Gumi kowannensu keyi duk da sanyi da akeyi a wannan safiyar. Wasu jikinsu har kakkarwa yake yi tsabar tsoro da tsananin firgici. Wata dattijuwar Mata ce Sanye da hijabi wanda hakan ya nuna cewa ga dukkan alamu musulma ce ta fara takowa ta ajiye lalitarta a gabanshi. Ɗagowa tayi bayan ta ajiye ta kalleshi tana mai cewa "Kuna ɗaukar Duniya wurin zama yayin da mutuwa a kowace sa a ƙara kusantar take. Kuna ɗaukar cewa Dukiya shine jindaɗin Rayuwa ba tare da tunanin irin fitinar da ke cikinta ba. Yaro wallahi kasani, kowani kobo kasamu sai Allah ya tambayeka yanda akayi ka sameshi, ko wane rai ka kashe sai kunyi shari'a a gaban Allah. Kuma duk tuban da zakayi nan gaba Allah bazai taɓa yafe maka haƙƙin mutanen da ka zalunta ba..."
Kuka ne ya ƙwace ma ta, cikin kukan ta cigaba da cewa "Azzalumai! Macuta! Mugaye! Iyayenku sunyi asaran naƙudarku! Wallahi ƙarshenku bazai yi kyau ba! Allah ya..."
Sauran maganar kasa fitowa yayi sakamakon fasa ma ta kai da ɗaya daga cikin ƴan fashin yayi da bindigarsa, take ta faɗi ƙasa matacciya jininta na malala akan titin. Saka kuka ɗaya daga cikin Matan tayi ta zo da gudu tana jijjigata tana cewa "Ki tashi dan Allah mama, kada ki mutu ki barmu. Ki tashi mama, dan Allah ki tashi..."

Bata ƙarasa faɗar abinda take so ba taji kyakkyawan mari akan kuncinta. Dafe kuncinta tayi tare da sakin wani irin rikitaccen ƙara ta soma ƙoƙarin sulalewa ƙasa. Saurin riƙota wanda ya maretan yayi tare da ƙara kifa ma ta wani marin. A take ta tureshi da ƙarfi daga riƙon da yayi ma ta tana mai kifa mishi marin shima. Cikin ƙaraji da dakewa ta shiga cewa "Allah ya tsine muku Albarka! Allah ya ruguza ku ya munana ƙarshenku! Ya sa kuyi mutuwar wulaƙanci da ƙasƙanci!"

Runtse idanunsa yayi domin marin ya shigesa sosai ba kaɗan ba duk da cewa fuskarsa a rufe take. Gudu ta soma yi sosai yayinda biyu daga cikin Maza matafiya suka bi bayanta suma.

2Pac ne ya bisu da gudu ya harbesu su ukun take suka mutu. Sauran mutanen da suka rage kuwa sosai suke sharce zufa wani na tsatstsafowa. Drivern kam sosai ya firgita, saboda tsananin firgici ma sai da ya saki fitsari a wandonsa ba tare da ya sani ba.

"Mutuwa ita ce mokamar duk wanda yayi gardama. Oya!, kowa ya zazzage Aljihunshi ya kawo abinda ya mallaka"

Ɗayan bayan ɗaya suka  fara kawowa suna ajiyewa, duk wanda ya ajiye kuwa akwai wanda zai cajeshi tsaf domin ganin ko akwai abinda ya ɓoye. Ana zuwa kan wata Budurwa taje ta ajiye, tana juyowa zata koma inda dukka pasinjojin ke tsaye 2Pac ya daka mata tsawa "Zakije a cajeki ko sai na fasa miki kai da bindiga?!"

"Dan Allah kuyi hanƙuri...Wallahi ban ɓoye komai ba" ta faɗa cikin yanayi na tsananin firgici da tsoro tana mai haɗe hannayenta biyu alamar roƙo.

Fincikota 2Pac yayi ya fara taɓa ta da sunan cajeta. Fasa kuka tayi wanda hakan ya sa ya ɗago tare da ma ta wani irin dangerous look wanda ya sanya ƙirjinta bugawa. Take sautin kukan ya tsaya amma hawaye basu daina zarya akan kumatunta ba. Cigaba yayi da taɓata har ya kawo kan breast ɗinta, runtse idanuwanta tayi yayin da hawaye ke gudu tamkar kogin da yayi ambaliya akan fuskanta. Foldling ɗinsu yayi a little bit, sensing the sensation of the act beginning to create a sense of humour all over his body (My stupid English😁). Dukka sauran ƴan fashin wani irin yanayi suka shiga mai wuyar fassarawa, yayin da sauran pasinjojin ke gefe wasu daga ciki na haɗa gumi, wasu kuma na zubar da ƙwalla.

Suddenly, Harbe harben bindigu ne ya karaɗe wurin. Da sauri 2pac ya saki yarinyar, da gudu duka ƴan fashin suka nufi cikin dajin, amma sunyi jinkiri domin take aka zubar da mutane huɗu murus basa ko motsi acikin su. Saukowa duka Sojojin sukayi daga Hilux ɗin suka nausa da gudu cikin dajin suka bi bayansu....

