Hakan yayi daidai da tasowar wata matashiyar yarinya wacce kallo ɗaya nayi mata na furta Ma Sha Allah tabarakallah, Hakika duk da munin kayan da ta sanya amma sai da kyau mai sunan kyau ya bayyana a fuskar yarinyar, Baka ce ba wai baka wuluk ba, za'a iya sanya ta a matakin chocolate color kirar fulani gare ta, sai dai bamu san fulanin ina ne ba.

Saman kanta kaɗai idan ka kalla zaka gane yawan gashin dake kunshe cikin kallabi duk dama suman gaban kan ta ya kwanta lub lub yayi mata saje don kuwa shi ya kara fito da ainahin kyan nata. Ta kanannaɗe suman kanta sannan ta sanya wani yagulallen mayafi ta rufe kan, tana sanye cikin shiga irin ta mabarata. Kaya ne zaka gansu yagaggu kuma zumbula zumbula irin sun masu yawa ɗinnan, kafafuwan ta na sanye cikin wasu shamulallun silipas wanda suka tsufa suka shamule har kana iya hango hujewar su ta tsakiya idan ana tafiya, yayin da saman silipas ɗin ya tsinke yafi so a kirga ana ta ɗaure shi da leda.

Babu abin da ke damunta sai tsagwaran talaucin dake manne a jikin ta, abin mamaki anan shine yarinyar dai ba zata wuce shekara sha shidda zuwa sha bakwai ba amma ɗauke take da cikin haihuwa wanda ya kai wata biyar zuwa shidda....Sa'annan tana goye da wata karamar yarinya wacce dai ba zata wuce shekara uku ba a duniya.

Ta mika siririn hanun ta, aka sanya mata naira hamsin ita ma yayin da ta dunkule tana ni yar barin wajen sai taji wata ƴar uwar ta mabaraciya na cewa,"*HADIZA* ana kara miki kuɗin, ai da sauri ta juya ta kalli mai rabon kuɗin sai yake cewa "Anshi wannan na ƴar ki ne"

Ta sanya hannu ta sake karɓa ta buɗe baki tayi godiya sosai anan na sake yarda ita ce mai ɗauke da wannan zazzakar muryar, kuma kenan yarinyar da ta goya ma ƴar ta ce?

Ta ɗan share zufan fuskar ta da dattin tsummokaran kayan ta, Ta zauna tana huci tsabagen gajiya da goyon yarinyar, a haka ta taka tsallaken titi ta mikawa wata mai kosai tace "Ban na hamsin ladiyo"

Ladiyo ta buɗe robar ta samo leda fara ta sanya mata kosan hamsin tana cewa"kin ga na sa miki gyara"
"Hadiza tace"To godiya nike, kar ki sanya yaji" bayan ta kar ɓa sai ta koma in da take ta kunce goyon da tayi tana cewa,"Sannu Sofia, anshi kosai ki ci"

Sofia ta karɓa da sauri sakamakon yunwar da ta addabi cikin ta don rabon ta da abinci tun jiya da yamma, Sofia na ta cin kosai taga Hadiza ta yi tagumi tana kallon ta, sai ta ɗauko guda ɗaya ta sanya wa Hadiza a baki amma Hadiza sai taki karɓa tana share wasu kwalla da suka cika mata kwarmin idanuwan ta.

Ta ce,"Kanwata Sofia kin fi ni bukata ki ci bai da yawa"

A hankali yarinyar ta furta Yaya ke ma ki ci mana, me yasa ki kuka Yaya?

Hadiza ta zuba wa Sofia idanu ta na tuna irin wahalar rayuwar da suke ciki rayuwar bara, kuma basu san yaushe zasu dena wannan rayuwar ba tun da abincin da zasu ci ma gagararsu yake, tufafin kirki ma basu da shi, babu iyaye basu da kowa sai Allah basu da wajan kwana sai rakuɓe rakuɓe yau su kwana anan gobe su kwana acen, ta sake goge wani hawayen daya zubo a kumatun ta, wannan karan kanwar ke share mata duk da karancin shekarun kanwar amma hakan bai hana ta fahimtar halin da suke ciki ba.

Ta shi tayi ta na cewa "Ya kamata muje muyi bara Sofia, Ta duka da kyar ta na cewa hau baya na goya ki ba zan iya ɗaukar ki ba" kasancewar Sofia tun da aka haife ta, data fara girma sai bata tafiya ko miye dalili ohooo.

Sofia ta tausaya wa yayar tata,duk da karamar yarinya ce amma ta san cewa Yayar na ta na wahala sosai, ta mika hannu ta goya ta, suka shiga cikin mabaratan suma suna ta bara a haka har Allah yasa ta samu naira dubu biyu.

Yamma likis suna zaune a bakin titi, babu sallah babu salati sai bara kawai, sai alokacin ta samu ta sayi ruwan pure water leda biyu, da shi tayi amfani tayi alwala ta kwance kallabin ta bayan ta sauke Sofia ita kuma ta fuskanci alkibla ta jero salloli biyun da ba tayi ba, tana zaune a wajan aka kira magriba, ta tashi ta gabatar da sallar magriba......Tana kallon wasu mabaratan na tafiya masaukin su, yayin da wa su kuma suna zazzaune saboda babu wajan kwana.

ALMAJIRA ✔Where stories live. Discover now