part 4

6 0 0
                                    

Bismillahir rahmanirrahim

Please follow up on wattpad @ayeeshatou

ABUJA 

Tunda ya barta anan wajen take tsaye babu inda ta sani a garin in banda anguwan da suka sauka shima yanxu in za'a kasheta batata iya fadin ga sunan unguwar ba.

           Wayarta  dake cikin yar qaramar pose dinta dake manage a hammata ta ciro, kunnashi tayi ko Allah zesa ya tsaya, kallon wayar takeyi yana starting a zuciyarta ko adduar ta daya Allah yasa ya tsaya  koda 2 percent ne tasman ze iya kira mata koda mutum daya ne Wanda tasan zai iya zuwa daukanta at this time,
Want irin bugawa qirjinta yayi tunanin gidan da tayi, yanzu ta ina zata fara bayanin ga abinda ya faru da ita? Me zatace ta fitayi da mota alhanin ita ba sanin ko ina tayiba, hatta zuwa dinner  ma yaya tazo shine har zata fita?.

              Ta tuna irin draman da sukayi dazu da yah aliyu akan zuwanta abujan,

Shigowa yayi gidan ranshi a bace yana fadin "ina Naidan take"  duk dangine a tsakar gidan wadanda bash tafi waliman da akeyi a gidan kawu uba ba, sai yan mata irin su Naida dake qannin amarya anata shirin dinner da za'ayi anjima.

     Tunda taji muryarshi ta fara zaro idanu dama tasan ko kowa yaji maganar tahowarta baiyi maganaba shi saiya tanka, jin muryan inna binta tayi daga tsakar gida tana fadin 

"Ba'asaninba tunda baka iya sallama ba kawai zaka fadoma mutane gida babu sallama"    juyawa yayi ya kalli sashin da take tana zaune saman farar kujerar robar da tana aka dauko mata daga wajen walima, 

share maganar da taimai yayi yana fadin "Amman fisabilillahi inna yarinyar nan fa exam ne da ita jibi Amman shine aka biye mata saida aka taho da ita bikinnan to wayene zai mata karatun jarabawar?"

"To kai in banda abinka ai ba bikine kadai ba, yanzu ko want wannan taron ma da aka akayi ai zaazo tana dangi itama tayi ziyara ko?

" eh Amman ai akwai bayan biki, in ta gama jarabawar ba sai tazo tayi ziyarar ba , jibine fah exam din yaushe har zatai karatun, to Allah yasa ta qara fadi wanna  karan ma zataga yanda zan babballata" 

     Harararshi inna binta tayi dama ba wani shirin arriving sukeyiba "to alhudahuda uban karatu inta fadi ka kasheta kawai, hakanan baza'abar mutum ya hutaba kullum karatu karatu itama batata sakata ta walaba, inadai jibine kace jarabawar ko? To kasha kuruminka insha Allahu gobe tare zamu koma da ita"

       Kwafa yayi ya juya ya fita yana fadin  "zamu hadu da ita ai"   ita dai tana daga daki tana jinsu tasan tunda taji yace zasu hadun nan to wasan buya zasuyi tayi harse ya manta.

Qarar vibration din wayarce ya dawo mata da tunaninta, har ta gama kunnuwa sannan koma ta mutu alamun shutdown, wani irin zufane ya karyo mata tasan yanzu sha daya ta kusanyi Idan ma bata wuceba,

Wani irin tsorone ke cinta  qafafunta har wani rawa sukeyi bayan zuciyarta dake lugude kaman zai fado qasa,

    Waigawa ta farayi tana qarema irin unguwan da take kallo, irin arean masu kudinnanne babu yawaitan mutane duk da titine Amman babu ko irin shagunan nan ko wasu tarkace wajen fahau sai hasken solar daya haske ko ina, 

        Gajiya da tafiyan tayi ta tsaya bakin titin kallon yanda daidaikun motoci suke zuwa su wuceta fuuu...

