shafi na hudu

299 6 0
                                    

*HUGUMA*
*_A RUBUCE TAKE_*
       (K'addara ta)

Page 04
----------------------------------------------------
*MAAB LUXURY HOME*

*_idan kaji gangami akwai labari_*
*_SABUWAR DUNIYA CE_*
*ALFAHARIN UWAR GIDA*
*FARINCIKIN AMARYA*
*MAIDA TSOHON GIDA SABO*
*DUNIYAR QYALE QYALE*
*KAYA NA ALFAHARI DA TAQAMA*

*_Ba iya kyawun idanu suka tsaya ba,harma da ingancinsu da kuma qwarkonsu,ka dade kana mora kana kece tsara a tsakanin tsararraku da sauran mutane_*

*nasan zaku tambaya ina ne nan?*

*MAAB LUXURY HOME*

😊 *Kai daga jin sunan ma babu tambaya*

*_duniyar qawata muku gidajenku ku ganku kamar a wata nahiya ko wata duniyar_*

*Suna kawo kayan kitchen rankatakaf manya da qananu*

*Kayan gado dana parlor*

*Kai...suna kawo kowanne nau'in kayan ado na cikin gida*

*Karkiyi qasa a gwiwa kuma kada kiyi sake ma dafe,maza garzaya ki nemesu a*

_adress dinsu dake No 22 Ahmadu bello way,kano state_

*Ko kuma kuyi order din kayanku kuna daga gida ta shafinsu na instagram*

@maabluxuryhome

*Facebook*
@maabluxuryhome

*Ko ku nemesu ta lambar wayarsu kamar haka*
08034631010

*Kyau inganci da rahusa shine takenmu*😊😊🤝🤝🤝🤝
____________________________


*Widad*

       Alhaji salim musayyib mai fata shine cikakken sunan,mazaunin maiduguri da wanda aka haifa a can,ya taso ya girma ya kuma yi gwagwarmayar karatunsa dukka acan din,nau'in jinsin nan da mutane ke kira da suna SHUWA_ARAB,saboda asalin iyayensu da kuma kakanninsu dukka ba'a maiduguri aka haifesu ba,ba kuma anan sukayi rayuwarsu ba,rayuwar da sukayi a maidugurin duka duka 'yar taqaitacciya ce,sanadin kasuwanci,asalin tushensu sun fito ne daga qasar mali zuwa yemen,kuma har yanzu danginsa da tushensa suna can gaba daya ko nace mafi yawa daga cikinsu,iyali ga mahaifinsa musayyib suke ta yado a nan,da kuma nashi ahalin shima daya tara.

          Matan aurensa biyu dukka 'yan asalin qasarsa wadanda suka hada masa tarin zuri'a da kuma yara masu yawa,dansa na farko da matarsa ta fari wadda ta kasance balarabiyar qasar yemen shine mahmud,wanda yake mahaifi ne ga widad data kasance ruwa biyu,balarabiyar mali kuma bafulatanar usul daga katsina  ta gefen mahaifiya,wannan shi ya taru ya bata wani irin sassanyan kyau daya banbanta da kyawun dukka cousin dinta da kuma sauran 'yan uwanta,domin ita daya mahaifiyarta ta haifa ta barta a gidan,sai tarin 'yan uba da kuma cousins da take dasu.

           Yanayi na rayuwa da kuma kasuwanci ya maido alhaji salim qasar kano da zama,ya fara tara iyalinsa shima,bayan ya aurar da mahmud arziqinsa ya qara ninkuwa fiye dana da,wanann ya siya manya manyan filaye ya hadesu waje guda,ya kuma yanki wani sashe na gidan ya fara ginin matsugunnin da zai zauna da matansa da kuma yaransa,bayan ya kammala suna gab da tarewa matarsa ta biyu ta rasu,sai mahaifiyar mahmud ce kawai Allah ya qaddara mata zama a gidan.

          Mahmud ne kawai ke rayuwa a wajen gidan,girman gidan ya sanya duk yaronsa daya tashi yin aure,za'a fitar masa da tsarin ginin da zai dace da gidan a gina masa ya tare a ciki,wannan yasa sannu a hankali gidan ya zama babban family house dake dauke da sassa sassa guda biyar,kuma kowanne sashe cike yake da albarkar zuri'a wadata da kuma kwanciyar hankali.

         Widad ta kasance ta musamman a wajen ummu,saboda ummun ta bude idanu ta gani a matsayin uwa kuma mahaifiya a wajenta,don itace ta raineta tun tana tsumman goyonta har kawo yanzu da shekarunta suke goma sha daya da watanni a duniya.

A RUBUCE TAKE k'addarataWhere stories live. Discover now