"Kinga saurara, da na yanke hukuncin Auren nan, seda naji ta bakin Imran kan ayi Auren nan, kuma zanje gidan zanji abunda yake faruwa, da kaina inga akwai yiwuwar raba musu gidan, ina son Imran yai zama me adalci a tsakaninsu shiyasa na haɗasu, amma zanje Gidan da kaina"

Gabanta ya ɗan faɗi bayan tayi tunanin idan ya samu labarin taje Gidan taci mutuncin Amira fa? Lallai ita ma se nata ran ya ɓaci.

Da sauri tace "Amma ai da ba se kaje ba, kawai dai na gaya maka ne kasan hukuncin da ya dace ka ɗauka, kuma ai be kamata a bar Ihsan ita kaɗai ba, tunda lokacin da ya tafi da Ihsan ita Amiran ba ta gidan"

"Nifa na gama yanke hukuncin da naga ya dace dan haka ki rabu dani"

Yai Maganar tare da miƙewa ya bar mata falon nasa gaba ɗaya ta raka bayansa da uwar harara.

Ammi ɗakinta ta koma, ta ciro wayarta ta kira Ihsan, Ihsan na ɗagawa Ammi tace "ke wai kina ina ne?"

"Ina nan Ammi, meya faru ne?"

"Kina nan a ina, yau mijinki ze dawo, suka tafi da waccan shashashar gurin taro shi, ke ba kya nan, muka biya muka ajesu a gidan su, nan ma ba kya nan, ke wace irin mara wayoce ne haka?"

"Au Ammi dama yau ze dawo? Ai ni babu wanda ya gayamin fa, Yanzu yana ina?"

"Ke kina zaune harse an gayamiki, ita ya a kai ta sani? To ki hanzarta ki tafi gidan, dan kin bari ta fara tararsa, Allah ya kiyaye dai amma ki hanzarta ki koma ki karɓi mijinki"

"To Ammi Insha Allah"

Ihsan ta katse wayar tace "Kai, taɓɗijan, Lallai banga ta zama ba, ta shiga harhaɗa jakarta zata koma gida.

Sosai bacci ya kwashe Imran, lokaci lokaci Amira ta kan leƙo ta duba taga yana lafiya, sannan ta koma ɗakinta.

Ƙarshe ta dawo falon ta zauna, tana karatun littafi a wayarta.

Se azahar ya tashi daga baccin, ya cewa Amira zeje masallaci, seda ya fita Sannan maƙotansa suka san ya dawo, a nan suka gaggaisa suka masa Barka da zuwa, tare da yi masa barka da arziki.

Ya koma gida ya tarar har Amira ta ajiye masa Abincin Rana, ya nemi Guri ya zauna akan kujera ya lumshe idonsa.

Ƙarar buɗe ƙofar Amira ne ya sa shi buɗe ido ya kalli inda take, crazy jeans ta saka, da wata fitinanniyar riga, attachment ɗin nan har ƙugunta, kamar za tayi rawar galar, hannunta riƙe da ƙaton robar popcorn.

"Captain ka dawo? Ga Abinci fa"

Seda Imran ya ɗan shagala da kallonta, can ya dawo hayyacinsa amma bece Komai ba.

Kusa da shi Amira taje ta zauna tace "wai ko wani abun yana damunka ne?"

Girgiza mata kai yai alamar a'a.

"To sakko kaci Abincin, in dai Ihsan ce ta kusa dawowa tana gurin aiki ne, nasan tunaninta kake"

Da sauri Imran ya kalleta, itama ta ƙureshi da ido, babu ko ƙiftawa, zuciyarsa ta shiga bugawa da saurin gaske, a jere ya dinga ajiyar zuciya, ya miƙe ya zauna a ƙasa, ta zuba masa Abinci.

Ya miƙe ƙafa yaci abunsa, dan ba ƙarya Amira ta iya girki, sedai yana ci yana satar kallon Amira, duk da ta rame amma kayan sun mata kyau sosai, sun zauna a jikinta.

Ta maida hankali tana kallon TV kamar ba ta san yana kallonta ba, seda ya gama yace
"Am done, zoki kwashe kwanukan"

Maimakon ta amsa, juyowa tai da Wani irin kallo, ta ɗan lunshe idanunta, seda Imran ya ɗan dirirce, cikin rangwaɗa ta zo gabansa ta kwashe kwanukan, ta dawo falon ta zauna, ta kalleshi tace "ko kana buƙatar wani abun ne?"

WUTA A MASAƘAUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum