page 4

61 11 1
                                    

*SAI NAGA BAYANKI*

              *NA SADNAF*

*ADABI WRITERS ASSOCIATION*

*PAGE 4*

            HAFSA

Kuka kawai take tana Jin kirjinta na suya har numfashin ta na neman d'aukewa,Alhaji Musa ya karasa da sauri Yana "Subhanallahi Hafsa jikin ne, Mujaheed zo ka kama ta mu Kai ta asibiti Mai ya sameta haka"?

Mujaheed da har lokacin yake wani irin kuka wajen Hafsan yayi yana nadamar fada mata maganar da ya sani Shiru yayi,bacin rai yasa ya manta ko Yaya sukayi maganar da ya danganci mahaifinsu ciwon ta tashi yake.

Hafsa da karfin addu'a taji ta fara jin sausauci ta dagawa mujaheed hannu akan ya kyalleta ba sai sunje asibiti ba,

Alhaji Musa da tsananin tausayin hafsa ke nukurkusar sa kamar ya Mata kuka yace "Sannu Hafsa muje na Kai ki asibitin mana"

Hafsa girgiza kanta tayi ta cije lebbenta tana "Ba sai mun je ba Alhaji Nagode"

Ta kalli Suhaib tana "abincin ku na kitchen ku je ku dauka kuje daki kuci, Mujaheed ku kawowa Abban ku ruwa ya Sha"

"Aaa hafsa a koshe nake ba sai ya kawo ruwa ba su dai je suci abincin"

Hafsa bata ce komai ba har yaran suka shige dakin ya rage daga ita sai Alhaji Musa a palon daya zauna akan kujera ita kuma har lokacin tana kasa a zaune.

Yaran na shigewa kukan da ta matse ta karfin tuwo ya kwace mata,kukan nan kawai zai Saka ta samu Sai'da a zuciyarta har mutane ashe sun fara zargin Alhaji ya juya musu baya ne  saboda su mujaheed ba yayansa bane.

Shiru palon ya d'auka ba abinda ke tashi sai sheshekar kukanta,Alhaji Musa kuwa bai yi k'ok'arin hanata ba dan wani zubin kuka na rage maka nauyin kirji da Yana da halin da zai cire hafsa a cikin  damuwar nan daya cireta akan maganar sukayi baram baram Da Alhaji Wada,daya zama amini a gare shi tun suna Yara,shakuwa da abota yasa suka Auri kawaye Alhaji wada ya auri Hafsa shi kuma Ya  Auri Khadija Hafsa kuma kanwar Amininsu ne margayi shehu daya rasu shekara biyu da suka wuce,gashi shi kadai ne ya rage Mata dan iyayensu sun rasu,yau ko ba Aure a irin zumuncin da sukayi da abota Hafsa kanwa ce a gare su ko shi ko Alhaji wada kamata yayi ace sun Riketa da kyau dan duk sun kawo wanan matsayin ne ta silar yayanta da ya dora su akan harkar kasuwanci Allah cikin ikonsa ya sa musu albarka Alhaji wada kuma ya zo ya kere su a kudi duk da suma ba laifi da nasu arzikin Amma wada yafisu nesa ba kusa ba.

Sai da Alhaji Musa ya sauke ajiyar zuciya ya kira sunan ta da "Da Hafsa"

Hafsa ta share hawayenta tana "Naam"

"Kiyi hakuri bazan gaji da baki hakuri ba Hafsa Duk halin da kike ciki Allah Yana sane dake idan kika yi hakuri watarana zai wuce in Sha Allah har yanzu baya zuwa ko"?

"Baya zuwa ni rabon da na Saka shi a idona har yaran na manta  sai yau da yaran suka dawo  suke ce min sun ganshi da matar sa da yayansa,na gaji Alhaji Ina ganin hakura da Auren nan shi zai fi min alheri,Ina ta zaman Auren da bashida banbanci da Babu,wai har mutane sun fara zargin Alhaji ya juya mana baya ne saboda Yana zargin su mujaheed ba yayansa bane,wanan maganar ta daga min hankali,Mai muka masa da zafi haka har kamar ummi ce zata yi tunanin dan su bakakke ne shi yasa babansu baya San su,yaran nan haka zasu zo su tasani a gaba da tambayoyi, makota suyi ta ce min suna ganinsa da matarsa da Yara suna yawo a mota amma ni da yarana idan zamu fita sai dai mu fita akafa ko mu samu abin hawa,duk wani hakkin mu dake rataye a wuyan Alhaji ba wanda yake saukewa ba wacce ya tsani gani sama dani da yarana,yau idan ba kai ba Ina ga kafin mu samu Abu sai mun hada da yin bara zamu samu naci abinci,haka zaa shigo gidanan yimin godiyar irin alherin da Alhaji ke yiwa mutane Amma mu kanmu bamu wuce mu nemi taimakon ba na gaji da wanan Auren Alhaji dan Allah ka shige min gaba wajen amso min takarda ta,Yau Banda matar Yaya ta gudu da duk dukiyarsa da ban wulakanta haka ba"

SAI NAGA BAYAN KIWhere stories live. Discover now