Yana da saurin bata rai idan abu bai masa ba, musamman tun da ya rasa matar sa to fa ya tsani kalmar aure ko da wasa baya son a ambaci wannan kalmar, shi yasa ransa yake baci ya kuma tafi hotel a duk sanda Daddy ko Mummy suka ambaci kalmar baya so ko kaɗan.

7:00am

Ya buɗe ido sai ya ganshi a hotel ɗin yama manta anan ya kwana saboda bacin rai, ya tashi ya zauna yana mamakin yau ita ce rana ta farko da ranshi ya bace amma bai gayyaci mace izuwa hotel ɗin ba, ya dade yana sake sake a zuciyar tasa sannan ya mike ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin dark blue suit mai matukar sheki da tsada, ya ɗauki briefcase ɗin sa sannan ya kulle ɗakin ya tafi office.

20min ne ya kai sa office ya shiga employees ɗin sa suna ta faman gaishe shi har ya shiga ainahin office ɗin sa sai da ya fara bawa secretary order a kawo masa hot chocolate tea, da cookies sannan ya shiga ya zauna a wani bangare na L-Shape cushion masu kyau har da T.V ya kunna yana kallon news jim kaɗan ta shigo da tray a hannun ta ta aje masa sannan tayi excusing ɗin sa ta fita.

Yana zaune amma tunanin yarinyar nan shi yake masa yawo a kwakwalwa, da kyar ya yi yaki da zuciyar sa ya soma kokarin ignoring ɗin ta aduk sanda zuciyar zata kawo masa tunanin ta sai ya kauche hanya........amma ya abin zai kasance sai Allah.

Knocking kofar da akayi ita ta dawo da shi daga trance ɗin daya shiga, ya amsa yana cewa "Yes come in"

Murɗa kofar akayi aka shigo Daddy ne sanye cikin suit shima irin ta Ahmad.

Cike da ladabi da kaskantar da kai ya durkusa ya gaida Daddy kanshi a kasa yasan cewa ya bata masa rai jiya amma ba laifin sa bane zuciyar sa ce, kuma su sun ki gane wa.....Yana tsugunne kanshi kasa yana jiran amsar Daddy amma shiru ba amsa sai ya ɗaga kai ya kalli Daddy, Hmmm

Daddy na tsaye abinshi da alama shima ranshi a bace yake da Ahmad ɗin, ilai kuwa sai yace "Time yayi za'a fara meeting" yana kai wa nan yayi hanyar fita amma Ahmad yayi saurin dakatar da shi yana cewa

"Daddy don Allah bazan iya jure fushin ka ba, na san a ƴan kwanakinnan ina ɓata maka rai amma babu yanda na iya ne, Don Allah kuyi hakuri zan nemo Mata In Sha Allahu Daddy"

Daddy yace "Mind you this is office, duk wata magana ta gida kasani sarai Ahmad bana yin ta a office so idan kasan ka ɓata min rai meet me at home" Daddy na kai wa nan yayi gaba abin sa.

GADAR KAWO
KADUNA STATE______________________

A takaice dai nan muka kwana zaune tare da wasu mabaratan, wasu daga cikin mu sun tafi gidajen su.

Muka wayi gari da safe duk muna zaune ni da Sofia sai wannan Dattijo mara lafiya don shima nan ya kwana, na tafi na siyo mana abinci wannan karan har da mara lafiyan nan da mai tsaron shi.

Na mika masa takeaway na abinci sai naga ya fashe da kuka yana min godiya su ka ci muma muka ci, jim kaɗan muna ta ɗan hira sama sama ina ɗebe masa kewa sai ga wasu makafi sun karaso wajan da sallamar su.

"Baba ya jikin?

Muryar dattijuwar macen ta sanya ni kare mata kallo, tana magana kamar wata likita tare da nuna tsananin kulawar ta ga mara lafiyan, Ban yi kasa a gwiwa ba nayi saurin cewa "Shin dama ɗan uwan ku ne shine kuka tafi kuka bar sa da yunwa, babu wani daga cikin ku da yazo ya duba shi, Haba mana ku kuwa"

Na faɗa ina girgiza kai alamar abin bai yi tsari ba, sai naji namijin na cewa,"Baba wacece wannan a kusa da kai kuma?

Mara lafiyan yace,"Baffah bakuwa ce jiya ta iso garin nan, kuma nan ma ta kwana tana ta kula da ni yau kam ma har da abinci ta siyo min" ya karashe maganar yana hawaye.

Nayi saurin tashi ina son goge masa hawayen amma ina wani tokarin da a kayi min a ciki na da hakan ya sanya ni yin sauti kaɗan ina dafe cikin na tsugunna, Mata makauniya tayi saurin cewa lafiya baiwar Allah, Me ya same ki?

Sai mara lafiyan nan ya ce "Anna ciki ne da ita tun zuwan su na lura da hakan ina kwance amma ina kallon su sannan kuma da akwai karamar yarinya a tare da ita da alama bata tafiya.

Ya kalle ni ya ce,"Yarinya waɗannan sune shugaban mu, duk wani mabaraci ya san da zaman su, kuma su suke raba kuɗin sadaka aduk sanda aka bayar.

Anna tayi saurin cewa," Baiwar Allah ina iyayen ki kike yawo haka, yakamata mahaifiyar ki ta hakura da neman kuɗin nan ki zauna agida duk da ban san halin da kike ciki ba"

Sai nace," Bamu da kowa Anna, na faɗi sunan kamar yadda naji mara lafiyan ya ambata, na cigaba da cewa daga Zamfara muke ne jiya muka iso kaduna, daga ni sai kanwata.

Duk da Anna bata ganin mu ina kallon fuskar ta, tana facing in da muke naga ta zubar da kwalla tana sharewa.

______________________________________
ALMAJIRA SABON SALO littafine da ni ke da yakinin duk wani masoyi na idan ya karanta shi ba zai yi dana sanin karantawa ba.

Na san you guys will always patronize me and stand by me saboda duk mai son ka yake kaunar ka kuma yake amfana da kai, Na san ba zai ji kyashin kai ma ka karu da shi ba.

200 naira kacal zaku biya dan samun shiga whatsapp group din da zan rinka posting in Allah ya yarda.

3119736620
Fadila Ibrahim
First bank
Sannan ku turo da shedar biya ta wannan layin

07031086858

Madallah.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now