Chapter 23-24

4 1 0
                                    

EPISODE 23 & 24
Tare da rungumo ta sun dad'e a haka , Afnan ta tattaro k'arfinta ta turashi gefe tare da galla masa harara , kai Abdallah wanan wace irin rayuwa ce? " kasan fa shed'an neman abokai yakeyi .

  Wata shu'umar dariya Abdallah yayi kana yace "nikam bazai galaba a kaina ba saboda komai kikaga inayi Afy kece sanadi , kina tunanin irin wanan shigar da kwaliyar bazai sa kowane d'a namiji jin sha'awarki ba ?" kisani niba dutse bane dazan dinga zuwa ina ganinki alhali inada tabbacin nine mijinki ,oya  zokiji , wasu zafafan hawaye ne sukayi nasarar zubo mata tace "babu komai banyi dan kayi sha'awata kamar hakan ba nayi ne dan na burgeka , k'ara matsowa Abdallah yayi tare da had'e hannayensa biyu yace " afuwan my Afy am sorry nasan nayi laifi kuma kar hakan dana fad'a yasaki dena yimin kwaliya ,uhm kawai tace "ta mik'e ta fice Abdallah ya rasa me yake yimasa dad'i gaskiya daya sani bai fad'awa Afnan wanan kalmar ba kash ya had'e hannayensa biyu , gwada lambar wayarta tafara dan yana son suyi maganar hidimomin da za'ayi a biki to gashi a kashe ranshi ne yakuma 6aci sai ya fara duba lambar momy , cikin sa'a ta shiga."

  Ring d'aya aka d'aga muryar momy ce dan haka ya sa ssaura muryasa tare da d'an risinawa barka da yamma momy , ywwa "barka dan Allah Afnan na kusa?" a 'a batanan , shiru yayi can kuma yace "to ya kashe wayar , momy ce ta fito parlor dubata amma batanan komawa bedroom d'inta tayi ,ta hangota a nannad'e a gado fuskarta sharkaf da hawaye , da sauri momy ta k'arasa kusa da ita tace " daughter meyafaru?babu komai momy ,to maiya faru naji kiran Abdallah yana nemanki fad'a kukayi ? a'a momy , momy ce ta had'e rai babu alamun wasa tace "ni mahaifiyarki zaki 6oyewa damuwarki ko ?mik'ewa Afnan tayi inda abinda ta tsana bai wuce fushin momy ba dan haka batason fushinta , momy kwanannan Abdallah ya tsiromin da abubuwa marasa kyautawa ,shine da rungumata ,sai kuma tayi shiru murmishi momy tayi a ganinta tana ganin y'arta zatayiwa matarsa zarra ,karki damu daughter , momy tace " cike da nishad'i , yau saura kwana nawa ne bikin ?saura kwana goma fa kwantar da hankalinki , daganan momy ta mik'e ta fice , Afnan ta kasa fassara maganar da momy tayi mata ...✍️.

Kardai Ku manta karku jini shiru ne yasa nayi muku wanan , kunsan dai haryanzu ban dawo ba , dukda yanzu andena comments ina tunanin zanbarshi sai zuwa bayan sallah kawai 👌tunda Baku nuna damuwa ba⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️

LAMARIN ƘADDARAR AURENAWhere stories live. Discover now