Chapter 1&2

68 4 2
                                    

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
      💍     💍      💍
💦 🌹🌹🌹🌹🌹🌹💦
    *LAMARIN KADDARAR AURE NA!!!.*

         💍     💍     💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_ZAINAB HABIB {Mom islam}_

  

Masu son NIDA YARINA da MK MIJIN DELU da complete ɗin LAMARIN ƘADDARAR AURENA suyimin magana ta whatsapp mata zallah pls 👉08141799224

EPISODE 1& 2

    Gidane d'an madai daici , baza'a kira masu gidan da talakawa ba ,amma sunada rufin asiri , d'akuna biyar ne , a cikin gidan , da kitchen da d'akin matar gidan dakuma bayin waje sai d'akin bak'i  daga gefe kuma a cikin d'akin matar gidan d'akin mai gidan ne a ciki ,wato mu had'u a parlor sai toilet a gefe , malale gidan yake da fasasun tails ,gefe ga pampo ,wata matashiyar mata na hango tana fitowa daga d'akinta , fara amma ba sol ba sanye take da doguwar riga ta atamfa mai ruwan ganye da kwaliyar flawoyi a jiki , rigar ta zauna a jikinta sosai , ta fito da asalin kyaun ta dakuma kyan diri na cikinta , hannayenta sanye suke a awar waro wuyanta kuwa wata sark'a ce y'ar k'arama , bakinnan yasha pink d'in jan baki , a k'ala zatayi shekara ashirin da biyar 25yrs , kitchen ta nufa , tukunyar dake kan risho ta sauke ta dawo ta   koma d'akinta , ta fito da jug da food flaks , kitchen ta nufa , bud'e tukunyar da ta sauke yanzu tayi , jollof d'in shinkafa ce yaji salad da carrot da albasa , sai k'amshi take zubawa , bud'e kular tayi ta zuba abincin ta rufe , ruwa ta d'ibo a randa ta zuba a cikin jug d'in , ta maida murfin ta rufe , tirai ta d'auko a kwando mai adon falawoyi a jiki ta jera abincin da cokali da plet da kula a ciki , ta nufi parlorn ta dashi , wani d'an madai daicin tebur ta ajiyeshi , kana ta koma bedroom d'inta , ta zauna a gaban stool tana kallon dressing mirror , k'ara shafawa fuskarta powder tayi tare da k'ara feshe jikinta da humra masu k'amshi ."

   Daga kanta tayi ta kalli agogon dake manne a jikin bango , k'arfe tara na dare , mik'ewa tayi ta k'arawa d'akin turaren wuta  ta ciro wayarta dake , chaji  wata number ta danna cikin sa sanyar murya tace ”amincin Allah ya tabbata a gareka mijina , daga cikin wayar wanda takira yace ”Afnan sarauniyar mata afuwan yau nayi dare ,yanayin aiki ne amma insha Allah ganinan , zuwa mekikeso ?"k'ara rage muryarta tayi tace ”banason komai Allah ya dawo dakai lafiya ,amen yace ”daganan suka kashe wayar , bacci ne yake k'ok'arin surarta tana k'in kwanciya , jiyo bugun k'ofa tasata ficewa da gudu , bud'e k'ofar tayi , tana ganinsa ta rungumesa tana dariyar farinciki , d'agata sama yayi yace ”ammata ba kya girma ko da alamu bakici abinci sosai ba ?" naci Afnan tace tana dariya , rik'o mata hannu yayi sukayi bedroom d'inshi , temaka masa tayi da cire kayan jikinsa ,ta rakashi toilet nanma ta temaka masa yayi wanka , wanan ta zamo al'adarsu tun tana amarya yanzu gashi shekararta biyu ,amma babu wanda zai ce tayi wanan shekarun komai nata kamar na budurwa , tare suke wanka sai dai inbabu mutum d'aya hakama cin abinci tare sukeyi abincin rana ko sbda babu organ nata sai lokacin da tayi ra'ayin cinsa ."

   Temaka masa tayi da shafa mai , ta dubo masa kayansa a drowa , wando gajere da farar singlet , gado ya hau zai bud'e laptop d'insa , cikin Maria raicewar murya tafara bubuga k'afa tana cewa uhm uhm my Hubby kazo muje kaci abinci , Hankalinshi ya tafi ga laptop d'in da ya bud'e , yace ”jeki ganinan , no bazan wuce ba harsai ka taso ,mik'ewa yayi tana gaba yana biye da ita , teburin data jera masa abincin sa ta nufa , bayan ya zauna ne , ta zubo masa tare da sa nata cokalin tana bashi a baki , shima hakan yake himata , har sai da suka k'oshi sanan kowa yai brush , Afnan na ganin Haisam zai wuce ,bedroom d'inshi ta rik'o masa hannu cikin shagwa6a tace ”yanzu lokacin bacci ne kadinga hutawa rayuwarka , badan Haisam yaso ba ta dawo suka wuce nata bedroom d'in ."

   Washe gari ta tashi da shirin zuwa anguwa , bayan Haisam ya fita tagama komai na gidan da yazame mata farillah , misalin sha biyu na rana ,tajiyo ana bubuga k'ofa , mik'ewa tayi ta je gurin mai buga k'ofar , tana bud'ewa gabanta ya fad'i , mama ce sanye da hijabi , tasan lokacin kukanta yazo , cike da masifa mama , ta shige ciki batare da tayi sallama ba ,Afnan ce ta bi yanta ,a parlor maman ta tsaye tana k'arewa gidan kallo , mtsw taja tsaki ,tafara sababi , ga gida har gida ,amma babu y'a y'a nikam Haisamu ya kwaso mana juya , ta fashe da kuka ,
  
  Afnan data mik'e daga durk'uson da tayi tace ”mama itafa aihuwa rabo ce , kee rufemin baki banason kinibibi , wayasani ma ko kafin auran naku kinje kinsha abinan na hana d'aukar ciki , shiru Afnan tayi ta sunkuyar da kai k'asa , inda sabo ta saba da gorin mama , amma ba'a sabo da wulak'anci , yasata fashewa da kuka mai ban tausayi, kitchen mama ta shiga hango gwan gwanin madara yasata Ciro ledar da ta sak'ale a Mara tasa cikali ta d'ibi madarar ta fito , itadai Afnan ta koma d'akinta ."

LAMARIN ƘADDARAR AURENAWhere stories live. Discover now