chapter 6

116 11 4
                                    


Cikin kaɗuwa Ammi ta ce. "Subhanallahi, Na'ima kin san me kike cewa kuwa? Baban nawa ne zai aikata wannan mummunan aikin?"

"Wallahi Ammi dagaske nake, kin san dai ba zan yi masa k'arya ba, ki zo ki ga yanda suke yi da Yarinyar, zaki tabbatar Ɗa da Mahaifi ne."

Jiki a sanyaye Ammi ta ce. "Wannan maganar ba ta waya ba ce, bari na kira Alhaji, za mu zo yanzun nan insha Allahu, amma dan Allah kar ki tayar da hankalinki da yawa, kin san a yanayin da kike ciki ba'a buƙatar ki saka damuwa a cikin ranki."

"Toh Ammi sai kin zo" Ta faɗi haka cikin kuka, zuciyarta na yi mata wani irin suya saboda tsananin kishi. Khamal ya shayar da ita ruwan mamaki, ba ta taɓa zaton haka daga gare shi ba, she trusted him over, ashe ya ce zai nuna mata halinsu na sojoji.

Cillar da wayar ta yi ta fito daga ɗakin kamar mahaukaciya, ko nauyin cikin jikinta ba ta ji. Zaune ta tarar da Captain a parlour kan kujera two seater, Abra na jikinsa ta yi bacci abinta. Kallon Television yake yi hankalinsa kwance tamkar babu wani abu na ɓacin rai da yake damun shi. Hakan ya ƙara k'ular da Na'ima, ta tsani wannan maziyar tasa, abu ya faru ya mayar da kai mahaukaci shi kuma ya dinga pretending like everything is okay.

Kamar zautacciya ta fara cillar da pillows ɗin kujera cikin kuka tana faɗin. "Wallahi Khamal ba ka isa ka tozarta ni ba, sai na kashe ka na kashe yarinyar in yaso nima a kashe ni!" Khamal dake bin ta da wani irin kallo cikin tsawa ya ce mata. "Na'ima! Wallahi kika sake wani abun ya samu Yarona da ke cikinki garin haukanki sai na nuna miki ɓacin raina, wanda baki taɓa ganin irinsa ba."

"Ya mutu ma ina ruwana Ni, kuma ɓacin rai ka daɗe baka nuna mun shi ba, ƙarƙari dai ka ce ka sake ni in tafi in bar maka gidanka, to idan ka sake nin sai me? Na ce sai me?" Tai maganar tana zazzare idanunta da sukai jawur, saboda azabar kishi da kuma kukan da tai.

A firgice Abra ta farka daga baccin saboda hargagin Na'ima, fashewa ta yi kuka tare da ƙanƙame Captain tana kiran sunan "Abbi".

Cikin tsana Na'ima ta wurga mata wani kallo tana huci kamar zata ci babu, ji take tamkar ta fizgo Abra daga jikin Khamal. Tsaki Captain ya yi ya miƙe tare da Abra a jikinsa ya shige bedroom ɗinsa yana rarrashin ta. Ganin haka yasa Na'ima fashewa da kuka tare da zama daɓas akan kujera, ganin yadda ya maida ita mahaukaciya.

"Khamal why? Me yasa zaka mun haka? Ban cancanci haka daga gare ka ba, kar ka saka mun tukwicin k'aunar da nake yi maka da cin amana."

Ta faɗi haka cikin sheshshek'a.

Ƙarfe biyar da mintuna su Ammi suka ƙaraso gidan, har lokacin Na'ima tana zaune a inda take, ta ci kuka ta gode Allah, sai wani irin haki take yi saboda tsabar ɗorawa kai masifa, ga nauyin ciki.

Tana jin ana knocking ta miƙe da sauri ta buɗe ƙofar, zatonta ya zama gaskiya su Ammi ne tare da Baffa.

Granny ce a gaba, baki buɗe take kallon Na'ima bayan sun shigo, tafa hannuwa ta shiga yi ta ce. "Na shiga uku ni Mari, wannan fita hayyacin naki da kika yi Na'ima na mene ne? Ko waya aka yi miki aka ce tsohuwa ko tsoho wani ya mutu?"

Na'ima ba ta bi ta kanta ba ta yiwa su Ammi sannu da zuwa cikin dauriya.

Kama hannunta Ammi ta yi cikin lallami ta ce. "Na'ima ba ki ji abun da na faɗa miki ba ne na cewa ki kwantar da hankalinki? Kin ga yanda kika koma kuwa?"

Sake fashewa tai da kukan tace "To Ammi ya zan yi? Ba ki ji yanda zuciyata take mun wani irin zafi da suya ba ne."

Baffa ya yiwa kansa mazauni ya ce. "Ina shi Khamal ɗin yake?"

"Yana ɗakinsa tare da Yarinyar." Na'ima ta faɗa cikin ɗacin rai.

"A'a, wacce yarinyar kuma? Me kuke zance akai ne? Me yake faruwa ne?"

DARE DA DUHUWhere stories live. Discover now