Mama na fitowa tayi waje ko rufo k'ofar batayi ba , Afnan ce ta mik'e ta fito waje , wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata , tanata zancen zuci ,ace tunda nayi aure banida kwanciyar hankali uwar miji tasani gaba , akan maganar aihuwa , ta kuma fashewa da kuka , tana cikin haka mak'ociyarta ta shigo suna mutunci sosai sunanta Fatima , mamaki  ne ya kamata ganin k'ofar gidan a bud'e , shigowa tayi da sallama tace ”Afnan har yanzu baki shirya bane ,ni gashi harna gama komai , kan Afnan a sunkuye bata d'ago ba , Fatima ce ta rik'o hanunta tare da shigewa da ita d'aki suka zauna , Fatima ce tace ”ko baki gayamin ba nasan mama ta shigo amma dan Allah kiyi hak'uri ki cire wanan surutun nata a zuciyarki , Allah ne me bawa kowa aihuwa kemafa bawai baya sanki bane ya hanaki , kuma ko asibiti da kikaje kince likitar tace ”lokacine beyi ba amma zaki biye mata hankalinki yadinga tashi ?".

   Afnan ce a share hawayenta tace ”Fatima kinfi kowa San in halin da nake ciki kuma kinfi kowa na anguwar nan sanin halin mama , takuma share hawayen da suka sake zubo mata race ”aurena da Haisam yin Allah bana mutum ba ,cikin tausayawa Fatima tace ”nasani amma kirage sawa kanki damuwa , tashi ki shirya muyi mu tafi , cikin fushi Afnan tace ”Fatima bazan iya zuwa ba wlh kwai kije zanje wata rana , babu rarrashin da Fatima batayiwa Afnan ba 'amma furr tak'i , haka Fatima ta wuce gida zuciyarta babu dad'i ko kad'an, bedroom d'inta ta koma ta kifa kanta akan fillo tana kuka , tana cewa ya Allah ka kawomin aihuwa cikin satinan Allah ka duba irin gorin da nakesha a gurin dangin mijina ."

Tana cikin kuka taji wayarta tana ring dubs mai kiran tayi , ganin my husband ,yasata dai daita muryata ,tace ”amincin Allah ya tabbata a gareka mijina ya aikin , dafatan babu wata matsala ko ?"dariya Haisam yayi yace ”wato ni zaki yiwa wayo ko ?"waya saminke kuka ? dariyar yak'e tayi kamar yana ganinta tace ”ba kuka nakeyi ba, kwai kai na ke ciwo , hmm Haisam yace ”badan ya yarda ba yace ”to ki kularmin da kanki , daganan sukayi sallama jiki a sanyaye , sallama taji na muryoyi da dama tasan ko suwaye , hakan yasata mik'ewa ta fito parlor su biyu  ne y'ammata ,da Khadija da Aisha , taunar cingom sukeyi cikin isa da wulak'anci , Afnan ce ta k'araso da fara'arta tace ”ah sanunku da zuwa , ko kallo bata ishesu ba bare tasa ran zasu amsa mata , neman guri tayi ta zauna a gefen kujera ,  Khadija mai shekara goma sha biyar ta mik'e tana yarfe hannu tayi kitchen , Afnan ce ta taso cikin zafin rai tace ”gaskiya yau bazan yarda ba ,kunason wulak'anta min gida ,  Aisha ce ta mik'e tare da gallawa Afnan harara tace ”gidan yayan mu ne dole muyi abinda ranmu yakeso ."

   Zuciya ce ta d'ibi Afnan ta wankawa Aisha mari ,da gudu Khadija ta shigo jin k'arar kukan Aishe ta cakumi wuyan Afnan , Afnan ce ta kaimata mari , dayake k'arfi ba d'aya ba , Afnan ta nad'a musu duka , girkin da basuyi ba kenan suka , wuce gida rai a 6ace , zama Afnan tayi tana girgiza k'afa , tana jiran abinda zai biyo baya, indomie ta dafa dan yunwa ce ta addabeta , tana gama dafawa ta kwashe a plet ta fito kenan ta jiyo tafiyar da bata tunanin ta kowace face ta mama , mama na shigowa ta ka6ar da abincin kana ta murjeshi a k'asa , bala'i tafara yo gidan ubanki ne kokuwa , dan sunzo ziyara gidan yayansu shine zakiyi musu duka , matsiyaciya juya kawai , Afnan ce ta dubi mama ido cike da hawaye tace ”mama menayi dahar kike jifana da wanan mugun kalamin ?"marine ya biyo bayan k'arshen maganar ta , juyawa mama tayi tana dura mata zagi."

    Afnan ce ta koma d'aki rik'e da kumatu tana kuka , janyo akwatin ta dake saman durowa tayi tafara loda kaya , sai da ta cikashi tabb sanan ta d'auki hijab d'inta ta fito waje , kulle gidan  , ta mik'awa Fatima mukulli Fatima da ganinta tace ”ina zuwa kuma yau , Afnan na kuka tace ”zani gidan iyayena , bazan zauna ba , Fatima cikin tausayawa tace ”karkitafi bada izinin mijinki ba ,girgiza kai Afnan tayi tace ”karkiyimin haka ,iya hak'uri nayi to yau nagaji da zagarmin iyaye da akeyi wlh , babu inda Fatima ta iya ,sabda tasan iya hak'uri Afnan tanayi , an k'ureta ne , haka ta k'ar6i mukullin ta janyo hijab a igiyar shanya tabi bayan Afnan , mashin ta tara ,sai da ta d'ora akwatin sanan ta hau tana d'agawa Fatima hannu ."

