page 7

63 9 0
                                    

*SAI NA GA BAYANKI*

              *NA SADNAF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*PAGE 7*

             "Kishatu karki min haka kishatu ke fa kanwar Rasheeqa ce uwa daya taya zaki fada mata Ina nemanki,taya zaki tura mata videon mu Kishatu ki duba abinda zai je ya dawo"

" Kasan da ni kanwarta ce ka fara nemana,Ina ga lokacin da ka fara zuwa dakina sai da na nuna maka matsayina a wajen ta ka rufe idonka saboda san zuciya ka nemeni  Alhaji kana wasa dani yadda kake tunanin zaka yaudareni wai ka ringa amfani dani ita kuma yayata itace matarka ta sunna wallahi Kai ma bazaka samu yadda kake so ba.

Kishatu tace tana hararar k'ofar tare da tuna ranar da ta fara taka kafarta gidan Rasheeqa da driver yaje har Tasha ya d'auko ta dan dama Rasheeqa  tasan  zata dawo Nigeria dan lokacin da Aurenta ya mutu bayan ta gama idda haka ta koma ta zauna a gidansu da yayyenta ke zaune duk da matansu da Yara sai ya zama ita kadai ce jal tunda dama su uku ne Matan Aunty Ama Rasheeqa sai ita,ita kuma kadai ce dan Aunty Ama da Rasheeqa duk suna Nigeria,zaman takura da takeyi yasa Yaya Nura ya kira Rasheeqa a waya yace Mai zai hana Kishatu ta dawo Nigeria ta zauna da ita tunda tana da hali,zaman da kishatu keyi anan din kamar da takura,kuma ya kamata ko yayane ace ta dan bar garin saboda ta nisanci tsohon mijinta tunda ya raba ta da yayanta.

Rasheeqa kuwa tace ba komai zata turo kudi a saka   ta a mota ta taho Nigeria,haka kuwa akayi Rasheeqa ta tura kudin mota ta taho Nigeria,kamar ta taka rawa a lokacin da taga a katon gidan da zata zauna,dan mijinta ba Mai kudi bane sai dai rufin asiri,Abu daya kawai ya sanyaya mata gwiwa taga kamar Rasheeqa bata da sakin fuska sosai,abinta dai kamar Mai jinnu yau ta mata mutunci gobe ta hade Mata rai,amma mijinta kuwa ta lura tunda tazo gidan yake nacewa kallonta kamar mayye indai zai ga Rasheeqa ta bada baya haka zai kura mata ido idan ta fito tana aikace aikace duk dan ta Kara siye Rasheeqa dan yadda tazo dinan bazata so komawa inda ta fito ba, satinta biyu kawai farinta ya kara fitowa tayi wani irin fresh da kyau saboda Jin dadin da ta Samu,inda Alhaji mijin Rasheeqa ya zama kamar tsohon mayye dan har zuwa.yake Yana lekanta.

Sau biyu kawai da ta raka Rasheeqa unguwa taga mazan garin kamar su cinyeta danya kamar basu taba ganin farar mace ba,dan a ranar ma sai da mutane uku suka kasa hakuri suka biyota har gida,Wanda inda ta baro kusan dukansu masu kyau ne farare kyaunsu bai wani dadda mazan da kasa ba,sai abin yazo mata bambarakwai a ranar Rasheeqa ke fada.mata idan ta kwantar da hankalinta yadda mazan garin kano ke San farare kyawawa ko wata uku baza tayi ba zata samu mijin Aure kuma Mai kudi,ai take taji kamar zugata tayi, Rasheeqa bata da rowa da yake ta fita killewa ita ta jibgo mata kayan gayu, ta fara gayu amma indai mijinta na nan haka zata ce ta Saka hijabi ita bata so,tuni tayi wani irin clean, kasancewar bata san kowa ba ta nemi izni a wajen Rasheeqa akan tana so ta dan zaga gari bata hanata ba ta dauko dubu goma ta bata tace har gidan Aunty Ama zata karasa dan tana da lambarta tana kuma shakkar Aunty Ama sosai dan zata iya cewa duk da uwarsu daya ita bata wani jawota a jiki ba,zata iya yiwa kowa tsaraba a lokacin da duk suke can Niger amma banda ita kafin mamansu ta rasu har damuwa ta ringa yi da yadda Aunty Ama take mata,idan tayiwa Aunty Ama magana sai tace ita haka kawai bata mata ba tayi zubi da munafikai.

Koda ta tashi shiryawa gayu ta dauka sosai cikin wani doguwar rigar atamfa Tayi parking din gashinta taje yiwa Rasheeqa sallama kenan ta saki dariya tana "Kinyi kyau Kishatu amma tumbi ya balain kwafsa miki"

Sai kishatu ta taba tumbinta ta tabe baki tana "Tunda na haihu wallahi nake fama da wanan tumbin shine kawai ya min cikas"

Jeki ki dawo Ina da ragowar maganin tumbin da na siya a wajen mmn mujaheed Mai siyar da maganin sanyi da na nono magangunan ta na da balain kyau idan kika dawo zan San Miki dama ya kusa karewa sai na Kara siya mana wani"

Mai bukata👎
(Aunty zeem mom mujaheed 08162859027)

SAI NAGA BAYAN KIWhere stories live. Discover now