PAGE ONE

71 4 0
                                    

🌺🌺🌺
*SOYAYYA CE SILA* 🪦🪦

                     *BY*
          *Oum Sumayya*
                       *&*
                *Oum Ikram*

*HONESTY WRITER'S*
*ASSO...✍🏽*

https://chat.whatsapp.com/GIbpPjFSqZU13mClanPXP0

    بسم الله الرحمن الرحيم

             *SHIMFID'A*

*Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allan subhanahu wata'alah mai rahama maijin k'ai,  tsira da amincin Allah su k'ara tabbata ga cika makin annabawa, annabin mu Muhammad s.a.w*

*Ya Allah yanda zamu fara wannan littafi lafiya Allah kasa mugama lafiya bisa aminci da yarjewar ka!*

                  *GARGAD'I!*

*Wannan littafi hakk'in mallakar mune bamu yarda wani ko wata yajuya mana shi tako wace siga bada izinin muba*

                  *AKIYAYE*

*Ina sake rok'on ku sisters Aunty's Mommy's dan Allah inkin san zaki zagemu ne to kawai karki karanta littafin domin daidan wani karkatan wani dan gaskiya duk wacce tazage mu to... Allah dai yakyauta mugudu tare mutsira tare*

               *GAISUWAR TAKU CE*

*Bazamu gaji da mik'o gaisiwa gareku ba masoyan mu masu k'aunar mu da gaskiya masu son mu tun daga cikin k'albin su alkairin Allah yacimmuku aduk inda kuke muna sonku fiye da yanda baki bazai iya furtawa ba domin da bazar ku muke rawa!*

                    *🆓PAGE* 
                        🅿️1️⃣

         *KADUNA STATE*
            *RAFIN GUZA*
                    (5:48pm)

Yammaci ne lis dan ana gab da kiran sallar magrib,
Iskane mai dad'in gaske ke kad'awa agari kasantuwar muna farkon damuna anyi ruwa yad'auke sai iska da sanyi masu dad'i dan basuyi yawa ba domin dai yau ankwallara rana garin akazo akayi ruwan sama hakan yasa garin baiyi wani sanyi sosai ba saima zafi zafi da yake d'an tasowa,  motoci da mashina ne keta kai kawo abisa d'an k'aramin titin daya shiga layin da babu kwalta aciki sai jan k'asa ga ramuka layin duk yabi yadame,  kowa ka gani burin sa ya isa makwancin sa hatta da tsuntsaye suma sauri suke su isa makwancin su,
Ahankali yake driving kamar baya son kaiwa inda zaije wak'ar omoh lay ne me taken am beginning to fall in love itace ke tashi acikin motan yanabi kamar shi yarerata yana sanye da kayan sojoji na Nigerian air force blue black da sukai matuk'ar amsan farar fatar shi fari ne sosai kallo d'aya zakai mai kagane yahad'a jini da fulani yana da idanu y'an madaidaita da zara zaran eyes lashes kamar yy k'ari sai dogon hancin sa da d'an madaidai cin bakin sa da yadace da cute face d'in shi daga gefen rigar shi naga ansa *Suleiman M* d'ayan gefen kuma ansa Nigeria air force daga k'asa kuma anzana mai rank d'in shi da bak'in abu two star hakan yabani tabbacin yanada matsayin shi a aikin sojan,  idanun shi ya lumshe yana bud'e su daidai kwanan dazata sada shi da layin nasu tundaga nesa yahango su tsaki yaja yana fad'in "Village girls kawai any time jiki arufe ko zufa baya damun su ninja lady" wani irin malalacin murmushi yasaki at the same time yanajan tsaki gudu yak'ara ma motan.

Y'an mata biyu ne ketafe daga gefen titin dukkanin su fuskokin su rufe da nik'ab jikin su sanye da uniform milk color hijaban su har k'asa safar hannu data k'afa da alamu dai daga islamiya suka taso, kai tsaye bazaka kirasu dogaye ba sannan bazaka sasu sahun gajeru ba,  cike da natsuwa suke tafiya suna fira atsakanin su jefe jefe,
D'aya ne takalli d'ayan tace "Munaihat kinga garin nan kamar wani ruwan za'a kuma yifa"
D'ayan ne takalli sararin samaniya da duhun magrib yafara shiga sannan gakuma jido nata had'uwa agabas da alamun wani ruwan na nan tafe murya asanyaye tace "Na'imah kenan mu mukai namu ikon balle kuma Allah s.w.a Allah yabamu mai albar...."
Maganar ta yatsaya ne cak saka makon wani irin abu dataji afuskarta da jikin ta dasauri tatare idanun ta tana k'ok'arin goge abunda taji acikin su gaba d'aya saida tagoge na idanun ta duk da tanajin alamun da saura dan idanun nata sai ruwa sukeyi sannan ta ankara dacewar irin cab'al b'alin nan nefa gaba d'aya itada Na'imah akai musu wanka dashi turus duk suka tsaya barin ma Na'imah data k'ure motar data watsa musu cab'al b'alin da idanu harta b'ace ma ganin ta,
Gaba d'aya sai sukaji sun muzanta ga abu milk mai nuna datti mazan dake zama bakin layin ne suke ta kus kus yayin da wasu ke dariya dan dama haushin sa nik'ab d'in dasukeyi ake take suka fara fad'in
"Nija lady how market ko kuna neman taimako ne is better kucire wannan tsumman daga fuskar ku saimu taimaka muku"
Jikin Munaihat na wani irin tsuma da kakkarwan b'acin rai taja hannun Na'imah suka sha wata kwana babu mai magana dan kam yau rai yab'aci ta lunguna lunguna sukabi har suka isa gida, gidan su d'aya suna shiga kowa rai ab'ace suka fad'a d'akin su batare da mgn ko slm ba duk da kasancewar gidan nasu na yawa amma basu cimma kowa atsakar gidan ba  alamun kowa na d'aki saboda magrib da ake gaf da kiranta,

