YAR ƘANWATA

24 0 0
                                    

Y'AR K'ANWATA

FIRST CLASS WRITER'S

🪦 *Y'AR K'ANWATA* 🪦

                NA

MAMAN AFRAH

FREE PAGE 1

* *TAURARI SHIDA!*

     *_ZANGON FARKO_*


RAHMA SABO USMAN
*GUGAN KARFE*

UMMY KHALIL
*DALILIN BESTY*

UMMU AFFAN
*AMINI NAH*

FATIMA AMINU (Ummu Sadiq) 
*GWARAMA* **

MAMAN AFRAH
*Y'AR ZUMUNA*

MUMMYN MIHAL
*MIJIN MAKOCIYATA*

*FARASHIN MAI SAYEN GUDA:*
*MAI SAYEN ƊAYA 300*
*MAI SAYEN BIYU:400*
*MAI SAYEN UKU:500*
*MAI SAYEN HUD'U:700*
*MAI SAYEN BIYAR:800*
*MAI SAYEN DUKA :1000*

_*Ku nuna soyayyar ku ga gwanayen ku* ta *hanyar sayan litattansu , ne tahaka ne zaisa mugane kunayin mu* 🥰

*SAI KUN K'ARASO*
_Daukar nauyi, *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION*_

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
ACCOUNT NUMBER HADIZA ABDULLAH
ZENETH BANK
2217944522
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Idan kun tura sai kuturo shaidar biyan ku tawannan lambar
0814 671 1395

Idan kuma katin wayane
Sai ki tura ta wanann numbar , 0814 974 1554


Ga mai neman ƙarin bayani sai ya tuntubi wannan lambar.
👇🏻👇🏻👇🏻
+234 808 800 2574
+234 903 028 3375

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

      JIHAR JIGAWA  

KAUYEN GUJUNGU

   Wasu magidanta ne guda biyu da ke zaune akan benci karkashin wata bishiyar maina sa, annin juna ne, dan dukkansu ba za su wuce shekaru talatin da biyu ba.

SALIM ne ya ce

"Gaskiya SAMINU ya kamata ace zuwa yanzu ka yi aure, tunda marigayiya ZAINABU ta rasu har yau ka kasa kallon wata mace da sunan SO, kullum idan ba ma tare to kana kebance a wani wuri kana ta faman tunani, wanda tunanin ba abinda zai haifar maka sai wata damuwa akan wacce ka ke ciki" y'a karashe  fad'in haka yana kallon aminin nashi.

"Tabbas SALIM maganarka haka ta ke, amma sai dai inaso ka sani mutum bashi da ikon hana zuciyarsa tunani, domin kuwa shi tunanin zuwa ya ke, aduk lokacin da ya ga dama ba tare da ka so ba ko kuma ka gayyashi ba. Nima ba da son raina ba nake yi sai ina addu, a  Ubangiji ya yaye min wannan damuwa da na ke ciki, maganar aure kuma gaskiya bana jin a kwana kusa zan iya rayuwar aure da wata mace dan ko na aureta ma  nasan tabbas zan shiga hak'k'inta ne domin kuwa wannan halin da  nake ciki zai sanya rauni wajen bata kular da ta da ce dan har yau ban fita daga jin zafin da rad'ad'in mutuwar matata ZAINABU ba" SAMINU  yace yana sa hannu ya share hawayen da suka zubo a idanunsa.

"Ka yi hak'uri SAMINU tabbas mutuwar mata akwai ciwo musamman mace mace ta gari tabbas na san ka yi rashin masoyi ya mai hak'uri da dattako, mace Mai sanin ya kamata, amma ya dace ka daure ka ke cire  damuwar ko yayane dan ZAINABU ta yi mutuwar shahada sabo da ta mutu ne akan gwiwa duk macen da ta mutu garin haihuwa to tabbas ta yi shahada gashi uwa uba rashin mutu mijinta na kuka da damuwar rashinta, duk macen da ta mutu mijinta na yarde da ita to tabbas y'ar  aljannace  in ji mama, aiki (S. A. W) " Cewar SALIM yana goge k'wallar tausayin amininsa  SAMINU.Yana kuma tunanin tashi matar da itama take d'auke da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe.

"Nima sanin hakan da na yi, wato mutuwar shahadar da ta yi shi ne ke sa ni jin sassauci a zuciyata, tabbas ZAINABU macece ta gari samun kamarta zai yi wuya ko in ce sai an tona dan dai babu abin da ya gagari Ubangiji "SAMINU yace yana jinjina kai.

"Wannan hakane kam Allah sa mu cika da imani "Cewar SALIM.

"Amin ya Allah "SAMINU  yace yana runtse idanunsa jin zafi da rad'ad'in mutuwar matarsa  ZAINABU na ratsa b'argo da  zuciyarsa.

