Hadiza bata ji labarin rasuwan Hamza ba sai kashe gari da safe. Kuka sosai tayi dan a cikin yaran Yaburra shine dan dama dama. In aka cira aiki da yike yawan sa su shi be cika musu ihu koh ya dake su ba. Hasalima shi wasu lokutan ya kan siyo abu ya basu a sace ba tare da Yaburra ta sani ba koh kuma ya basu kudi yace su boye. Sai zuwa azahar Fusam ta zo tayi murnan ganin Hadiza ta qara samun sauki, karayar da ta samu a wurare har uku ne dama sai an dan dau lokaci kan su warke. Ribs dinta sun karye, sannan hannunta daya ya karye da kuma qaramar yatsar hannun hagun ta.

Rungumar juna suka yi da Fusam, sunyi kukan murna sunyi dariyar farin ciki. Fusam ta nunawa Hadiza farin cikin ta akan auran da tayi ita kuma Hadiza ta qara qarfafa mata cewar In Shaa Allah Ibrahim da mahaifin sa zasu yi iya kokarin su dan ganin Haji Modu ya yarda Fusam din ta dawo hannun Hadiza da zama. Murna ya gama lullube Fusam. Sai da ta ci abinci ta qoshi tukum ta fara ba su Daada labarin abunda Shatu ta dinga fadi da yadda ta dinga yin abu kamar wadda ta fara sabon hauka. Duka suka yi Allah ya kyauta da kuma tir da hali irin na Yaburra.

Normal rayuwa ya cigaba bayan auran Hadiza da kuma rasuwar Hamza. Ana sati guda daidai da bikin sauran yan uwan Maryama suka koma Yola aka bar Daada wadda ke jinyar Hadiza dan tana asibiti har zuwa wannan lokacin. Fusam kuwa tana zaune gidan ubanta sai dai Yaburra tana fama da rashin dan ta bata koh shiga sabgar ta. Suma gefen su Ibrahim normal abubuwa suka cigaba da tafia, yan biki sun watse. Ibrahim yayi hutun sati guda kan ya koma bakin aikin sa, zuwa lokacin yana gab da gama bautar qasar sa. Ba ranar da baya zuwa asibiti duba Hadiza, most times ma so biyu yike zuwa; da safe ya ga ya suka kwana sannan ya koma da yamma ya sha zaman sa har sai ya fara jin barci koh ita Hadizan ta fara jin barci tukun ya musu sallama ya koma. Kusancin su nata qaruwa kadan da kadan.

Sati biyu daidai Hadiza tayi a asibiti aka sallame ta aka ce mata sauran jinyar a gida zata qarasa shi har ta fara amfani da hannunta. Nan da nan su Baba Azumi suka yi shawara da Daada cewar zasu maido da ita nan gidan nasu a cigaba da jinya har ta gama samun sauki kan ayi maganar tarewa. Sosai Daada tayi na'am da shawarar tace zata qara zama da Hadiza kan ta koma Yola. Abunda basu sani ba shine Ibrahim already yayi nasa shirin tare da mahaifan sa. Sai ranar da aka yi sallaman suka zo Hajia Falmata ta gabatar musu da nasu qudurin.

"Tunda dai yanzu anyi aure. Yarinya ta dawo amanar mu, tana karkashin kulawar Ibrahim hakan din ya sa muke ganin jinyar ma mu ya kamata muyi. Kunyi iya kokarin ku yan sati biyun nan muma dan Allah ku bamu damu nuna kalar namu kulawar akan ta. Ibrahim kuma ya fara sauke nauyin da Allah ya rataya yanzu a wuyar sa". Hajia Falmata ta fadi. Sosai kowa aka yi na'am da shawarar surukan Hadiza na tafia nasu gidan da ita har zuwa sanda zata sama sauki ta tare a nata gidan. Ganin yanzu Ibrahim din ya fi su iko da Hadiza ya sa ba yadda suka yi suka amince dan haka a yammacin ranar Ibrahim yaje ya dauko su ya dawo da su gida. Maraba sosai aka yi da ganin su, aka yi musu tarba na mutunci. Daki guda musamman aka shirya a cikin gidan dan dawowar Hadiza gidan. Satin su daya da dawowa daga asibiti Daada ta kintsa ta koma Yola. Ranar su Hadiza da Fusam da ta zo mata sallama sun sha kuka. Alkawari Daada ta musu cewar in an kwana biyu zata dawo ta duba su. Itama Hadizan tace in ta sama lafia zata zo ganin su, musamman kakarta da ta dade bata gan ta ba.

