Na share kwallar data zubo min, muna ta tsallake gawawwakin mutane ana ta janye su gefe da alama sallah za ayi musu ko zasu samu damar shiga rami ma oho ni dai na samu waje kusa da ƴan uwa na mabara ta na zauna ina tunanin rayuwa.

ABUJA maitama
______________________________________

Da murna suka rungume juna bayan sun haɗu, Dawowar Ahmad kenan daga Zamfara.

"I miss you bro" cewar Kamal yana shafa keya.

Ahmad ya ɗaura hannayen sa akan kafaɗar ɗan uwan nasa yana cewa"Bro ka girma fa shekara guda ne ban ganka ba amma dubi yadda ka kusa kawoni jiki"ya faɗa teasingly
Ya cigaba da cewa"Anya ma medicine ɗinnan kuke karantawa,Uhmmmm Ahmad ya faɗa yana dariya

Kamal kamar zaiyi kuka ya ce"Yayaaaaa mana"

Dai dai lokacin da suke shiga main palourn gidan bangaren Mummy, Tana zaune saman sofa ita da Nadiya suna kallo, Nurain kuma yana dinning yana assignment.

Suna zama Daddy na shigowa cikin natsuwar sa da tafiyar sa irin da manyan mutane yayi gyaran murya bayan ya zauna.

Mummy ta tashi da sauri da ɗauko masa ruwan swan mai sanyi da cup ta tsiyaya masa ta duka har kasa tana mika masa ya karɓa fuskar shi da fara'a, bayan ya sha ya sanya mata albarka akan ladabi da biyayyar da take yi masa.

Ahmad ya duka har kasa ya gaida Daddy.

Daddy ya amsa yana cewa"Ka dawo lafiya, Ina fatan komai ya tafi lafiya lau"

"Yeah, In Sha Allah dama idan na dawo ne zan karasa musu sauran project ɗin su sannan sai a aika musu da shi" Gobe in Allah ya kai mu Daddy muna da Conference meeting da Raynolds Construction company ya kamata ka shigo gobe Daddy"

"Uhmm Allah ya kai mu Ahmad, ina fatan babu wani matsala kuma?

"Ah nooooo babu komai dama abin kenan"

"Okay Ma Sha Allah, to ya maganar mu kuma ta wancen ranar?

"Daddy wace magana kuma, Ahmad ya tambaya kamar bai gane abin da suke nufi ba.

"Are you serious, you've forgotten?

"Ahmad ya sanya yatsun hannayen sa a tsakiyar kansa ya shafa lallausan suman sa sannan ya ce "Daddy not again please, am not ready for now, I need space" Ya faɗa yana bata rai.

Daddy ya kalle shi sai bai sake ce mishi komai ba, ya mai da kallon sa zuwa ga Nurain wanda yake dinning yana assingment yana masa maganar makaranta yana cewa,"Nurain boarding school ɗinka is ready tun da ka nace kai FGC MALALI kake so duk school ɗin dake Abuja ba wanda ya maka sai na kaduna, anyway komai ya zama ready next week monday zamuje ai maka registration.

"Yes, Nurain ya faɗa jikin Mummy yana murna yana cewa "Daddy ai Salis ne da Ayman duk suna cen ni kaɗai na fara a nan kuma na saba da su, gwara kawai nima akai ni cen ɗin.

Mummy tace,"Allah ya ba da sa'a Nurain ni dai fatana ka mai da hankali ko Daddy ta ɗan dubi in da Daddy yake wanda yake kallon Ahmad hankalin shi kachokam yana kan yaron amma shi Ahmad ya kasa gane in da Daddy ya dosa, ya girgiza kai ya koma kan Nurain yana mayar masa da amsa.

Ahmad ya ta shi ya tafi flat ɗin shi,ya nufi wani ɗaki daga cikin side ɗinsa babban waje ne wanda ya ajiye kayan zanen sa dana awards ɗin da ya samu tun suna degree a UK da project ɗin da yayi lokacin da ya gama Masters, zane masu kyau da sha'awan kallo.

Daram ya zauna a wata kujera yana facing ɗin plain board yana son zana abu amma zuciyar sa na masa kuna ya rasa me yasa da yaji maganar aure ranshi yake baci....shi ya yadda da kaddara bawai soyayyar sa da nasreen ce ta hana shi kara aure ba illa baya son yayi wani auran abin da ya faru da shi ya sake faruwa.

Zuciyar sa na kawo masa zanen yarinyar a idanuwan sa amma hannun sa na rawa karo na farko kenan a tarihin rayuwar sa tun yana yaro bai taba ɗaukan pencil ba tare da ya zana wani abu ba, yau kuma ya kasa, kuma fa ga fuskar ta nan tana masa yawo a idanuwan sa amma ya kasa ɗaukan pencil haka ya karaci zaman sa ya fita ya tafi hotel yana mamakin lamarin.

************************************
RAFIN GUZA, KAWO
KADUNA STATE

Tsakiyar titin kasa karkashin gadar kawo wani mai bike ya banke wani dattijo a rashin sani, iyalan sa suka rugo a guje suka ɗauke sa zuwa gefe, mai mashin ɗin yana ta bada hakuri.

