002...

28 5 1
                                    

🧛🏻‍♀️🧛🏻‍♂️🧛🏻‍♀️🧛🏻‍♂️

       *TASHAR MAYU*
                       _*©®2022*_
  
                      🧛🏻‍♂️🧛🏻‍♀️🧛🏻‍♂️🧛🏻‍♀️
*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*
      _Kungiya d'aya tamkar da dubu._

*Story/Written*
_Abdull Alhaji Musa_
      _*Ft*_
_Meen@t A 'Yadoma_

_____________________________________
*NOTE*: _Bamu Yadda wani ko wata su juya wannan littafi ta kowace siga ba_
_____________________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK💯✅* 😂😂
*_22th-Jun-2022_*

002......
....Ganin tamkar basu san da yana magana ba yasa shi sake maimaita "ƙauyen Gangare zan sauka."
Yanzu ma a banza domin da alamu fasinjojin cikin motar tamkar basu ganin shi.

Tsoro gami da falgaba ne suka mamaye zuciyar shi, nan fa ido ya rena fata wata zufa ce ta cigaba da wanke mashi jiki.

Mutane biyun nan daya tarar harkan gaban su suke sam basu damu dashi ba,a sassan kare suke ko motsin kirki basu yi yadda kasan gumaka haka suka kasance na tsawo wannan tafiya da sukayi.

Ƙarar parking da akayi ne ta sanya shi sauke ajiyar zuciya, tare da saka ƙafa ya fita daga motar, tabbas da ya san abinda zai tarar bazai yi gigin barin motar ba.

Tozali yayi da cincirindon mutane da jikinsu ya kasance jajayen kayane kansu rufe yake da jar hula ta jikin rigar ta yadda ba zaka iya shaida fuskokin su ba, wata Red ɗin wuta ce mai sanfurin ball dake ci Babu kakkautawa suke kewayewa suna wasu surutai da sauri_sauri.

Firgici da tashin hankali sune suka yima zuciyarshi dirar mikiya ganin inda ya tsinci kanshi babu zato bare kuma tsammani.

Tamkar waɗan da aka tsaida haka suka dakata da kewaya wannan zagayayyar wuta mai samfurin Ball, cikin ƙaraji suka furta wata kalma da sauri da sauri.

Ganin Red ɗin wutar ya tashi sama yayinda tsartsatsin wuta ke zubewa yasa waƴennan mutane masu sanye da jajayen kaya suka sauka kasa suna mai yiwa wannan wuta *sujjada* hade kuma da furta wasu kalmomi cikin kara,Junaid ko daya kasance a wannan guri baima san lokacin da mutanen nan suka aikata hakan ba domin kuwa wangale baki yayi yana bin wannan wuta da ido.
Wutan sai data kai tololuwa sama kafin nan ta rabe gida_gida tare da sauyawa daga samfurin ball izuwa kawunan kwarangwal, launin wutan kuwa ta dawo baki kirin.

Juyawar wannan wuta izuwa samfurin kawunan kwarangwal suna kuma shawagi a sararin samaniya yayi matukar razana Junaid wanda hakan ta saka shi jada baya,aikuwa taku daya dayayi da bayan sai ta bada sauti kamar ya taka wani abun,kafin Junaid ya duba inda yasa ƙafan nasa ya kuma komar da ganin nasa kan wannan hatsabiban abubuwa dake shawagi kuwa sai yaga wannan wuta da suka kasance cikin samfurin kawunan kwarangwal sun yiyo kansa kafin yayi wani yunƙuri sai jin yayi wutar ta ratsa ƙirjinshi tare da shigewa jikinshi, tangal_tangal yayi kamar zai faɗi ba shiri yayi saurin sanya hannunshi tare da dafe ƙirjin shi, wata sumar tsaye yayi ta wucin gadi idanunshi suka rufe komi na jikinshi ya daina aiki na wani lokaci.

Buɗe idon da zai yi sai ya tarar babu taron mutanen nan sannan kuma babu wannan wuta,juyawar da zaiyi sai yaga mutanen na shigewa cikin motar, sannan ba iyakan mota daya zo a cikin bane ɗaruruwan motoci ne a gurin yayinda mutane ke kokarin shigewa,ganin motar tasu ta kusa dashi ne yasaka shi shigewa ciki domin kar'a tafi a kyaleshi nan gurin da baisan ko ina bane.

Cikin motar ya shige cike da al'ajabin wannan al'amari, sannan kuma ya sake cikewa da mamaki ganin wannan mota itace wanda yazo a ciki kuma mutanen nan sune suka zo tare amma kuma yanayin kayan dake jikinsu ta sauya..... kaf cikin motar babu wanda ke wata magana ko wani kwakkwaran motsi kowa kanshi duƙe yake ƙasa hular rigar jikinshi ta rufe mashi rabin fuska,wato hular sauka tayi ta rufe musu idanu da kuma rabin hanci illa bakin su ake iyya gani.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 30, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

TASHAR MAYU....Where stories live. Discover now