A ranar da Na'ima su kai faɗa da Salima, washegari ta shirya tace ba zata cigaba da zama ba, tafiya za tayi gida.

Captain yace "dear, yanzu tafiya zaki ki barni a nan, nika ɗai?"

"To zaman me zan cigaba da yi, ka san EDD ɗina ma ya kusa, gara ina gida haihuwa ta zo min, tun da suna kula da kai kuma an kusa sallamar ka"
Haka ya ƙyaleta, tai shirinta ta juya Kanon dabo.

Washegari da safe wajen ƙarfe sha ɗaya na safe, Salima tai wanka ta shirya ta koma gurin Khamal, a hanyar da zata sada ta da ward ɗin da yake, ta haɗu da Faruk hannunsa ɗauke da Abra.

Ta tsaya suka gaisa, ta kalli Abra tace "ina ka samo wannan cute Babyn haka?"
Nan Faruk yai mata bayani yace "a gurin operation Captain Khamal ya tsinto ta, tana gararanba a cikin daji, Kuma ikon Allah, Allah ya haɗa jininsa da ita sosai"

Salima tace "ita ma kidnapping ɗin nata a kayi?"

Yace "Sanin gaibu se Allah"

Tace "ikon Allah, to an gano iyayenta?"

Yace "A'a, ba'a gano su ba, tana gurin wata staff ɗin mu ne, Madam Halima matar Captain Abdussamad Goza"

Tace "ok, Allah sarki shes cute Masha Allah, to yanzu ya za'ai da ita? Tun da ba'a samu iyayenta ba?"

Faruk yace "Ai da kyar ne idan ba Captain ne ze ɗau yarinyar nan ba, dan kamar sun daɗe da sanin juna, yana son yarinyar sosai dan har ya raɗa mata suna, it ma Abbi take ce masa, kamar sun san juna,. Se dai be gayan abun da ya yanke ba amma nafi kyautata zaton da ita ze koma, ya riƙeta kan a ga iyayenta"

Ɗan shiru Salimaa tai kan daga bisani tai ajiyar zuciya tace "thats good" daga nan ta wuce zuwa in da Khamal yake.

A wannan karon ma bata samu kulawa daga Khamal ba, sema tijarar da yai mata ya koreta daga ɗakinsa.
Idan da sabo ta saba da wannan abubuwan na wulaƙanci da hantara da yake mata, amma sam ba ta damuwa, ita dai burinta ya amsa yana sonta.

Washegari ta koma cikin barrack, cikin ikon Allah ta bi ta compound ɗin su Madam Halima, abun mamaki ta ga Abra a tsaye hannunta da teddy ɗinta, tana rarraba manya manyan idanunta tana ƙarewa gurin kallo.

Ƙarasawa in da take Salima tai, ta durƙusa a gabanta tace "cute baby, how are you?"

Ɗan ja da baya Abra tai tana kallon Salima.

Wani tunani ne ya faɗowa Salima, ta kuma matsawa kusa da Abrar tace "ina da sweet, ai zaki sha ko in baki?"

Still Abra ba ta amsa ba, saboda ba ta iya jin abunda Salima ke faɗa.

"Ok, zomuje in kai ki gurin Abbi"

Bakin Salima ta ƙurawa ido, taga kamar Abbi tace.

Ta miƙawa Abra hannu, aikuwa ba musu ta bita, saboda ganin laɓɓan Salima sun ambaci Abbi.

Salima ta ɗauki Abra ta tafi da ita.

Yadda a kai Abra ta fito kuwa shine Madam Halima ce t fita  tare da Abra, da suka dawo ne, taga Abra ta tsaya tana kallon murguza murguzan karnunkan da ke kaiwa suna komowa a compound ɗin, ta ɗauke Abra ta shiga da ita gida, a zatonta ko tsoronsu take ji, sedai bayan shigarta wanka, Abra ɗin ta sake fitowa tana kallon karnukan, wanda a nan ne Salima tai awon gaba da ita, tare da ƙudurce wani abu a ranta.

Tun da Madam Halima ta farga Abra ta ɓata ta shiga cikin tsananin damuwa da tashin hankali, saboda Abra ta shiga ranta matuƙa, sannan da ya zata fara bayanin yarinyar da aka bata ajiya ta ɓata?.

Captain Khamal kuwa ji yake tamkar zuciyar sa zata fashe, maimakon yai murna ze koma garinsa da yai wata da watanni baya nan, amma ya kasa farinciki saboda ɓatan Abra, ji yake kamar 'yar cikinsa ce ta ɓata, haka nan yaji yana ƙaunar yarinyar, dan har a wani sashi na zuciyar sa yana jin idan iyayenta suka bayyana be san ya zeyi ba, sakamakon tsananin ƙaunar yarinyar da yake yi.

DARE DA DUHUWhere stories live. Discover now