Wasu kuma zasu kwanta suyi baccin su kalau da safe suyi wanka suci abincin hotel ɗin sannan su kama hanyar su, su tafi.

Amma da akwai mace ɗaya wanda ta nace masa kuma shima yafi kiran ta saboda wayewar ta daban yake da sauran ƴan matan, wacce ya kira ranan. sunan ta zainab ana ce mata *Zee mama*

Zee tana son Ahmad har cikin ranta wanda tun bayan rasuwar matan sa taso ya aure ta amma haƙan ta bai cimma ruwa ba....Har wa yau tana ta fafatawa don ganin zuciyar ta ta samu gurbi acikin zuciyar Ahmad sai dai kash shi ko ɗigon soyayyar ta baya ji amma kuma yana aikata alfasha da ita.
***************

Yau asabar yau ne kamal zai dawo daga UK hayaniyar gidan ma kaɗai ya isa mutum ya gane.

******

Flat ɗin Daddy, ɓangaren cin abinci wato dinning cen na lekooo mana sai naji Mummy Na'ima na magana.

"Daddy wai me yasa Ahmad yake haka ne, na faɗa masa kar yayi tafiyar nan zuwa Zamfara amma shine ya tafi, Wai babu wanda zai je ne daga office dole sai shi"

"Calm down Mummy bana son kina ɗaga hankalin ki akan karamin abu, gobe zasu dawo In Sha Allah" Clients ɗin mu ne suka ce su a Zamfara suka sauka kuma baza su iya karasowa Abuja ba saboda biki zasu yi, if not da Ahmad bazai takura kan shi ba, Kin san yana kokari sosai"

"Uhmm amma duk da haka ai kanin sa ne zai dawo ba zai tsaya su gana ba shekaran su guda fa ba su haɗu ba"

"Na'ima kullin ina faɗa miki ki rage shiga tsakanin su, ta iya yuwuwa yanzu haka sun yi waya, abu mai sauki ma tun da gobe gobe In Sha Allah zai dawo" cewar Nene, takan shigo ta duba su, kuma suma suna duba ta sosai, Nene ta cigaba da cewa "Bana son na kara jin wata maganar kuma"

Kowa ya cigaba da cin abincin sa , suka gama kowa yana damuwan sa jim kaɗan sai ga dawowar Kamal lallai ya sha tarba wajan ƴan uwa, ana ta wasa da dariya...bayan yaci abinci ya huta yayi wanka, ya fito shan iska sai ya iske mummy zaune a palon ta, ya kara sa yana matsa mata tafin kafa yana cewa "Nan da shekara biyar ina dawowa zan ringa miki physiotherapy, ya faɗa yana keta

Mummy tayi murmushi tana cewa "Allah ya ida nufi son, Allah yasa albarka a karatun"

"Amin Mummy", yawwa Mummy wai ina Yaya Ahmad ?

"Yaya ya tafi Zamfara amma gobe zai dawo In Sha Allah" Cewar Mummy

"Okay let me give him a call"
Ya tashi yana cewa "Excuse me please"

"Okay, you are excused and please my regards to him idan kun yi waya, tell him that nayi missing ɗin sa"

"Okay Mummyn Ahmad" kamal ya faɗa yana tafiya da ɗan gudu yana dariya.

************************************ZAMFARA STATE
BAKURA

Motoci guda biyu ne suke ta faman gudu a hanyar Zamfara ko da suka iso wani kauye, Ahmad ya hango babban masallaci sai ya umarci driver da ya tsaya suyi sallah, suka yi parking ya fito sauran escorts din sa duk suka fito suna biye da shi, bayan sun yi parking a waje mai kyau wasu suka tsaya a wajen motocin su, wasu kuma suka shiga masallaci.

20min suka ɗauka a cikin masallacin kafin duk suka fito suna kewaye da shi yayin da yana tsakiyar su, suna iso wa bakin titin mabarata suka fara bin sa suna bara haka ya rarraba musu kuɗi bandir ɗin ƴan dari biyu biyu, mai yawan gaske kuma kowa ya samu.

Yana tsaye jikin motar tasa ya gama raba kuɗin zai buɗe kofar kenan sai yaji ana cewa "Hadiza ki zo da gudu ya gama rabon fa"

Tsayawa yayi yana lalubo sauran canjin da yake da shi to his own surprised sai yaga babu sauran canji sai bandir ɗin dubu ɗaɗɗaya......ya buɗe motar zai shiga sai yaji zazzakar muryar ta tana cewa "Yallaɓai a taimaka mana da saka don Allah"

ALMAJIRA ✔Donde viven las historias. Descúbrelo ahora