Baffah ne yayi saurin zuwa wajan da taimakon matarsa Anna, Mutanen suka sanar da su cewa goshin bawan Allahn ne jini ke zuba, Anna ta tambaye sa shin akwai inda ke masa ciwo ne, ya ce "Aa kan sa ne kawai in da yaji ciwo shine yake masa zafi sai jikin sa kuma yana masa rawa.....da alama ba wannan bane karo na farko da Anna ta soma wannan aikin.

Anna ta bawa wannan bawan Allan taimakon gaggawa sannan ta samu biro da paper tayi rubutu, ta karɓi kuɗi a wajan mai mashin ɗin da yayi sanadiyar accidents ɗin ta aika aka je chemist, jim kaɗan aka dawo, Drip ne, sai Canuler, da kuma cotton/audiga  da Bandage sai allurar pain reliver da syringe da kuma spirit.

Taimakon gaggawa ta bashi, ta mai allura sannan tare da taimakon mutanen gefen ta, ta goge masa ciwon da spirit sannan ta nemo jijiya duk da bata gani Allah mai iko sai naga ta sanya syringe a daidai wajan vein ɗin, ta tura Canuler sannan ta sanya masa drip cikin natsuwa take ce masa shin babu in da yake maka ciwo?

Shi kuma yana daɗa basu amsa daga karshe iyalan sa suka zazzauna gefen sa suka rike ruwan yana shiga a hankali, Shi kuma yana kwance.

Ni dai Diela I was surprise, su ɗin fa makafi ne, amma dama Anna likita ce ko miye? ban isa na baku amsar ku ba yanzu nima bin labarin nake yi.

Bakura_______________________________
Days after

Yau kwana biyu kenan wata musiba ta faɗa ma ƴan garin bakura ƴan kidnappers da naji ana kiran su da bandits suka shigo garin babu zato babu tsammani sai kashe kashe su keyi cikin wannan tashin hankali mu mabarata da muka kasance bamu da matsuguni muka rasa in da zamu dosa, to kowa ta kan sa yake yi bamu da in da zamu ɓoye saboda sun kona gidajen mutane, sun kona shagunan mutane da duk wani wajan da mutum zai ɓuya face Masallaci, shima masallacin suna kewaye da shi suna ganin mutum ko babba ko karami harbe shi suke yi idan mace ne kuma ta musu kyau sai su sanya ta a mota su tafi da ita.

Wannan dalilin ne yasa damu da sauran mabarata da kaɗan daga cikin  jama'an garin muka yanke shawaran barin garin tare da yin tattaki ta hanyar zamfara to katsina in da sai da muka billa ta jibiya.

Hakika na tsorata da wannan lamari ni Hadiza yau kwanan mu uku a hanya muna tattaki gamu ga ayarin mabarata, tafiya kawai muke yi kamar masu gudun hijira, Sofia na baya na goya ta idan na gaji kuma sai na sauke ta na huta kafin suyi nisa haka dai muke ta tafiya.....Allah sarki faruwar al'amarin nan sai ya tuna min da mahaifiya ta shekara ɗaya daya wuce na kuma tuna kaddarar data same ni, Ba wannan bane farkon shiga tashin hankali na ba, kawai na tsorata ne saboda halin da nake ciki, kuma kanwata ba kafa.

Muna isa Jibiya wasu daga cikin mu har da mabarata suka yaɗa zango a garin jibiya in da ni kuma na rasa me ya kamata nayi.
Kwana mu kayi a titi da asubahi muka  ɗau hanyar kaduna domin ƴan uwan mu mabarata sun shaida mana cewa akwai mabarata dayawa a kaduna kuma ana samun kuɗi sosai...Hmmmm To ya zanyi ni Hadiza tun da haka na tsinci rayuwata ko na ce zan zauna a garin jibiya wa na sani, gwara ma kawai mu bi sauran zuwa kaduna.

Tun safe muke tafiya muna hutawa har Allah ya kawo mu Dutsin ma, Anan na rabu da su Allah ya taimake ni wani daga cikin mu ya tausaya min hakan yasa sukai ta tsayar da motoci sunfi goma har Allah yasa wani bawan Allah mai sharon ya taimaka min na shiga motar sa ni da Sofia, muka bar sauran ayarin har da hawaye na.

______________________________________
ALMAJIRA SABON SALO littafine da ni ke da yakinin duk wani masoyi na idan ya karanta shi ba zai yi dana sanin karantawa ba.

Na san you guys will always patronize me and stand by me saboda duk mai son ka yake kaunar ka kuma yake amfana da kai, Na san ba zai ji kyashin kai ma ka karu da shi ba.

200 naira kacal zaku biya dan samun shiga whatsapp group din da zan rinka posting in Allah ya yarda.

3119736620
Fadila Ibrahim
First bank
Sannan ku turo da shedar biya ta wannan layin

07031086858

Madallah.







ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now