Chapter 25-26

5 1 0
                                    

EPISODE 25 & 26

   Ganin cikin Maimunatu yafara girma yasa Haisam fara kula da Maimunatu , hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba , tana ganin yanzu ya dawo sonta ne sosai , yau juma'a Haisam na zaune a kasuwa yaji wayarshi na ring cikin azama ya ɗauka ,jiyayi ance "kai ne Haisam ? eh nine Haisam yace "cikin rawar jiki duk da bai san mai kiransa ba ,amma yana tunanin alkairi ne ,malm Haisam muna nemanka a shagon mu na sai da turaruka muna odar su daga Dubai abokina ne ya bani lambarka , gaskiyarka da riƙon amana yasa nayi maka magana , cikin rawar jiki Haisam yace "to nagode ya waiga ya kalli ƴan tsirarun kayan dake jere a shagonsa kayan kwaliya ne basuda wani yawa amma Allah ya sanya masa albarka a cikin sana'ar ."

    Ya naji kayi shiru ?babu komai Haisam yace sukayi sallama , Haisam na ajiye waya yafara saƙa da warwara anya zai yarda da ƙudirin mutumin nan ? baisan ko waye ba hmm , ya zurfafa cikin tunani yaji sallamar Abubakar babban abokinsa yanada shago a nan kasuwar jos ɗin wato ƴan tifa yana sana'ar sai da atamfofi ,shima yanada katafaren shago babba kuma suna bada sarin atamfofi , gefe kuma takalma ne masu kyau da tsada , Haisam abokina ya kiraka ?" Haisam ne yace "eh ya kira "to ka amince zaku fara kasuwanci tare ? uhm Haisam yace " bawai naƙi bane amma inason kasani wanan ɗan akurkin shagon da nake rainawa yana rufamin asiri ina tunanin ranar da Allah zai yi ikonsa ya zamo bana wancan shagon kaga akwai damuwa ,

   Abubakar ne ya taɓi kafaɗar Haisam kana yace "karka fara wanan tunanin abokina insha Allah bazakayi kuka da Alhaji Jamilu ba ,mutum ne na mutane kuma bashida ƙeta , to Haisam yace "Allah ya zaɓa mana abinda zai zamo alkairi , amma bazan bar shago naba dole zan nemi mai zama a ciki , daganan sukayi sallama kowa ya kama gabansa ."

   Haisam ne ya tada mashin ɗinsa bayan ya rufe shago duba agogon hanunsa yayi ƙarfe biyar na yamma , hakan yasa shi ɗaukar titin da zai sadashi da gidan sa , yana isa ya kashe mashin ɗin tare da tura ƙofar kasancewar Maimunatu ba rufewa takeyi ba ,ya shiga da mashin ɗinsa ya kullo ƙofar , da bayan ya jingine mashin ɗin ya nufi  ɗakinsa ya kwanta batare da ya doshi ɗakin Maimunatu ba , da shigowarsa da komai Maimunatu na gani ta windo."

   Yunƙurowa tayi da ƙaton cikinta a ƙalla zaiyi wata biyar ta gyara ɗaurin zaninta , saukowa tayi daga gadonta kana ta fito palo , ganin yamma tayi bata ɗora komai ba yasata jan dogon tsaki tace "wanan wace irin rayuwa ce ga ciki ga aiki ni wlhi bazan iya ba sai kace wata baiwa , haka dai ta ƙarasa ɗakin Haisam ta tura ƙofar babu sallama, hangoshi tayi kwance dagashi sai gajeran wando ,sosa kai tayi tare da yatsina fuska tace "sannu da dawowa , juyowa yayi ya ɗan kalleta yace "yawwa ya jikin ? da sauƙi tace kana ta zauna gefensa ,yanzu dai yaɗan rage tsanar da yayi mata albarkacin wanan ciki na jikinta , shima a halin yanzu yana son ganin jininsa , shiyasa yake ɗan sakin jiki da ita , janyota yayi tare da rungumeta yafara  haɗe bakinsu guri guda tare da shafa bayanta , tuno azabar da tasha a daren su na farko tayi kuma tunda Haisam ya yi sex da ita bai ƙara yiba sai yau , zaro ido tayi kuma gashi tanason ta cima burinta na wani shu'umin magani da mamanta ta kawo mata hakan yasata daurewa ta fara maida masa da martani , ganin cikin zafin nama yake komai yasata fahimtar yana buƙatar ta , cikin zuciyarta tace "Allah ka bani ikon daurewa a wanan karon , fitowa nayi domin leƙa gidansu momy."

