Chapter 31-32

4 1 0
                                    

EPISODE 31 & 32

   Ganin rana tayi kuma Maimunatu bata fito ba yasa mama miƙewa ta nufi kitchen ta kunna risho kasancewar bata iya kunna gas ba , ruwa ta dora da wake a haɗe dan da alama shinkafa da wake zata girka , fitowar Maimunatu daga ɗaki kenan ta leƙa ɗakin Haisam taga babu kowa ya fita , kitchen ta nufa hango mama tana gyaran shinkafa yasata cewa sannu , washe baki mama tayi cikin rawar jiki tace "sannu ƴar albarka."

  sai da Abdallah ya sami nutsuwa da Afnan sanan ya shafo fuskarta tare da manna mata kiss a goshi , Allah yayi miki albarka duk da wani ya rigani amma dole nayi alfahari da wanan rana gaskiya Afy kin shayar dani zuma , Afnan dake kwance tana kallonshi yana sumbatu ta rungumeshi tare da raɗa masa a kunne tace "karka damu mijina koda wane lokaci ina tare dakai , wanan maganar ta Afnan tasa shi jin daɗi sosai ya miƙe ya shige toilet ya sakarwa kansa ruwa , wankan tsarki ta fara kana yayi na sabulu ,Afnan miƙewa tayi ta ciro masa boyel mai laushi baƙi da farar hula da farin takalmi kasamcewar akwai wasu kayan nasa a ɗakinta ..

  Yana fitowa ta shige itama wanka tayi tare da na tsarki ta fito kanta ɗaure da towel na tsane ruwa ,

  Samunsa tayi har ya shirya sai zuba ƙamshi yakeyi ga wani sihirtaccen kyau da yayi mata ..

  Kamo hanunta yayi tare da ɗorata kan cinyarsa yace "gaskiya zanje in dawo ki kularmin da kanki ,

  Ƙara marai rai cewa tayi ta ce "gaskiya nagaji da fitarnan inace hutun two weeks ka ɗauka ,

  Buɗe baki Abdallah yayi yace "wane ni yazanyi da jama'ar da suke jirana in dawo ?"

    Uhm to yanzu ina zaka ?"zanje duba Sadiq ne wai sun dawo gida ..

   Kishi ne ya tasowa Afnan amma dole ta danne dan tanason samun fada a zuciyar Abdallah ,ka gaishe shi shida momyn 'nashi oky Abdallah yace "yana ɗaura agogo a hanunsa,

   Shafa fuskarta ya ƙarayi kana yace "natafi  Allah ya tsare Afnan tace "fuskarta ɗauke da murmishi ."

da isarshi gidan takalma ya gani a ƙofar ɗakin zasukai na mutum huɗu ,nazari ya kamayi dan lokacin magrib ta farayi , jiyo surutun su yayi suna cewa ai wlh hajiya ki kaɗa ƴar banza ...

  Kina zaune da mijin zata fara kawo miki cikas  nifa dama bason aurannan da yayi nakeba duk da bani ke zama dashi ba ...

   Momyn Sadiq ce tace "uhm ni yanzu ma kullum sai nayi kuka sbda ya sabarmin da komai nasa , wata daga gefe tace "uhm nidai banida  ta cewa tunda tun farko baki ɗauki shawarar mu ba ....

   Akwai wani hatsabibin malami wanda yataɓa yimiki aiki har kika samu cikin Sadiq .

Tagumi ta zuba alamar tunani , momyn Sadiq ce tace "wlh wanan karon bazan aikata zina ba inaji ina gani ,

  Nice ban jira lokaci ba ai likitoci sunce akwai lokaci dagani har mijina muna aihuwa ,

   taɓe baki sukayi tare da miƙewa sukace to kizauna ta kasheki karkuma ki neme mu , fashewa tayi da matsanancin kuka ta miƙe tsaye tana takowa gabansu tace ...

   To ni mezan sa boka yayi mata ?" sallamar da sukaji ne yai sanadiya faɗuwar gaban momyn Sadiq ta dafe ƙirji suko sauran ko a jikinsu sukayi waje kowacce na kallon Abdallah ."

   Zama tayi jugub a kujera tana share gumin da yake karyo mata tare da mai maita innalilahi a zuciyarta .

Abdallah wayarsa ya ciro yafara danne danne amma inka lura dashi sosai hankalinsa a tashe yake ,

Ko kaɗan bata ƙaunar taji  yayi mata magana hakan yasata miƙewa ta nufi hanyar da zata sadata da bedroom ɗinta keee!!! taji Abdallah yace " cikin tsawa juyowa tayi batare da tace "komai ba ,

   Kuma maida hankalinsa kan wayar dake hanunsa yayi a zahiri kukan zuci yakeyi dan nafili yaƙi fitowa .

Takai wasu mintuna a tsaye a gurin dan yanzu tsoransa ma takeji kar tayi ƙwaƙwaran motsi ya yanke mata mumunan hukunci,

Tashin hankali gami da rashin ƙaunar maman sadiq ya darsu a zuciyar Abdallah ,mai maicin da zuciyarsa take yimasa shine zina ?zina tayi kenam ba ɗana bane ?" ya ilahi ya riƙe kansa da yake sara masa."

   Ya ɗago kansa ya dubi maman Sadiq yace "naji duk abinda kuke ta taunawa akai dame na rageki ci ko sha ko tufafi kokuma haƙinki ne bana saukewa kiji tsoron Allah ,

  Yaci gaba da cewa kin cuceni kin cuci  ɗanki dan bazance ɗana ba ,

   Momyn Sadiq jira take taji kalamin Abdallah na ƙarshe yace ya yafe mata sai taji akasin hakan yace " na sakeki saki biyu inkin sami miji kiyi aure kuma ki tafi da ɗanki banida alaƙa dashi.....✍️.

Fans kuyi haƙuri kwana biyu kunjini shiru nayi tafiya ne amma na dawo ganin sharhinku shine zai sa kusami pagin gaba amma in bangani ba sai bayan sallah gaskiya 🤗.

LAMARIN ƘADDARAR AURENAWhere stories live. Discover now