na ya uzzura wa Ummu na akan ta aure sa, babu yadda ta iya saboda bata da kowa gashi ya kalallame ta da kalaman soyayyah, Ummu na dai ta auri Mahaifin mu, suka zauna a gidan Ummu na,..saboda shi dai bai da komai a wannan halin.

Tashin farko taci tuntuɓe da ciki na, ta haife ni ƴa mace kyakkyawa.....Mahaifin mu ya siyar da rabin rakuman Ummu na, wai zai kara jari a kasuwan cin sa, kasancewar Ummu na mace ce mai hakuri sai bata hana sa ba.

*Abiy* shine sunan da nake kiran Mahaifin mu tun tasowa ta, shekara ta ɗaya, Abiy ya sai da ragowar rakuman Ummu na, Sannan lokaci guda yace mata zasu bar Ingall zasu koma *NIGERIA* saboda ya canja sana'a.

Ta tambaye shi sana'ar me ya koma, amma yaki gaya mata komai.

Da fari Ummu ta ki yadda amma sai ya cigaba da kalallame ta da kalamai masu dadi har dai ta yadda, suka tafi Kasar Nigeria inda suka sauka a garin BORNO, muna wata shiyyar daga cikin garin borno.

Abin mamaki shine Abiy ya kasa kama wa Ummu na gida kullin muuna rakuɓe rakuɓe a wata ƴar rumfa, idan ruwan sama ya sauka haka za muyi ta shigewa gidan mutane muna fake wa.

Jagab haka rumfar mu take jikewa da ruwa ranar sai dai mu kwana waje cikin sanyi haka muke rayuwa, babu gata ko kaɗan, Sai ya kasance mun saba da rayuwar Ummu na kuma kamar dai Abiy ya rufe mata baki, bata iya ce mishi kala balle har ta kai da tace masa yana mata ba daidai ba,
haka ta cigaba da zama da shi, Kwatsam sai ya fara tafiye tafiye ya bar mu cikin wannan halin.

Idan zai tafi baya bamu ko sisi na abinci, babu, Ummu na ita ke faɗi tashi tai ta bara tana nemo mana abin da zamu ci.

*SANADIN FARA BARA TA*

Wannan wani kalan uba ne, duk da ban san me kalmar uba take nufi ba, amma na san cewa shine yake tare da Ummu na, Abiy idan ya dawo babu wani kewar mu da yake yi zai zo yayi ta wa Ummu masifa wai ta dena yawan bara, tana zubar masa da mutunci, meyasa bazata kama sana'a ta rinka yi ba.

To ya bata kuɗin sana'ar, Bai bata ko sisi ba hasali ma duk tafiyar sa da dawowarsa tafiya ɗaya ce ya ajiye mata bandir ɗin kuɗi ƴan ɗari biyu biyu.

Ummu na takaicin Abiy ya ishe ta, babu abin da take sai kuka da kunci har ya tafi, saboda bata taba tunanin haka rayuwa zata canja mata ba.....Kuma hakan ba shi zai sa ya ɗauki kuɗi ya bamu ba, har ta kai ma idan Abiy ya tafi sai shekara shekara yake dawowa, idan yaga dama ma sai yayi shekara biyu bata sanya shi a idanunwan ta ba.

Dama ba wani sanin sa nayi ba, to ko ya dawo ma tsoron shi nake bana zuwa wajan shi saboda yana yi ma Ummu na masifa da faɗa....wani dawowa da yayi wanda zan iya cewa kaddarar samun cikin Sofia ne, wanda tun daga wannan dawowan har izuwa rana mai kaman ta yau bamu sake sanya shi cikin idanuwan mu ba.

Ummu na, ta sha wahala da cikin Sofia, alokacin ina da shekaru goma sha biyu, nice nake ta ɗawainiya da Ummu na, har Allah ya sauke ta lafiya, murna nake tayi an sama min ƴar uwa mace sai nan nan nake da jaririya, Da kai na, na zaɓa mata suna SAFIYA, Ina kallon yadda Ummu na take mata wanka, aiki na raino da goyo,Haka zan goya ta muyi ta yawan bara gida gida, lungu da sako, ana kiran mu da ALMAJIRAI wasu mazan sai suce za suyi lalata da mu ni da Ummu na.....Kaskantacciyar rayuwar sa muka fuskan ta, wallahi ko da wasa ban taba bin maza ba wai saboda abinci, ban taɓa rike hannun ɗa namiji ba duk da cewa na san bamu da shi, kuma yawan ci sai suce sai mun bada kan mu kafin za'a bamu bara.

Wallahi ko zamu kwana da yunwa dai mun gwammaci mu ki yadda da bukatar su, sai dai kullin mu rakuɓe a rumfar nan muyi ta kuka, haka muke kwana a zaune tsabagen kada cikin dare a shammace mu ai mana wani mugun abu.

Allah yana tsare mu har wani lokaci da sofia takai shekara biyu bata tafiya kuma bamu san dalilin rashin tafiyar ta ba, abubuwa sai kara gaba gaba sukeyi, suturar kirki ma bamu da ita, kullin cikin tsummokara muke, kayan mu sun yayyage sun koɗe, babu kyan gani.

So tari sai na iske Ummu na tana kuka idan na tambaya sai tace "Har yanzu Abiy bai dawo ba, bai zo ya duba mu ba"

"Ni zan ta lallashin ta ina mai kwantar mata da hankali, in gwada mata tun da tana da mu babu komai,In Sha Allah wataran sai labari.

Wata rana ranar da ba zan taɓa mantawa da shi ba a tarihin rayuwa ta.

______________________________________

ALMAJIRA SABON SALO littafine da ni ke da yakinin duk wani masoyi na idan ya karanta shi ba zai yi dana sanin karantawa ba.

Na san you guys will always patronize me and stand by me saboda duk mai son ka yake kaunar ka kuma yake amfana da kai, Na san ba zai ji kyashin kai ma ka karu da shi ba.

200 naira kacal zaku biya dan samun shiga whatsapp group din da zan rinka posting in Allah ya yarda.

3119736620
Fadila Ibrahim
First bank
Sannan ku turo da shedar biya ta wannan layin

07031086858

Madallah.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now