Ganin irin kallon da wasu masu motocin suke mata a ganinsu sun dauka irin karuwan nanne masu tsayawa a bakin titi da daddare,

  kallon jikinta tayi ko shigarta tayi kama Dana prostitute ne maybe shiyasa basa tsayawa su taimaketa duk da ita kantar bawai tayi tsayuwan kaman me neman taimako bane tana tsayene irin na Wanda ya rasa abinyi a rude take .
Kukan ta fashe dashi mai cin rai yanzu kome ya sametama ita ta ja ma kanta, souring toshe bakinta tayi da duka hannuwanta Kukan na tsayawa a lokaci daya, yanda aka dallaro wajen da take da hasken da batasan ko na menene ba,

Dayake wajen da take tsugune akwai flowers a wajen kuma akwai rufi so babu haske sosai a wajen,Tuni ta nemj kukan ta rasa tsabar kidimewa jikinta jikinta babu inda baya rawa,

         

    tunowa da irin yanda ake kidnapping a wannan zamanin yasata jin tsoronta ya qaru,

         Dallarota akai da torchlight din daya kashe mata idanun yasa ta dena ganin komai na gabanta rashin ganin kuma ya tafi da duk wani motsi na jikinta

                                 * * * Har bayan sha dayan dare babu Naida ba labyrinth, duk inda hankalin mutanen gidan yaje ya tashi duk cikin manyan babu Wanda ya iya runtsawa suna tsaye cirko cirko kamar masu jiran suga ta ina zata bullo,

Kowa da tunaninshi ina zataje Ina za'a sameta a wannan dare,

Masu dawowa daga dinner tuntuni kafin Tara kowa na makwancinshi hatta amarya sun dawo Amman babu Naida a cikinsu, barinma aunty binta da tafi kowa tana hankalinta, 

     Su salima ne aka tasa a gaba sai sun fadi inda taje tunda su suke tare da ita amma suma kansu since basu gantaba Dan tun kafin ma a qare dinner babu ita duk a zaton suma ta wani wajenne shiyasa basu damuba.

Wayako an buga duk inda ake tunanin za'a iya samunta Amman kowa se yace be gantaba wayantako a switch off ake jinshi.

          Kamal ne ya shigo ranshi a bace idanunshi cike ba bacci yake fadin 

      "wllh duk inda sha biyu ta buga a gidan nan gado zani, bazan zauna in hana kaina bacci take wannan yar banzan yarinyar ba sai da nayi nayi kar a taho da ita amma bansan wanene ya daure mata gindin zuwa ba"

Babu Wanda ya iya tankashi kowa da tunanin dake ranshi, u umma ko tana zaune da cikin dakin aunty salamatu ( matar kawu sani) duk hidindimun da ake na neman Naida tanaji ko fitowa ma bata yiba bare ta ji ya ake ciki shiyasama babu Wanda ya sakata a ciki.

         Amman kuwa can qasan ranta cike yake da damuwan da fargaban kar wani abu ya sami diyarta, duk da a fuska take nuna halin ko in kula Amman in ka kalli idanunta dakyau ne xaka gane hakan.

        Kawu uba ne ya shigo da sallama waya riqe a hannunshi amsa sallaman mutanen dake tsakar gida sukayi,            Kallon su yayi " kuje ki kwanta dare yayi fah in sha allahu za'a ganta" maida kallonshi ga inna binta yayi

   " inna kije ki kwanta kinsan fah ba wani cikakken lafiyane dake bah"

Cire tagumin fuskarta tayi tana fadin " ina naga ta kwanciya ba'a ga yarinya ba? Wannan diya ba'a San wani hali takeba aiko na kwanta ma bajin dadin baccin zanyi ba"  

"Karki damu inna yanxu na gama waya da daga ofishin yan sanda na sanar musu da case din batar amma sunce sai tayi 24hrs ba'a gantaba tukuna sannan zasu fara nasu binciken"

Tafa hannu ta shigayi " ni binta yanzu ya batan ma amma ace baza a nemoshiba har sai ya kwana daya tukunna? Yo inma kashewa ne ai tuni an gama bandashe da itama, wadannan mutane da son zuciya suke"

           Kamal dake shaqe da ita yace "Babu wani son zuciya haka yanayin aikinsu yake in kuma zaki fita ki nemota da kankine ga hanya nan, waya sanima ko ke kika boyeta saboda kar ta koma idan ba hakaba tun dazu da kin bari an maida ita da duk haka bata faru ba amma kika hana"

      Wani harara kawu uba yamai tare da daquwa "ungo nan nace, fita anan" ya fadi yana nunamai qofa.

    Aikuwa fitan nashi shine maslaha Dan dabe fitaba idan inna binta ta tada fitina saita tashi kowa da ya samu yai bacci a gidan nan.

The journey isn't started yet just show some love by liking and I will inspire you with the book 🥰

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: 5 days ago ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BAKAN GIZO 🕷️Where stories live. Discover now