“Ya gajiyar Asibiti?. Ya mai jiki?”. ta tambayi Mommy tana fito da warmers ɗin da ta san ake zuba abincin dare acikinsu.
“Da Sauƙi Jummala. Sannunki da aiki ƴar Albarka”.  Ta faɗi tana buɗe tukunyar. Macaroni da wake tayi wanda ya ji bushasshen kifi da kayan ciki sai tashin ƙamshi yake yi. Iya girkinta na ɗaya daga cikin ababen da ya Sanya Soyayyar Jummala acikin zuciyarta, duk kuwa da cewa ita ta koya ma ta. Amma kuma bata wani sha wahala wajen koya ma tan ba kasancewar yadda yarinyar take da kaifin basira da saurin ɗaukan abu.

Duk da cewa Girki ba shi bane muhimmin abinda ya sa ta ke aiki a gidan, amma kasancewar ta iya yanzu kusan duk abincin daren gidan ita take yi yanzu. Iya girkinta a ƙananun shekaru yana ɗaya daga cikin abubuwan da Jummala zata kalli Mummy tayi Alfahari da ita. A wasu lokuta ma ta kan janyo tunanin irin soyayyar da Mummyn ke nuna ma ta kaɗan ne za'a ƙara akan wadda Inna take ma ta, sai dai kawai ta san akwai tazarar da Soyayyar da Mummyn da ta Innarta bazasu haɗu ba, Tunda ita ce Mahaifiyarta wacce ta ɗauki cikin ta har wata tara tana kwance. Yanzu ta girma ta zama budurwa sosai abun har mamaki yakan ba Amina da yadda girmanta ya faru cikin ƴan shekaru da kuma yadda ta girman. Inna tana tsokanarta akan girmanta wasu lokuta take faɗa ma ta har ta shiga watan goma kafin aka haife ta. Sai dai duk yadda ta iya girki Ubaid baya taɓa cin girkinta. Abin yana ba Mummyn mamaki ta yadda da ya sanya abincin abaki yake gane wannan ba ɗanɗanon abincin Mummyn shi bane. Kuma duk yunwar da yake ji haka yake haƙura da shi idan ba ita ta dafa ɗin ba, shiyasa take ɗiba acikin wanda tayi na rana ta saka a Fridge idan dare yayi tayi mai warming ɗin shi, baya damuwa da koma menene yake sake cin abinshi.

Mummy ce ta raba abincin a haka yau ba hirar da suka yi kowa da abin da yake saƙawa a ransa.

*******

Cikin tsananin razana, firgici, tsoro da wani irin dokawar zuciya Waleedah ke kallon system ɗin da ke gabanta, ta kasa gasgata abinda idanunta suke gane ma ta a halin yanzu. Mr. Jamaluddeen ɗinta ne ya saɓule fuskarsa izuwa wata fuska ta daban. Mr. Jamaluddeen ne da fuska biyu. Mr. Jalaluddeen ɗin da ya lalata ma ta rayuwa. Mr. Jalaluddeen ɗin da ya zame ma ta komai na ta a lokacin da bata da kowa. Mr. Jalaluddeen ɗin da ta ke da mummunan zargi akanshi. Mr. Jalaluddeen da a yanzu take bincike akanshi a matsayin Babban Mai laifin da ake zargi da ba'a da wani evidence da za'a iya kamashi da shi!!!...

Ta daɗe tana tare da Mr. Jamaluddeen tun tana 200 Level a Amoud University da ke nan Somalia. Maraicinta shine abinda ya tsayar da karatunta na wani lokaci domin dama duk hoɓɓasawar Mahaifinta AbdulMu'umin shi yake yi. Gashi lokacin da Allah yayi masa rasuwa da shi da Mahaifiyarta wacce Soyayyarta ya zame ma ta gaba a komai na rayuwarta. Ganin rashin madafar gashi ɗan abinda suke da shi da ya siyo ya ajiye na kayan abinci kafin ya rasu sai ƙarewa yake ya sa ta ɗauri aniyar fara neman aiki. Ƙaddarar haɗuwarta da Mr. Jamaluddeen shine ya sa cikin Sa'a ta samu aiki a AL-MUBARAK Hotel cikin tarin ayyukan da ta yi applying. Ƙarancin masu aiki da suke da shi a ɗan wannan lokaci ya sa aka sata room service na kaiwa waɗanda suka sauka a Hotel ɗin abinci idan sunyi Order. Da ganinta ya bayyana ma ta yadda yake ji game da ita. Tun farko ta ƙi amincewa amma saboda ita yasa ya dinga yin odar abincin da ba ci zai yi ba kawai sai don saboda ya ganta, ita kuma kafewa da tsoron saɓawa Allah ya hanata bashi haɗin kai. A ƙarshe dai haɗa kai suka yi da Chief chef na hotel ɗin aka saka ma ta ƙwayar gusar da hankali acikin ruwan shanta wanda ake bawa Ma'aikata a yayin da zataje hutawarta da daddare . Farkawa tayi kawai ta ganta akan gado, sai daga baya abubuwan suka fara dawo ma ta ɗai ɗai da ɗai ɗai ta ɓarke da kuka mai tsuma rai. Da ƙyar da lallashi ya dinga ma ta kuma ya dinga yi ma ta Alƙawurran da bata san iyakansu ba. Sai daga bisani tayi shiru tuna cewa bata da wanda zai taimaketa ko ya kula da ita sai ita da kanta. Bazata manta yanda ya ɗauketa har cikin Jakuzzi inda ya haɗa ma ta ruwan zafi yana dropping ɗinta ba. Ba zata manta irin azabar da taji da kuma yadda hawaye yake kwarara a idanunta tana yi tana tsaftace jikinta ba.

Bạn đã đọc hết các phần đã được đăng tải.

⏰ Cập nhật Lần cuối: May 01, 2023 ⏰

Thêm truyện này vào Thư viện của bạn để nhận thông báo chương mới!

IMRANNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