   Yau alhamis ,asabar ɗaurin aure gida yafara cika da baƙi su Anty Aisha itace a sahun gaba su momy da Anty ba ƙaramin haushi sukeji ba akan rashin yawan shawarar da Alhaji bayayi dasu , amma a hakan hausawa sukace komai wayon amarya ..... yau takama juma'a akayi sa lalle kasancewar Abdallah ya cikawa Afnan account batada matsala da kuɗi, komai tsadar tsadar abu inhar momy tagani to bata ƙyashin siya saboda kyansa , babu wani wasanni da sukayi , washe gari asabar dubban al'umma suka sheda ɗaurin auran ABDALLAH DA AFNAN akan sadaki mafi albarka      dubu ɗari lakan ba ajalan ba , kowa ka gani fuskarsa cike take da annuri anci ansha amarya na hango sanye da wani haɗaɗen less mai ruwan pink da flawoyi baƙake a jiki ba ƙaramin kyau tayi ba fuskarnan tasha makeup sai sheƙi takeyi , ƴan uwan momy ne suka riƙe hanunta suka shiga da ita sashen Alhaji kasancewar babu kowa duk suna ɗakin baƙi , Alhaji munkawo Afnan ne ka sanya mata albarka , cikin farinciki dakuma nishaɗi dan Afnan ta auri wanda dady yakeso yasashi cewa , Allah ya albarkaci auranki Afnan Allah yayi miki albarka , kanta a sunkuye wasu zafafan hawaye ne suka zubo daga fuskarta."

Tunowa tayi da lokacin auranta da Haisam dady ko kulata bayayi da aka kawota gabansa lokacin da za'a kaita gidan mijinta cewa yayi bashida abin cewa , amma yau itace yake cewa haka , tashi kuje Allah yayi miki albarka yar albarka , wani sanyi taji ko ba komai zata aurin zaɓin iyayenta a gurinta babu abinda yakai farincikin su a gurinta."

    Ɗakin Anty suka wuce da ita itama fuskarta cike da fara'a tace "madallah naji daɗin ganin wanan rana , anty Ummi dake gefe ta ja Afnan wani ɗaki banji mai sukace ba suka fito suka koma ɗakin momy.

   Misalin ƙarfe takwasa kowa yayi sallah ya idar motoci suka fara hallara a harabar gidan , daga ganin motocin ma kasan kaf cikinsu babu na haya duk na ma'aikatane  , Allah sarki rabuwa da iyaye sai dole Afnan ta ƙanƙame momy sai kuka takeyi momyn ma sai da ta zubar da hawaye sosai ganin Afnan tanata gursheƙen kuka, kasancewar ba wasu ƙawaye ta ɗiba masu yawa ba suka shige mota Afnan ma da ƙyar suka sanyata tanata kuka , ganin babu kowa a motar daga ita sai Abdallah a gefe , sai ma yanzu ta lura dashi , a gefenta sai direba , da ya maida hankalinshi ga wayar dake hanunshi , waro ido Afnan tayi shima Abdallah maida mata da martanin waro idon yayi ya sanya hanunshi cikin nata suka fice , kasancewar kowa ya fice daga gidan iya motarsu ce kawai, Afnan dai bata yi magana ba kasancewar jinta takeyi kamar zazzaɓi ne zai kamata , tafara haɗe hannayenta biyu tare da rintse idonta dataji yana yimata zafi .....✍️.

Ga

LAMARIN ƘADDARAR AURENAWhere stories live. Discover now