   Mislin k'arfe goma na dare Haisam ne ya keta bubuga k'ofa amma shiru , cikin mamaki ya nemi guri a kan mashin d'insa yana jira Afnan tazo ta bud'e masa , yasan dai bata bacci sai ya dawo , sallamar da yaji ne ta katse masa tunaninsa , mijin Fatima ne ya mik'a masa hannu ."

    Bayan sun gaisa ya mik'a masa mukulli , cikin rashin fahimta Haisam yace ”wanan mukullin kamar na gidana ?"mijin Fatima ne yace ”eh shine mai d'akin naka ce tabawa Fatima tabaka , ran Haisam babu dad'i ya kar6i mukullin ya bud'e gidan , shi ko lura ma baiyi ba gidan da kwad'o sai yanzu ."

     Shiga da mashin d'in yayi ya ciro wayarsa a aljihu , ya danno lambar Afnan , jiyayi ance a kashe take , cikin tashin hankali ya bud'e parlorn ya shige bedroom d'insa , zama yayi a bakin katifar tasa cike da tunani , tun zamansu da Afnan bata ta6a tafiya anguwa bata sanar masa ba , to anya yau lafiya kuwa?" sai sak'e sak'e yakeyi a zuciyar sa , tun a hanya yakejin yunwa ,amma da yashigo yaga gidan babu gimbiyarshi yasashi ,jin komai ya ishe shi , ya had'e kai da gwuwai wa ."

      
*FARKON LABARI*
Afnan yarinya ce ga Alhaji Nasir , Alhaji Nasir yanada arzik'i dai dai gwar gwado , zuwa makkan shi sau biyu , yanada mata biyu , da Hajiya Zainab da Hajiya Wasila , Hajiya Zainab tanada yara biyu ,da Afnan da Salma ,Hajiya wasila nada yaro d'aya babba mai suna Usman ,duka yaran nasu sun girma kuma suna gidan aure , Alhaji Nasir yanada zafin rai sosai kuma ba kasafai yakeson ana kawo complain d'in yaransa ba , inhar kunason zaman lafiya dole kaso yaransa koda sunyi abin rashin kyautawa, kowace a cikinsu na k'ok'arin ganin sun kyautatawa y'ay'ansu ,amma baya gani , yanada wata yaya mai suna Anty Aisha , bata k'aunar matanshi ko kad'an ita kuma Allah bai ta6a bata aihuwa ba , ta tsani taga y'ay'an mutane , kuma a hakan tasami shiga , a gurin Alhaji Nasir ."

    Kuma shawarar ta tana aiki sosai , acikin y'a y'anshi Afnan ce bata auri mai kud'i ba , kasancewar batada hangen nesa , kuma Allah ne ya had'ata da Haisam , a gurin wani biki da sukaje  , shekaru uku da suka wuce , na k'awarta , yanayin kamun kanta yasa Haisam jin yana sonta , sun dad'e suna soyayya , kuma a soyayyarsu sunci karo da mahassada da makusa , kaf cikin dangin ,dadynta da Hajiya Zainab da Hajiya Wasila babu mai son auran , hakan yasa duk wuyar da takesha bata magana ,saboda  tasan babu mai temaka mata , wata k'awar mahaifiyarta mai suna anty Ummi 'itace mai zuwa gidanta ta kawo mata abubuwan da zasu amfaneta ,kuma take tambayarta matsalar ta ,itama Rana kai mata ziyara sosai bata d'aukar lokaci mai tsayi bataje ba,  Suna shiri da y'ay'an ta sosai kuma ziyartar junansu , wanan kenan ."

     Suna zuwa anguwar su Anty Umma ta sauka , Ciro kud'i a jakarta tayi ta mik'awa mai mashin ,tafara bubuga k'ofar , mai gadi ne ya fito yana washe baki , gaisawa sukayi Afnan ta shige ciki , direct parlorn da zai sadata da , Anty Ummi tayi ,parlor ne tsarare yasha kayan alatu komai na gidan a in burgewa ne , inka shiga parlorn kamar karka fito saboda wani k'amshi da keyiwa mutane sallama , Afnan ganin bataga Anty a parlor ba yasata wucewa bedroom d'inta ,samunta tayi tana waya, janyo akwatin nata tayi ta zauna a bakin gado, saboda bata ban banta Anty Ummi da mahaifiyarta ba , kasancewar bata nuna mata wani abu dazai 6ata mata rai , Anty na gama waya ta zauna a bakin gadon kusada Afnan , idanun Afnan sun ciciko da hawaye ta kifa kanta a cinyar Anty , mamaki ne ya kama anty ganin akwati a gefe kuma ga Afnan na kuka ."

     Anty ce ta d'agowa Afnan kai tare da jero mata tambayoyi , meyafaru mai Haisam d'in yayi miki ?kodai mahaifiyar tasa ce? "babu tambayar da Afnan ta amsa sabida kuka yaci k'arfinta ,cikin tausayawa anty ke kallonta tana girgiza kai , Anty ce ta shiga toilet ta had'a mata ruwan zafi ,ta bud'e mata sabon brush da man goge baki , ta  tara mata ruwa a bahon wanka ....✍️.

Idan naga comments zan cigaba ,saboda kune na maidashi free , rashin sharhi zaisa ya zamo na kud'i🤙.

LAMARIN ƘADDARAR AURENAWhere stories live. Discover now