Page 3

110 6 0
                                    

❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤💃🏽❤

                  ROYAL CONSORT
Korean inspired novel

         ©️ marriam mayshanu.... ✍️

Page 3

Labarin hukuncin sarki ya isa kunnen kowa a cikin masarautar,ciki kuwa har da Her majesty The queen,da kuma mahaifiyar sarki (queen dowager) hakan kuwa ba qaramin girgiza su yayi ba,musamman mahaifiyar sarki da ko da yaushe fatan ta bai wuce sarauniya ta samu juna biyu domin ta haifa wa masarautar su magaji ba,tana fatan hakan tun kafin ranar da mai martaba zai yi tunanin yin wani auren,wato ya kawo consorts cikin masarautar,wannan dalilin ne yasa hankalinta yayi matuqar tashi qwarai da gaske yayinda ita sarauniya ba za'a ce bata damu ba,amma damuwar ta ba mai yawa bace domin ta dad'e da sanin cewar matsayinta na matar sarki a suna ne kawai amma bata da wani gurbi a zuciyar mai martaba,dama dalilin da yasa yake zaune da ita saboda mahaifiyar sa ne,kuma sannan da dalilin dokar qasa,domin sarauniya tamkar Uwa take ga al'ummar qasa,hakan yasa idan har ba wani gagarumin laifi da kai tsaye za'a iya kiran shi da ta'addanci ba,to ko sarki bashi da ikon cire ta daga wannan sarautar tata,ma'ana ba'a sakin aure a gidan sarauta.

Sarauniya HANEEFAH mace ce mai sanyin hali,bata da hayaniya ko kad'an,tana da matuqar dattako da sanin ya kamata,kasancewarta a matsayin sarauniyar garin JOSHUN kuma shugabar inner court bai sa ta kasance mai jin kai,ko kuma amfani da mulkin da take dashi domin cusgunawa bayin Allah ba,hakan yasa ta fita daban daga halayyar mutanen da suke cikin masarautar,mutanen da idon su ya rufe akan mulki suke mata kallon lusara,saboda tana da dukkan ikon da zata aiwatar da dukkan abinda taga dama,ko da kuwa sawa a kashe wanda taga haka kawai bata qaunar ganinsa ne,fad'a kawai zatayi a aiwatar da hakan.

Dowager queen ce a daki sai kai kawo takeyi cikin zurfin tunani,duk tunanin ta bai wuce yadda za'a yi taga ta dakatar da shigowar jalilah cikin masarautar ba,amma kuma ita kanta tasan cewar ta makara domin aikin gama ya riga ya gama,tuni ofisoshin da suke da alhakin ciccike takardun da zasu bawa jalilah lasisin shigowa cikin fadar suka gama aikin su,rana kawai mai martaba zai saka,ita kanta ta rasa mafitar abinda take shirin yi,wani murmushi ta saki da alama akwai wani abin da ta d'arsa a ranta tare da zama akan wata shimfida dake qasa kamar katifa,sai qaramin tebur a gabanta daidai yadda mutum zai iya dora hannunsa idan yana zaune a qasan.

A bangaren Shukra kuwa haka ta wuni a ranar sukuku har mutanen ma'aikatar su suka fahimci akwai wani abu da yake damun ta,hakan yasa kowa ya daga mata qafa ranar,ita kadai take zaune bayan sallar ishaa gari yayi duhu sosai,waigawar da zata yi ta hango wata algaita (Abin kidan sarauta) nan taake tunanin yayanta ya fado mata domin gwani ne wajen busa algaita,tashi tayi a nutse taje ta dauko algaitar,ta fita can wajen filin ma'aikatar su qarqashin wata bishiya ta zauna,a hankali ta fara busa algaitar hawaye na sauka daga idonta,domin babu abinda take tunawa sai rashin ahalinta da tayi da kuma kewar su da yake damunta,haka ta cigaba da busa algaitar yayin da kidan algaitar yake ratsa cikin masarautar har cikin kunnen mai martaba da dawowar sa kenan daga ran gadi tare da babban bafaden sa sai guards guda biyu domin yana fita ne cikin badda kama,yadda idan ba saninshi kayi sosai ba,zai yi wuya ka iya gane cewar sarki ne,dai dai lokacin da kidan algaitar ya sauka a cikin kunnensa yai daidai da tsayawa yayi cak ba tare da ya qara gaba ba,a nutse yake jin yadda sautin kidan yake fita cike da qwarewa da qayatarwa,juyawa yayi ya kalli babban bafadensa (chief eunuch) yace
"Kana jin abinda nake ji kuwa?" Murmushi C.E yayi tare da dan rusunar da kanshi alamar girmama wanda yake magana dashi sannan yace
"Ina ji mai martaba,idan kayi umarni sai aje a taho da mai busar yanzu"
Martanin murmushin mai martaba ya mayar masa tare da cewa
"A'ah ba yanzu ba,amma gobe ina son kaje ma'aikatar masu kid'an (bureu of music) kaje ka taho min da mai busar zuwa grand palace"
Dan rusunar da kai yayi alamar girmamawa don da alamu hakan ya zamar masa jiki,idan har zai yi magana da mai martaba sai an durqusar da kai.