Ibrahim ne ya dauke ta ya kaita tashar mota suka mata sha tara na arziki. Suna tafia a mota tana qara sa masa albarka tana basa shawarwari. Godia sosai ya mata ya mata fatan alkhairi.

Yaburra tunda aka yi auran har Hadiza ta gama zaman ta a asibiti bata taka qafarta taje dubata ba, a cewar ta itama tana makokin mutuwar dan ta.

Wato irin sabuwar rayuwa Hadiza ta fara a gidan surukan ta tun bata sakin jiki da su har ta fara sabawa dan sosai suka karbe ta. Sosai suke nuna mata kulawa, kannen sa suna tarairayar ta dan cikin qanqanin lokaci ita da kanwar shi wadda suke kai daya har sun zama kawaye kullum tare suke, Hansatu tana zuwa dakin da take dan taya ta zama ta debe mata kewa tunda bata futa koh ina bayan tafiyar Daada ma dakin ta dawo da kwana dan basa barin Hadizan ita daya sabida cikin dare tana iya buqatar abu gashi hannunta a karye. Shima Ibrahim wani irin sudden change yan gidan suka gani a wurin shi, zuwan Hadiza ya futo da wani side of him da basu taba gani ba. The side that loved to play a lot and loved to smile a lot. Sosai hakan yikewa mahaifiyar sa harma da kannin sa dadi. Ba kunya yike nunawa Hadiza matsanacin so da kulawa dan in dai ya dawo daga aiki straight dakin ta yike wucewa nan yike zama ya ci abinci, yayi komi a can. Weekend da ya tashi yike shigowa sai dare. Tun Hadiza na kunya kunya har ta fara sakin jiki sosai da shi dan lokuta da yawa zaka jiyo kawai sautin muryoyin su suna hira suna dariya duk da mostly Ibrahim ne ke hirar Hadiza na sauraron sa. Hankali da nutsuwar Hadiza ya sa kowa a gida ke qara son ta. Sosai Hajia Falmata ke nuna mata kulawa dan har ta wanka ita ke taimaka mata wurin yi, cin abinci da komi sai an taimakawa Hadiza amma haka nan basa gajiyawa da yi mata hidima. Tamkar diya Hajia Falmata ta dau Hadiza.

Duk ranakun zuwa asibitin ta kuwa kashe zuwa aiki da duk wani abu da zai yi ranar Ibrahim yike yi ya kai ta da kansa a duba lafiyar ta kan su dawo gida. Fusam ma a duk sanda ta dan sama dama musamman in tana dawowa daga makaranta tana biyawa ta duba Hadiza kan ta wuce gida. Hankulan su a kwance.

Wataran da tazo ne take ba Hadiza labarin wani yaron aminin Baba da ya zo daga can garin Yobe dan zama da su. Labarin sa Fusam ta bawa Hadiza da Hansatu duka tausayin sa ya kama su. Baakura ya rasa iyayen sa duka cikin kwana ashirin. Mahaifin sa ya fara rasuwa kan mahaifiyar sa ta bi baya. Rashin madogara ya sa ya taho har garin Borno da tambaya har ya gane gidan aminin mahaifin sa Haji Modu. Yana zuwa Baba yayi maraba da shi ya sa aka bashi dakin Hamza yace a nan gidan zai zauna shi ya dau nauyin riqe sa sabida shi daya tal abokinsa ya haifa kuma sosai a baya wannan abokin ya taimakawa Haji Modu a lokacin da yike buqatar taimakon sosai.

Ya kuma ji dadi dan duk shekarun da suka dauka not in touch sabida yadda suka zo sukayi loosing contact, abokinsa be mance shi ba tunda har yana bawa dan sa labarin sa wanda har ya sa yaron tasowa zuwa neman sa. Dole ma ya riqe masa dan sa duk da hakan be wa Yaburra dadi ba.

End Of Chapter 🎊🎉

Hello people ya muke duka. Hope we're still enjoying the story.

Don't forget to bombard me with votes and comments. They keep me going😥😫

Lawh-Al-MahfouzWhere stories live. Discover now