Chapter 47-48

6 0 0
                                    

EPISODE 47 & 48

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

   Afnan da tun usulinta batason tashin hankali tafara kuka tare da durƙusawa a gaban Abdallah ta riƙo masa hannu , kana tace " dan darajar iyayenka ka kaida ta , bai yi magana ba sai ficewa da yayi daga ɗakin , momyn Sadiq kasa magana tayi sbda baƙin ciki Afnan ce ta rungimeta suka dinga kuka, bayan fitarsa driver ya shigo a guje tare da cewa hajiya mai gida na mota yana jiranki ,sallama tayi musu kana ta rufawa  mai gadi baya , buɗe murfin motar tayi ta shiga suka miƙi titi , babu mai cewa kowa komai , shikam zuciyarsa tafar fasa takeyi kamar garwashi gaskiya da ba zina tayi ba zai iya mai data amma tuna abin ya kasance da haka yana ganin sai dai su haƙura kawai , horn ɗin da driver yayi ne ya tabbatar musu da cewar sun iso gida , buɗe murfin motar tayi da sauri ta fice tana kuka , tana shiga palo ta wuce bedroom ɗinta da gudu ta faɗa gado tana wani irin kuka mai cin rai , ita kam tafi tausayin Sadiq ɗin a kan mahaifiyar tasa , can kuma wata zuciyar tace " ke meye naki na tausayin sa bayan bakida alaƙa dasu? gaki a cikin matsala ,

Kawar da zancen tayi ta ɗauko wayarta , lambar momy ta dannawa kira ring ɗaya ta ɗauka , sallama Afnan tayi bayan momy ta amsa Afnan tace "ya dady da anty suna lpy momy tace .

  "lafiyarki kuwa Afnan?"  naji muryar taki tayi kama da ta mai kuka , kuma dai dai ta muryar tayi kana tace " llah momy wlh ba komai nayi missing ɗinku ne inason zuwa , momy ce tace " to shine zaki ɓata ranki ? ki kwantar da hankalinki muna lpy karki dinga tada hankali kinga ba ke kaɗai bace , waro ido Afnan tayi kana tace " momy nikaɗai ce man au wai kun ɗauka cikine da ni ? eh momy tace " hmm wlh banida komai , cewar Afnan , momy ce tace " Allah zai kawo ki kwantar da hanlalinki kinji , to tace " tayiwa momy sallama , numbar anty ummi ta kira dan tasan tayi laifi yaushe rabon da suyi waya."

    Lokacin taga gidan Haisam tana cin azaba gurin mama batada wata uwa banda anty ummi yanzu kuma da ta auri burin iyayenta shine zata watsa mata ƙasa a ido ina , jin an ɗaga wayar ya sata cewa aslamu alaikum , daga ɗayan ɓangaren anty ummi tace " walaikissalam Afnan kinanan? uhm anty da farko dai ayimin afuwa dan Allah , nasan ban kyauta ba , share zancen anty tayi da cewa karki damu yarinyata ,

    nan suka kuma gaisawa kana sukayi sallama  , turo ƙofar da Abdallah yayi ne yasata kai dubanta ga inda ya ke , tsaye yake a bakin ƙofa ya zura hannayensa cikin aljihu , ya kallonta.

   Zaune suka a wani tsararren palo wanda yaji kayan more rayuwa wannan palo shine zakaji ana yiwa kirari da aljannar duniya , hajiya Maryam ce zaune kusada mai gidan nata wato Alhaji Aliyu mai nera , Alhaji Aliyu mai nera shaharaten mai kuɗi ne na ji da gani , sananne ne kowa ya sanshi a babu wanda zaka yiwa kwatancen sunansa yace " bai sanshi ba , shine uba ga Husna ƴa ɗaya tilo da Allah ya basu ,Husna tayi karatu sosai musamman ma na boko , har yanzu taƙi fito da mijin aure da zarar Alhaji yayi magana mahaifiyarta zatace guda nawa take karya takura mata , akwai wata rana tana cikin tafiya a motar ta , sai motar ta sami matsala , tana tsaye bakin titi motar Abdallah tazo wucewa , bayan ta sa masa hannu alamar ya tsaya ta roƙesa da ya temaka ya rage mata hanya zuwa gidansu,

