Yar ƙanwata

3 0 0
                                    


❤‍🩹Y'AR K'ANWATA❤‍🔥

Paid buk 300
NA MAMAN AFRAH
Fa'iza abubakar unity bank
0020281885

*Mutane da yawa suna tambayata menene ma,anar Y'AR ZUMUNA har gajiya nake da amsa tambayar nan dan haka na maidashi Y'AR K'ANWATA yadda kowa zai fahimta nagode masoya*💔

PREE PAGE 3

Sun zauna tsawon shekara uku a garin Jahun kafin daga bisani suka koma GUJUNGU da zama, bayan sun biya sadaki an daura musu aure SALIM da FIRDAUSI, SAMINU da ZAINABU, a inda suke zaune a unguwa d'aya sai dai kuma wannan karan ba gida d'aya suke da zama sabo da ba su samu gidan haya wanda zai ishesu ba. Haka suka taso da rik'e zumunci ,mutane ne da ba ruwansu sun iya rik'e mutuncin su da kuma talaucinsu Sam basu damu da abin hannun mutane ba wai dan su basu dashi ba.Sun d'au shekaru da dama da aure sannan ZAINABU ta samu ciki Sai da lokacin haihuwarta ya yi sai jini ya dinga zuba har dai ta haihu y'ar babu rai kafin itama a lokacin Allah ya karb'i ranta. SAMINU ya ji mutuwar matarsa, sannan uwa uba FIRDAUSI da SALIM da su ma mutuwar ta tab'a su sosai.

Dawowa labari, sakanni su ke dunkulewa su zama Mintina, mintina ke harhadewa su zama awanni, su kuma had'e wuri guda su zama satika, satika su zama watanni, watanni su kuma sai su zama SHEKARA.A halin yanzu Mimi na da shekaru uku cif ta gama wayonta tsaf babu wanda ta sani daga iyayenta sai kwa Yayanta ,yanzu an sakata a makaranta sai ya rakata makarantar su sannan ya wuce tashi makarantar.

A wannan lokacin ne kuma SAMINU ya nemi amincewar amininsa SALIM akan yana so ya tafi Kaduna neman kud'i saboda ya gaji da zaman haka yana so ya yi nesa da gida ko ya samu damuwar da yake da ita, ta mutuwar matarsa ta barshi dan anan babu abin da ya ke kullum sai tunani.Da farko SALIM bai amince ba sabo da bayaso SAMINU ya tafi shi kad'ai ya fi so su tafi tare amma sai SAMINU ya ce ba za ayi haka ba dan ba zai so shi mai iyali ya barsu ya yi nisa da su ba,dan haka shi ya zauna shi SAMINU ya tafi idan ya ga wuri da samu in ya so idan ya dawo sai su koma tare. Haka SALIM d'in ya yarda da maganar SAMINU, sabo da shima yana so SAMINU ya samu sukuni daga wanna tunanin matar tasa tunda har an samu zai yi tafiyar gwara ya barshi ya tafi in yaso idan ya dawo sai su tafin kamar yadda ya buk'ata.

Ranar da ta kasance laraba a ranar ne SAMINU zai tafi Kaduna, za su tafi ne tare da wani mutum da ke bayan layin da suke, ana kiranshi Usaini, wanda shi Usainin shi ne zai nuna masa kasuwancin dan dama shi ne ya bashi shawarar ya tafi neman kud'i watakila idan ya yi nesa da gida damuwarsa za ta ragu ko da bata fita duka ba. Haka SALIM da SAMINU suka ringa ssllama tsakaninsu, sallama ta ki k'arewa sun kasa rabuwa idanunsu duk sun yi ja jawur saboda damuwa kowa bai son rabuwa da d'an uwansa. Anan SALIM ya tsaya a tasha har sai da motar su SAMINU ta tashi suna d'agawa juna hannu har sai da motar ta b'acewa SALIM ya daina hangota kwata -kwata sannan ya juya ya koma gida ranshi dad'i, sabo da ji yake kamar ya rabu da wani Sashe na jinin jikinsa, soyayya, amintaka shak'uwa sun gama shiga tsakanin SALIM da SAMINU. Shima SAMINU a nashi b'angaren hakane dan tun da suka fara tafiya a motar bai buda baki ba da niyyar magana gaba d'aya jin ransa yake ba dad'i banda dole babu wani abun da zai rabashi da SALIM, a haka dai har Allah ya saukesu lafiya a Kaduna garin gwabna.Tunda suka sauka ya ke ta neman wayarsa dan ya kira SALIM amma kuma bai ganta ba, neman duniyar nan amma ko alamarta babu gaba d'aya jakar kayansa ya bincike amma kuma ko mai kama da wayar babu daga baya ya sadakar da cewa wayar fad'uwa ta yi...

Paid buk akan naira dari uku local d'aya daga cikin taurari shida, ki biya ki mallaki naki ki karanta cikin aminci da kwanciyar hankali 💞

YAR ƘANWATAWhere stories live. Discover now