********************

Tunowa yayi da goran ruwa da aka basu suyi testing yayin da kamfanin ke neman yin bikin buɗewa kuma suke son rajista da NAFDAC wanda hakan yasa kamfanin suka gayyaci gwamna garin ABUJA buɗewa sakamakon branch ɗinsu da suka gina a faɗin jihar ta KATSINA. Tare da Gwamna suka je da shi, kuma saboda ba a mota ɗaya suka je ba ya sanya aka sa mishi nashi daban acikin Motar har katon biyar. Mantawa yayi ya bada umarni a shigar mai dasu a wannan ranar saboda yanda ya dawo a matuƙar gajiye.

Da sauri ya buɗe boot ɗin Motar, aikuwa tabbas ruwan na nan har yanzu. Ɗaukan gora biyu yayi daga ciki ya rufe boot ɗin ya zo ya buɗe bonnet ɗin ya sa ruwan, yana gama sawa ya buɗe Motar yayi ma ta key ya cinnata kan titin da gudu. Gudu yakeyi Sosai akan titi har ya zo wucewa ta wurin da akayi fashin, mamaki ne ya kamasa sakamakon ya san cewa yau babu sojoji akan hanyar amma kuma ya ga Hilux ɗin Sojoji a fake a gefen hanyar. Baiji ɗar ba ya cigaba da gudu akan titin still har yanzu zuciyarsa ta kasa tsayuwa akan abu guda duk da cewa ɓangaren da yafi ganin cewa idan yayi aikin saɓon zai samu abinda ya keso ya fi ƙarfi.

Awa uku cif yana sharara gudu ya isa SABON GARI, slow down yayi. Yana kallon gefe da gefen hanyan yana jin matsanancin faɗuwar gaba. Yana isowa gurin wani kango zuciyarsa ta tsananta bugawa. Shiga yayi cikin layin da ke gefen gidan ya faka Motar ta sa haɗi da fitowa. Jingina da Motar yayi ya runtse idanunsa yana sauraron yadda zuciyarsa ke faman bugawa tamkar zata fasa ƙirjinsa ta fito.

Sosai Zuciyarsa ke gargaɗinsa amma wata zuciyar kuwa ƙara ingizasa takeyi. Waigawa yayi yaga yadda tsirarun mutane ke shawagi akan hanyar. Nufar kangon yayi bayan ya tabbatar ya saci ido baya tunanin akwai wadda ya ganshi. Shigarshi ke da wuya idanunshi suka sauka akan wani yaro yana bacci a ƙasa. Wani irin bugawa zuciyarsa tayi sakamakon yadda yaji wani iri acikin jikinshi a lokacin da ya kalli yaron. Fari ne sol da shi tamkar ɗan Fulani, munshari yake yi yayin da fuskarsa take a kyaɓe da busassun hawaye wanda ya alamta irin kukan da yayi.

Kusanto shi yayi ya ɗan bugi kaɗarsa ya na so ya tashe shi. Juyi yayi wanda hakan ya sanya wandon da ya sa kasancewar yayi masa yawa ya bashi damar bayyana kusan rabin fatar ɗuwawunsa a waje. Runtse idanuwansa yayi saboda yadda yaji wani iri a jikinsa. Ƙara dukan shi yayi a baya wanda hakan ya yi nasarar farkawarshi daga bacci yana mai buɗe idanunshi a hankali.

Dishi dishi ya soma gani wanda ina ganin hakan ya samo asali ne sakamakon rashin cin abincin da baiyi ba. Sai kuma ganinshi ya fara dawowa dai dai har idanunshi suka sauka akan fuskar mutumin da ke tsaye akanshi. Take yaji wani mummunar faɗuwar gaba haɗe da tsoron mutumin wanda bai san mai yasa ba.

Tashi yayi zaune da ƙyar, tsamin da jikinshi yaji yayi sosai ne ya sanya shi tariyo abinda ya faru ɗazun da safe. Hawayene suka soma sintiri akan fuskarsa. Yanzu shikenan shi bazai taɓa yin rayuwa irin wanda sauran yara kamar shi sukeyi ba?. Yanzu shikenan shi bazai je makarantar boko ba?. Bazai karanta Al Qur'ani kamar yadda Malam Uzairu yake karantawa ba?. Ba zai ci abinci ya sa kaya a kula da shi shima kamar yadda yaga ana yiwa sauran yara ba?. Goge hawayensa yayi ya dafe bango yana ƙoƙarin tashi tsaye. Yana tashi ya jingina da bango, hannunshi ya kai kan fuskarshi ya sake goge hawayen da suka kasa daina kwarara.

Duk abin da yake yi yana tsaye yana kallonshi. Zuciyarshi cike take taf da tarin tausayinshi. Anya zan iya aikata abinda zuciyata ke umartata kuwa?.

"Idan ka jinkirta kuwa, kai da samun wannan kujera har Abada!"

Maganar Boka ce ta saukar mai a ƙwalƙwalwa Wanda hakan ya sanyashi nufar yaron...


































IDAN HAR KUNSAN CEWA KUNA JINDAƊIN WANNAN LITTAFIN, KU NUNA MIN ONE LOVE TA HANYAR YIMIN SHARING, VOTE DA KUMA COMMENT DOMIN SHINE ZAI ƘARA ƘARFAFA MIN GWIWA KUGA INA MUKU UPDATE AKAI AKAI BA TARE DA GAJIWA BA.....

Naku har kullum, Forever REAL❤!

Alƙalamin real__ahmerd✍️

#VOTE
#COMMENT
#SHARE
#FOLLOW

IMRANWhere stories live. Discover now