"Assalamu Alaikum, Abban ina wuninku" IBRAHIM wanda ake kira da KALIL ya ce yana d'an risinawa, yaro ne fari tass wanda a kalla zai yi shekara goma sha uku  sanye yake da kayan makarantar islamiya ruwan toka.

"Lafiya k'alaw KALIL an taso daga makarantar "SALIM  da SAMINU suka had'a baki wurin amsa gaisuwar tasa.

"Eh mun taso" KALIL d'in yace cikin girmamawa.

"To maza aje a cire kayan makarantar ko" SAMINU yace yana murmushi.

"To  Abba "cewar KALIL dan duk da  ABBA yake kiransu duk da cewa ABBA SALIM shi ne ABBA nashi.

  Cikin gidan ya nufa cikin natsuwa yana rik'e da jakar leda mai d'auke da littafansa na islamiya, daman su ABBA  a k'ofar gidan ABBA SALIM suke zaune akan bencin. da sallama ya shiga gidan, Mama FIRDAUSI da ke nauke kayan da ta kwashe tuwo, daga  gindin murhu za ta kai cikin kicin d'in  su na langa-langa ta amsa sallamar dak'er sabo da nauyi da cikinta ya mata, da sauri KALIL ya ajiye  jakar leda akan tabarma ya nufi Mama FIRDAUSI da  sauri ya karb'i kanukan hannunta, ya shigar da su kicin d'in. Binsa Mama FIRDAUSI ta yi da kallo tana jin son d'an nata yana shiga cikin ranta yaro mai sanin ya kamata ga hankali tabbas Allah ya bata da mai nagarta wanda kowacce uwa za ta yi alfahri idan ta same shi.

"Sannu Mama" KALIL ya ce ganin Mama FIRDAUSI ta zauna dak'er.

"Yauwa KALILINA"ta ce cikin fara, a da k'arfin hali dan jin yadda mararta ke ciwo.

"Mama me kuma za, a yi in miki"ya ce cikin tausayinta ganin tana cije leb'e.

"babu komai kawai ka cire kayan makarantar sai ka d'auki ruwa a buta ka kaiwa su ABBAnka ka ga magriba ta kusa, sannan ga hadari a garin nima miyar nan dana kad'a nake jira ta tafaso na sauke na kashe wutar sabo da  kar hadari ya taso"

"To Mama "y'a ce cikin girmamawa ya shiga d'akin nasu na k'asa wanda ya ke d'aki d'aya  ne, kayan ya cire ya linke sannan ya canja wasu ya fito ya d'auki butocin ya kaiwa su ABBA a k'ofar gida.

   Bayan an fito daga masallacin ne ya shigo gidan domin d'aukan tuwon su ABBA ya kai musu dan lokacin bayan magriba ne duhu har ya shiga,ya tarad da Mama FIRDAUSI tana lazimi bayan ta gama ta bashi tuwon nasu ya tafi ya kai musu ya dawo ya d'auki ruwa ya kai musu, bayan ya dawo daga kai musu ruwan sai ya tarad da tuwo a plate an zuba miya aka, da alama dai nashi ne, abin da ba, a tab'a yi ba dan tun da ya bud'i ido ya yi wayo bai tab'a cin abinci ba shi kad'ai sai dai shi da Mamansa FIRDAUSI, daman da ya shigo tana cikin d'aki ta amsa sallamar ,da sauri ya tashi ya tafi d'akin domin ya tambayoyin Mama FIRDAUSI  yana shiga d'akin da sallama  sai bai ji ta amsa ba hangota ya yi daga can k'arshen gado tana durkushe akan gwiwoyinta ta kama gadon ta rirrik'e, da gudu ya nufeta yana kiran sunanta amma ya ga sai jinke baki ta ke tana girgiza kai dafata ya yi hana kiranta da tambayarta menene  ya sameta, ta kasa magana sai hannu ta ke nuna masa, cikin k'arfin hali da kuma dauriya ta furta "Ab..ban.. ka tuni ya fahimci ABBA ta ke so ya kirawo a guje ya fita har haki yake. ABBA da suke cikin cin tuwonsu miya ta yi zau zau basu ankara ba sai ganin Kalil sukayi ya taho wurinsu da gudu wannan yanayin d''a suka ganshi shine ya tabbatar musu akwai matsala, dan Kalil yarone nutsatstse ba za ka taba ganinshi yana guje gujen hauka ba, ai kafin ya k'araso ma sun mike tsaye su duka biyun

"ABBA Mama tana kiranka kuma bata da lafiya dak'er ma take magana...Ai kafin ya k'arasa fad'a ABBA SALIM ya  nufi gidan a kidime, Kalil ma da ABBA SAMINU baya suka mara masa, sai dai su a tsakar gida suka dakata, ABBA SALIM na shiga ya ga  Mama FIRDAUSI kwance cikin jini....

YAR ƘANWATAWhere stories live. Discover now