Shukra tana zaune tana busa algaitar ta,kamar wacce aka zabura ta miqe da sauri ta tafi taje ta ajiye algaitar a inda ta dauko,daga bisani da dauki hanyar inda suke wanki,cikin sa'a kuwa tana zuwa ta taradda wasu 'yan mata wanda shigen kayansu iri daya ne da nata amma nasu yafi nata tsafta da kyalli kuma kalar nasu shudi (blue) sabanin nata da yake brown ruwan qasa,da gudu taje ta qarasa gaban su ta tsaya,tsayawa sukai suna kallon yarinyar suna jiran suji da me tazo
"Barka da yamma my lady" abinda ta fada kenan cikin girmamawa (ta kirasu da MY LADY ne domin dokar girmama duk wanda yake gaba da kai a masarautar,su 'yan matan nan palace maids ne,wato wadanda suke aiki a ainihin cikin masarautar bangaren ahalin gidan) kallonta suke sheqeqe sai guda daya ce a cikinsu tayi mata kallon arziqi,ita kadai ta iya amsa mata maganar da tayi
"Lafiya kika tsayar damu haka? Ko kinyi batan kai ne? Daga ganin kayan da suke jikin ki dai na tabbatar ke servant girl ce"
Kada kai tayi alamar "Ehh" sannan ta qara da cewa "Dama zuwa nayi don Allah neman wani taimako"
Zaro ido sauran 'yan matan sukayi,suka kalli wacce ta fara amsa mata sukace
"Kina da lokacin wannan servant din kenan? To sai kin taho"
Kayan wankin da suka zo diba ne a hannunsu sukayi gaba suka barta ita da shukra a tsaye,matsowa tayi dab da shukra tace
"Fada min da me zan iya taimaka miki?"
Shukra ta sassauta murya tace
"Dama na san gobe ne asabar din qarshen wata da kuke aikin kwalemar cikin masarauta (monthly cleaning) shine dama nake son ko zaku taimaka min ina son na shigo na taya ku"
Kallon shukra take da mamakin me take son taje tayi a cikin masarautar amma dai bata tambaye ta ba,tace mata
"Ni ina aiki ne a quaters din ladies investigators ne,idan zaki iya zuwa da wuri gobe da safe amma kada ki bari kowa ya ganki,zan baki uniform dina sai muyi aikin tare"
Murmushi shukra tayi cike da farin ciki ta fara jero mata godiya,haka suka rabu tana mamakin abinda yasa shukra take son shiga cikin masarautar,haka tabar tunanin ta a ranta har ta qarasa inda zasu ajiye kayan wankin da suka dauko,tana jin qawayenta suna mata tsiyar ya ta qare da servant girl ,ita dai bata kula su ba ta shiga sabgar ta.

Shukra kuwa murna ce ta cika ta domin ta dade tana jiran wannan ranar da zata shiga domin dubawa ko zata hadu da court lady din da take nema,haka taje ta kwanta cikin dokin gari ya waye wataqila wannan shine mataki na farko da zata iya wanke sunan ahalinta da aka sa sunansu cikin 'yan ta'addan qasar.

Oum tasneem ✍️

ROYAL CONSORTWhere stories live. Discover now