DANDANO

1.7K 27 3
                                    

*Z A F A F A   B I Y A R 2023*

*_DANDANO DAGA LITTAFIN_*

*_A RUBUCE TAKE k'addarata_*📖📖📖✍🏽✍🏽

*S a f i y y a H U G U M A*

         A nutse ta bude k'ofar toilet din ta fito daure da babban towel fari sol,lallausar farar fatarta mai santsi da sheqi tana ta daukan idanu.

         Gaban dressing mirror din dake dakin ta isa,ta ja kujera ta zauna tana kallon fuskarta a ciki,gaba daya jin ranta da jikinta takeyi babu dadi,fuskarsa ke gilma mata cikin idanuwanta,sam jikinta bai bata ba,ta kasa nutsuwa gami da gamsuwa da wannan tafiyar da ya qirqirar mata bagtatan lokaci guda,tana tsaka da hidindimunta,tun daga yanayi fuskarsa da kuma yadda ya dinga tuqi daga bauchi zuwa katsina takejin kamar ba abbas dinta ba,tabbas akwai abinda ke faruwa,akwai wani muhimmin abu dake gudana,tayi tunani har babu iyaka,ta laluba dalilin tas tun daga randa ya sanya qafa ya fita daga gidan zuwa dawowarsa da kuma isowarsu katsina......tayi zagaye cikin tunani da abubuwan da suka wanzu kaf! Ta kasa gano abu guda daya farun.

            A iya saninta sun rabu suna masu kewa da kuma shauqin juna kamar ko yaushe,hakanan koda safiyar ranar sun jima ita dashi akan waya suna hira,wata irin hira irin wadda ke fallasa sirrin zuciyar masoyi zuwa ga dan uwansa,yana ta mata qorafin a takure yake acan din tare da mita tana lallabashi tana kuma masa dariya,har suka rabu kyawawan kalamai ne bisa fatar baki da zuciyar kowannensu,to amma me ya canza hakan?

"AKWAI WANI ABU" ta fada murya qasa qasa tana motsa tausasan lips din bakinta tare da zare idanunta daga kallon da take qarewa fuskartata,ta dauki lotion dinta mai taushi da qamshi ta fara shafawa fatarta cikin kasala taraddadi da kuma damuwa.

            Duk bayan wasu mintuna saita kalli wayarta dake gefe tana tsammanin kiransa,saboda ta sani haka suka sabarwa juna,duk inda zashi cikin nigeria..... matuqar tafiyar mota zaiyi itace abokiyar hirarsa har ya isa inda zashi,idan kuma hakan bata kasance ba.....zaiyita kiranta har ya isa din,amma wannan karon ko gilmawar miscall dinsa bata gani ba bare kiransa,a qididdigen da tayi a yanzun kuma, tabbas koda baije gida ba yana gab da isa

"Waishin meke faruwa?" Ta sake jefawa kanta tambayar wata irin damuwa tana tabata tun daga qasan zuciyarta.

          Cikin dauriya ta shirya kanta cikin doguwar rigar atamfa,ta fidda ainihin kyanta da surarta sosai,duk da yanayin da take ciki sai data tsaya gaban mudubi ta kalli kanta,lokutta da dama takan dubi kanta da kanta tana tuna WACECE ITA A SHEKARUN DA SUKA SHUDE,a yanzun sai taga kamar ba ita ba.....komai yana zuwa yana shudewa da wani irin sauyi mai ban mamaki.

          Lausasan slippers ta zurawa qafarta,sannan ta isa bakin qofa ta kama handle din ta bude tabi siririn corridor din da zai sadaka da ainihin falon gidan.

          Tun bata qarasa ba ta hangeta zaune cikin falon,halittace mai girman matsayi a wajenta,halitta dake sahun farko cikin halittu mafi soyuwa a wajenta,a duk lokaci irin wannan da zatayi balaguro ta taho takanas saboda kasancewa da ita.....duniyarta kan cika da farinciki,takanji a duniya yanayi irin wannan bashi da tsaara a wajenta.

          A jikinta taji tahowarta,saita dauke idanunta daga kan tv din da take kalla ta maida kanta,kusan lokaci daya suka sakarwa juna murmushi,ta kuma rigata magana

"Wannan nauyin wankan naki dai yana nan,affan ya fara kuka har sai da aka fitar dashi" cikin karaya da rauni da takeji cikin gangar jikinta da zuciyarta ta qaraso dab da ita ta zauna,tana shirin amsa mata.....kamar me kiran yana jiran dai dai lokacinne kira ya shigo wayarta,a hanzarce ta daga wayar tana duba me kiran, zuciyarta cike da fata da burin ganin wanda ranta ke darsa mata.

          Batasan sanda murmushi ya subuce mata ba hadi da fitar siririyar ajiyar zuciya ba

"Ina zuwa" tace da mommie,ba zata iya amsa wayarshi a gabanta ba,ita kadai tasan hottest words da suke gayama junansu,kuma muddin aka samu mishkila mommie taji daga ita har shi sun gama tafka abun kunya.

A RUBUCE TAKE k'addarataWhere stories live. Discover now