Yar ƙanwata

0 0 0
                                    


❤‍🩹Y'AR K'ANWATA❤‍🔥
          paid buk 300

Fa'iza abubakar unity bank
0020281885
        FREE PAGE 6
             
             *BY*
*MAMAN AFRAH*



*Mutane da yawa suna tambayata menene ma,anar Y'AR ZUMUNA har gajiya nake da amsa tambayar nan dan haka na maidashi Y'AR K'ANWATA yadda kowa zai fahimta nagode masoya*💔

     Kalil ne ya nufi d'akin zai je wurinsu yana d'auke da Mimi da ke ta faman kuka, kafin ya k'arasa d'akin gaba d'aya ya k'arasa zubawa Inda   ,bai gama zubawa ba gaba d'aya ya rushe, kuka ya ke sosai, kafin ya juya ana ta zuga ruwan gashi tsakar gidan ruwane tandam haka ya bi yana tafiya har ya k'arasa cikin zauren gidan, yana shiga ya ajiye Mimi daga hannunsa ,dan gaba d'aya daga shi har ita sun jik'e jagaf da ruwa, Mimi sai karkarwar sanyi ta ke, rungumeta ya yi suke kuka a tare dan da ya bud'e k'ofar gidan ma zai fita tsabagen duhun da ya gani shi ya sa ya dawo. Haka suka ci gaba da zama cikin duhu dan fitilar a hannun ABBA ta ke gashi kuma k'asa ta zubo musu, takurewa sukayi a wuri guda sai kuka suke Mimi sai kiran Mama ta ke Kalil na jijjigata yana bubbuga bayanta dan ya kasa magana ,jim kad'an ya mike da sauri ya ce Mimi ta zauna a soro yana zuwa dan so yake ya kirawo makocinsu, Mimi k'in zama ta yi haka ya goyata a bayansa suka bud'e k'ofar suka fito ruwan na dukansu dan gaba d'aya Mimi Zazzabi ya rufeta, yana zuwa kofar gidan makocin nasu ya dinga bugawa da mugun k'arfi amma shiru ba,a bud'e ba, sabo da k'aran ruwa ba zai bari su ji bugun ba.

   Ya kusa awa guda yana bugawa amma ba,a bud'e ba,ganin Mimi na shid'ewa  ya hak'ura da bugun dan lokacin an k'afe ruwan ,haka ya koma cikin zauren na su ya zauna yana kuka a haka har aka fara kiran assalatu sannan shima Zazzabin ya rufeshi,haka dai ya lallaba  ya kwantar da Mimi a k'asa dan tuni barcin wahala ya yi  gaba da ita, cikin gidan ya koma amma baya iya hango komai sai tudun k'asar zubewar d'akin, dawowa ya yi ya koma gidan makocin nasu ya dinga bugawa da mugun k'arfi, Malam Isyaku da ke alwala ya ji k'aran buga kofa da farko ya yi zaton a wai gidan ne amma da ya saurara sosai sai ya ji a gidanshi ne. Saurin kammala alwalar ya yi ya nufo kofar gidan dan jin wanda ke buga musu kofa,yana zuwa ya ce

"Waye " Malam Isyaku  ya ce yana fargabar jin amsar dan ya san dai koma wanane ba lafiya ba, dan idan lafiya babu yadda za ayi a buga musu kofa yanzu.

"Baba Kalil ne dan Allah ka zo dakin mu ya ruguje kuma su ABBA suna ciki "Ya k'arasa fad'a yana kuka.

Da sauri  Malam Isyaku ya bud'e k'ofar tun kafin ma ya gama jin k'arshen maganar. Yana bud'ewa ya hau tambayarshi yana masa bayani yana kuka a hanzarce  Malam Isyaku ya  tafi masallacin layin ya kirawo mitane da suke  masallacin, dan har lokacin ba,a shiga sallah na.

  Da sauri mutanen suka biyo bayanshi aka zo aka ga barnar da ruwan ya yi, haka aka firfoto da ABBA da Mama FIRDAUSI duk k'asa ta farfasa musu jiki, sannan gaba d'aya rai ya yi halinsa, haka aka fito da su mutane kowa na fad'in albarkacin
bakinsa,wasu na cewa

"Daman ginin tsohone,kuma bai samun gyara "

   Wasu kuma na cewa

"Tsautsayine, daman can Allah ya sa k'asa itace ajalinsu, gashi sun yi mutuwar shahada "

    A haka aka yi musu suttura dan gaba d'aya komai a gidan Malam Isyaku akayi, haka aka d'auki makara biyu mai d'auke da mata da miji, aka kai su makwancinsu Allahu akbar ashe kwanaki d'aya suka d'akko. Kalil kam ya sha kuka kamar me haka Mimi ma dan Kalil magana ma gagararsa ta ke sai bashi baki ake amma daga ya ga Mimi na kuka shima bai iya yin shiru😓 anan gidan Malam Isyaku ake zaman makoki, dan gidan ruwane ga kuma laka shi yasa Malam Isyaku ya ce ayi a gidansa. An rasa yadda za ayi a fad'awa ABBA SAMINU mutuwar amininsa da matarsa dan an rasa da number da za, a sameshi dan ma Kalil ya fad'a musu cewa tunda ABBA SAMINU ya tafi ba su yi waya da ABBAn nasa ba.

     *BAYAN KWANA BAKWAI*

 
  Kalil da Mimi anan gidan Malam Isyaku su ke zaune, har akayi sadakar bakwai, bayan an yi bakwai ne Malam Isyaku ya shawarci matarsa surayya akan yana so su rik'e yaran a hannunsu tunda ba su da kowa, amma surayya  haka ta kekashe k'asa ta nuna it's fa yaran ba za su zauna mata a gida ba, haka kawai yaran da bata da wata alak'a da su za ace ta rik'esu hakan ma ba zai tab'a yiwuwa ba.Shi kuma Malam Isyaku ya ce tunda ya yi niyya babu mai hanashi taimakon yaran domin idan sun tafi ina za su je?  haka dai su ka zauna a gidan amma ba dan surayya tana so ba.

   Malam Isyaku bai fiya zaman gidan ba kullum yana,tafiya kasuwa dan haka idan ya saka kafa ya fita babu wani abu da su Kalil ke fuskanta sai azabtarwa dan ta d'au alwashin  ba za su tab'a jin dadin zaman ba.Kai ya kai ko abincin kirki bata basu sai dai wani lokacin Kalil ya fita ya yi aikin k'arfi ya siyo musu su ci ko idan abincin kad'an ne sai ya hak'ura ya barwa Mimi

   Yanzu aka fara ku dai ku biyomu domin jin yadda za ta kasance 💞💞💞

YAR ƘANWATAWhere stories live. Discover now