Gaba d'aya hijaban nasu ya lalace barin ma na Munaihat dan gaban ya baci ga idanun ta dake ta fitar da ruwa dan cab'al-b'alin yashiga sosai,
Na'imah ne takalle ta cikin wani irin masha hurin b'acin rai tace
"Munaihat kinsan waye ya watsa mana cab'al-b'alin nan kuwa?"
Munaihat daketa goge idanun ta cikin hasala da takaici tace "ai wallahi kowaye bai kyauta mana ba yanzu kafun uniform d'in nan yafuta aiki ne gwamma kema Abban ku na iya sauya miki wani nikofa dak'yar na tara kud'in nan nasiya yanxu ta ina zan samu kud'in siyan wani?"
Tak'arisa maganar wani irin zazzafan hawaye na zubo mata,
Dafata Na'ima tayi tace "kiyi hak'uri"
Hawayen tashare cikin takaici tacire riga da wandon tasauya zuwa wasu riga da zani na atamfa dasuka sha jiki sosai,
Na'imah dai na kwance tana kallon ta ganin zata futa ne yasa tace "Baki tambayan waye ba?"
D'an b'ata cute black beauty face d'in ta tayi tana turo d'an madaidaicin bakin ta tace "ke harma kinga kowaye kenan mtsss wallahi danine nagan shi am sure saina d'auki dutse na rotsa glass d'in motar bansan meyasa masu mota keda care less akan wad'anda suke tafe ak'asa ba mtssss"
Kai kawai Na'imah takad'a cikin takaici tace "uhmm d'adi na dake saurin d'aukan d'umi daga magana to Mubasshir ne na bayan layi"
Wani irin juyowa tayi tana kallon Na'imah tace "are you sure?"
Kai tagyad'a cikin tabbatar wa,
Da sauri Munaihat tad'auki wani hijab green da duk yakod'e shima tasa tana fad'in "kan uban can wallahi yanxu nan zanje gidan su wulak'an cin nashi har yakai haka to yau zai san ya tab'o Fatima"
Da sauri Na'imah tamik'e tarik'e ta kam tana fad'in "calm down Munaihat kefa kinada matsala to inkinje kice mai mene kin san halin miskilancin sa yana iya yarfaki kita masifa ya manna miki hauka yy banza dake zauna kiji"
Tak'arisa maganar tana zaunar da ita abakin y'ar katifar su,
Dak'yar tazauna tana huci many'an idanun ta alumshe sai zara zaran eyes lashes d'in ta daketa motsi duk sun jik'e da hawayen dake futa daga idanun ta,
Kai kawai Na'imah ta kad'a tace "i know abunda yamana bai kyauta ba kuma tun ba yauba kin san yanda Mubasshir yatsane mu alayin nan musamman ma ke! amma kiyi hak'uri shi yak'i d'an zamba ne cikin aminci ake bin sa"
Fararen idanun ta dasuka fara canza launi zuwa ja tasauke kan Na'imah not knowing mezatace while tana gyad'a kanta kamar kadangare dak'yar tasauke wani irin numfashi daidai ana kiran magrib tazame hijab d'in tace "ohh ya Allah mena tsare ma wannan guy d'in nan alayin nan ga mata nan masu sa nikab dayawa amma ni yasamin idanu burin shi yatozarta ni burin shi intozarta amma ta Allah bata shiba and menene amfanin gayamin dakikai bayan kin san bazaki barni naje na kare mai tanaji ba? Any time idan yamana wani abun nace zan d'auki mataki saikice a'ah what's your plan? Yanzu kiduba yanda ruwa keta futa a idanuna duka biyun inajin kasa acikin su nagoge nagoge sunk'i fita amma kin hana ni fita haba Na'imah!"
Cike da tausayin ta tace "am so sory once again nasan koda kinje shine asama dan rashin gaskiya za'a bamu yana iya cewa bai ganmmu ba amma yanzu nagama yanke shawarar hukuncin dazamu yanke akan shi!"
Cikin takaicin ta tashare hawayen fuskasta tana kallon hijab d'in ta dako sati biyu baiyi da siye ba tace "bb wani hukuncin dazamu iya yi akanshi kawai zan sake had'ashi da Allah nasan zai saka min"

Murmushi Na'imah tayi kamun tace
"Kawo kunnen ki kiji yanda zamu jefa d'an iska akomar mu muwahalar dashi"

Ba musu takara mata kunne a setin bakin ta,
D'an zaro many'an eye ball's d'in tayi  jin abunda take cewa saikuma ta rausayar dakai tana d'an cije bakin ta tace "uhm M.D kashiga komar mu amma kina ganin bb matsala? "
Dariya Na'ima tayi tace "kinga idan mukabi haka asauk'ak'e zamu rama sannan zamu kawo k'arshen miskilancin sa da wulak'ancin daya sha yimana"
Dariya itama tayi tana mik'ewa ta fita daga d'akin dan zuwa d'akin Maman ta,  azaune tasame ta tanacin tuwo zama tayi tana mata sannu da gida sannan tamik'e tazubo tuwon itama tazauna tanaci Mama takalle ta anatse tace "Fatima!"
D'ago idanun ta tayi cike da mmkn sunan ta da Maman takira ta amsa da "na'am Mama!"
"Mun gama mgn da Aunty Zainab Mubarak zai zo wajen ki anjima"
Afirgice tamik'e tace "Mama kamar ya zai zo mezan mish..." Mgnn ya mak'ale mata abaki saka makon shigowar.......✍🏽

SOYAYYA CE SILAWhere stories live. Discover now