    Suna cikin tafiya tana satar kallonsa dan Abdallah kyakyawane in baku manta ba , suna isowa tace " ya bata lambarsa , baiyi mata musu ba ya bata har ya zamo daga wanan rana tana kiransa suna gaisawa , kwanci tashi asarar mai rai , Husna ta fara nunawa Abdallah tsantsar soyayya tun bai san tanayi ba har yazo ya gane , wata rana yazo gidansu badan yaso ba sai cewa da tayi zasu gaisa da mahaifiyarta , yake gaya mata shikam yanada mata , Husna tayu baƙinciki amma kadancewarta wayayya ta nuna babu komai gashi yac" bai shirya yin aure nan kusa ba , itadai a tata zuciyar ta ƙudiri aniyar auransa ko ta wane hali  wanan kenan.

Alhaji ne ya dubi Hajiya Maryam yace " lokaci yayi da zan fitarwa da Husna mijin aure sbda lokutan da na ɗaukar mata sun cika , kukan da Husna ta fara ne yasa su Alhaji juyowa kallonta , kuma bai fasa maganar ba , Hajiya Maryam ce tace "a wanan karon ina goyon bayanka ai tanada samarin ruwan ido ne yasa take rainawa mutane hankali , Husna batada zaɓi banda dole ta karɓi zaɓin iyayenta amma kuka yaci ƙarfinta ,tashi tayi da gudu ta haura samma inada ɗakinta yake , ta faɗa gado tare da sakin wani sabon kukan , tunanin Abdallah da yayi mata nisa tafara yanzu yazanyi duk wata hanya da zanbi dan haddasa musu fitina na kasa dole nabi abinda su hajiya sukeso , da haka bacci mai nauyi yayi nasarar ɗaukarta ."

   Abdallah ne ya ƙaraso kusa da Afnan ya ɗauketa ya ɗora akan cinya kamar ƙaramar yarinya , raɗa mata yayi a kunne wai two days mai ya sami baby na ne tadena bani kulawa ?" narkewa Afnan tayi kana tace " nikam babu ruwana da kai , mekuma nayi ? cewar Abdallah , Afnan ce tace " dan me bazaka dawo da matarka ba ?" walwalar fuskar Abdallah ce ta gushe ya kalli Afnan yace " zaki iya zama da miji mazinaci ? zaro ido tayi tana kallon Abdallah da idonsa ya ciko da ƙwallah  tare da girgiza kai , to inhar bazaki iya ba karki ƙara yimin zancenta akwai maza a duniya bani kaɗai bane autan maza ya kamata kisani babu ni babu momy sadiq!!!!!.

    Jin zancen nasa babu daɗi takeyi amma babu inda zatayi dole ta kawar da zance dakuma tinanin momy Sadiq ta rungumi mijinta , rungumota yayi yana shafa mata gashin kanta tare da murza ƴan yatsunta , itama fara yimasa wani salo tayi na daban dama tayi amfani da maganin da momy ta bata , tunda naga Abdallah ya fara harata yasani rufo musu ƙofa nayo waje.

Yau Afnan ta tambayi zuwa gida , daƙyar Abdallah ya barta amma da sharaɗin karta daɗe, tun safe tayiwa momy waya akan gatanan zuwa , kowa na gidan murna yakeyi dan an daɗe ba'a haɗu ba , momy tasa an shirya mata abinci kala kala, dady ma yau bai fita ba sbda yanason su gaisa da ƴarsa ,

    Abdallah na fita ta fara shiri tana gyara gado taci karo da kuɗi masu yawaa  tunani ta fara ko Abdallah ya mance dasu ne , ring ɗin wayarta ne ya katse mata tunani , Abdallah me mai kiran amsawa tayi tare da cewa ka isa lpy , lpy lou sweety ina kewarki dariya Afnan tasa tare da cewa " kai mijina daga fitarka ? eh man Afy jinake kamar in dawo , zaro ido tayi kamar yana ganinta tasan inhar sukaci gaba da maganar zai iya dawowa yayi mata haramiyar zuwa gidansu , am sorry Allah ya dawomin dakai lpy mijina akwai tanadin da nayi maka so karkaji komai , nidai fatana karka bari ƴan mata su kallemin kai , dariya sukasa a tare kowa ya ajiye wayar , dafa ƙirjinta tayi kana tace " my man rigima , tacigaba da shirinta

LAMARIN ƘADDARAR AURENAWhere stories live. Discover now