Yar ƙanwata

3 0 0
                                    

❤‍🩹Y'AR K'ANWATA❤‍🔥
      paid buk 300
Fa'iza abubakar unity bank
0020281885
       PREE FAGE 4

                *BY*    
            
   *MAMAN AFRAH*

    A b'angaren SALIM ma haka ya yi ta kiran number  SAMINU tun bayan komawarsa gida, amma kwata kwata ta ki shiga hakan ya sa ya yi tunanin ko sabo da suna hanya shi yasa tak'i shiga, amma abin mamaki har dare bai samu wayar SAMINU ba, daga K'arshe ma sai ake cewa a kashe. Tunaninsa babu caji ne dan haka ya hak'ura da kiran dan ya san matuk'ar SAMINU ya yi cajin to tabbas zai kirashi.A haka dai har washe gari kiran SAMINU  bai shigo wayar SALIM ba, sannan kuma shi SALIM d'in idan ya kira wayar SAMINU bata shiga y'a shiga damuwa sosai, kafin daga bisani Mama FIRDAUSI ta ce masa ya yi hak'uri watakila wayar ta fad'i ne, haka dai ya hak'ura ba dan ya so ba, dan ya san SAMINU bai haddace number wayarsa ba bare idan ya samu wata wayar ya kirashi, ballema ina ya ga kud'in da zai siyi wata wayar dan banda  kud'in motar, sai ko y'an kud'ad'en da basufi ya ke cin abinci ba.A haka ya dangana da jiran kiran SAMINU.

    SAMINU ya tambayi Usaini akan ya kira wani a waya a had'ashi da SALIM su yi waya, amma Usaini yace ko layi ma bashi da shi bare ma waya , dan tun da aka sace masa waya har yau bai sake siyan wata wayar ba dan yana da  buk'atun da suka fi siyan wayar muhimmanci.Hakuri da juriya sai kuma addu, a su SAMINU ya rik'e ya maida hankalinsa kan abin da ya je nema tunda ya san dai lafiya lau ya bar su.

     *Bayan sati biyu*

  Hadari ne a garin domin lokaci ne na damina gaba d'aya sama ta yi bak'in  kirin, sai walkiya ake zabgawa ga kuma k'aran cida da ke tashi ruguguguu, kowa da kowa na saurin tafiya gida ko in ce mazauninsa dan gudun kar ruwan ya ritsa da shi, domin lokacin dab ake da kiran sallar ishe, i ga wani duhu da ya baibaye garin kamar tsakar dare sabo da  haduwar haddirin walkiyar ce kawai ke haska duhun. ABBA SALIM ne  ya taho daga kasuwa da yake yau lahdi kasuwar garin na GUJUNGU  ke ci, babbar kasuwa ce, dan haka har lokacin mutane basu gama bajewa ba, haduwar hadarin ne ma ya sa kowa ke neman inda zai tafi. ABBA SALIM rik'e yake da  ledar gurasa da kuma rogo da ya siyo wa iyalansa a matsayin kayan kasuwa wato tsaraba.Sauri yake dan  da kafa ya taho bai hau abin hawa ba, dan gani yake da ya hau abin hawan gwara ya had'a kud'in ya yi cefane sabo da  halin babu da suke ciki,yana zuwa dede zai shiga gidan ya jiyo muryar mai gidan da suke haya yana ta masifa akan a tabbatar zuwa jibi an had'a masa kudinsa in ba haka ba duk abin da ya musu su suka jawa kansu Mama FIRDAUSI sai hak'uri take bashi, dakatawa ya yi da shiga gidan dan gudun kar ya masa masifa shi kuma ranshi b'aci yake akan cin mutuncin da yake musu, baya d'aga musu kafa ko kad'an, bayan ya san basu dashi. Bayan maina ya samu ya dan lab'e, har mai gidan nan ya zo ya wuce ba tare da ya ganshi ba.

   Gidan ya shiga ya gan su, tsaye curko curko su duka ukun, ranshi ne ya ji babu dad'i kwata-kwata baya son ake tadawa iyalansa hankali, dan dai babu yadda zai yi na.

mmn afarah 09030283375

YAR ƘANWATAWhere stories live. Discover now