*HAZAƘA WRITERS ASSOCIATION*
KUNDIN AJALI
Na
MS Kutama
HAƘƘIN MALLAKA
Hazaƙa Writer's AssociationGODIYA
Ina miƙa godiya ga Allah Subhanahu wata ala da bani ikon fara rubuta wannan littafin , tsira da aminci su tabbata gurin fiyayyen halitta .
SADAUKARWA
Ga ƴar uwa marubuciya ;-
Sanah ShahadaUbangiji ya baki lafiya Albarkacin fiyayyen halitta .
Bismillahir Rahmanir Rahim
KUNDIN AJALIA wani zamani mai tsawo da ya shuɗe a cikin daular larabawa , Anyi wani ƙayataccen Birni mai suna madinatul lasamar .
Madinatul Lasamar na ƙarƙashin mulkin wani azzalumin sarki wanda suke wa laƙabi da fasa taro , wato sarki rauhul abraaz bin kashiful yamani , sadauki ne wanda ke dakawa maza gumba a filin daga , wanda duk faɗin nahiyar babu wanda ya kai shi .
a wannan lokaci duk faɗin duniya babu sarkin da ya kai shi ƙarfin mulki .
sarki rauhul abraaz bama talakawan shi kaɗai ba har manyan attajiran dake ƙarƙashin sa tsoron sa suke saboda tsantsar hatsabibancin sa da rashin imanin sa .
Sarakunan dake ƙarƙashin ƙasar sa biyayyar dole suke masa , don idan suka ƙi a take zai saka a kashe ka kuma a shafe ahalin ka , a maye gurbin ka da waninka wanda zai rinƙa yi masa biyayya da bin dokokin mulkin sa .
Isa da girman kai da Ji da mulkin sa ƙara iza wutar tsantsar zaluncin sa suke , domin a gaba ɗaya nahiyar babu wanda ya isa ya tanka masa .shekarun sa hamsin da biyar a duniya , yana ɗan shekara ashirin ya hau karagar madinatul Lasamar .
bai taɓa yin aure ba kuma bashi da burin yin hakan .
dalili kuwa shine tun kafun mahaifin sa sarki kashiful yamani ya rasu lokacin da aka haife sa bokaye suka tabbatar da duk ranar da aka ɗaura masa aure da wata mace ranar zata zamo ranar rushewar mulkin sa , daga lokacin ya rasa ƙima da darajar mulkin sa maƙiyan sa za su yi nasara akan sa .
wannan shine babban dalilin da yasa sarki rauhul abraaz ya tsani mace a rayuwar sa , babu abunda ke shiga tsakanin sa da ita face yayi mata fyaɗe kuma yasa a kashe ta .
a rayuwar sarki rauhul abraaz ya yiwa mata fyaɗe sunkai guda dubu biyu kuma duk wadda ya yiwa a take zai hallaka ta .
wannan mummunar ta'asa ta sarki rauhul abraaz ita tasa gaba ɗaya matan nahiyar suke tsoron ganin shi kuma suka tsane shi fiye da yadda suka tsani mutuwar su , domin kuwa da suna da ikon kawar dashi daga doron ƙasa da tuni sunyi hakan .bashi da imani ko adalci a cikin sha'anin mulkin sa , domin komai matsayin ka a masarautar sa matuƙar kayi laifi bai san wata kalma wai ita yafiya ba .
sarki rauhul abraaz mutum ne wanda babu wanda ya isa ya faɗa masa balle yayi masa karan tsaye a cikin mulkin sa .
a rayuwar sarki rauhul abraaz babu mutumin da ya zame masa ƙarfen ƙafa kamar yarima ansar bin kulaifa , yarima ansar yana zaune ne a wata ƙasa gabas da birnin madinatul lasamar .
jagorancin ƙasar yana ƙarƙashin mulkin ɗan uwan sa sarki Irfaan bin kulaifa .
gaba ɗaya al'ummar ƙasar ma'abota bautar rana ne shekarun sarki irfan ashirin da bakwai a duniya ya gaji sarautar ƙasar a wajen mahaifin su .
tsakanin sarki rauhul abraaz da sarki irfan gaba ce mai tsananin gaske domin a gaba ɗaya nahiyar wannan ƙasar ce kaɗai sarki rauhul abraaz ya kasa mallakar ta , domin tun zamanin mahaifin sa ba'a ga maciji tsakanin ƙasashen biyu , duk da cewa ƙasar madinatul lasamar ta tserewa ƙasar nurul hayawan ƙarfin mulki , yawan dakarun yaƙi da kuma ƙarfin sadaukantaka .
mahaifin su sarki irfan ya kasance jarumi ne wanda a gaba ɗaya nahiyar sarki rauhul abraaz ne kaɗai ya fishi ƙarfin damtse .
![](https://img.wattpad.com/cover/287662132-288-k679336.jpg)
BẠN ĐANG ĐỌC
KUNDIN AJALI
Phiêu lưuLabari ne akan wani Littafi wanda duk wanda ya samu damar mallakar sa zai juya duniya kuma ya zamo gagarabadau . amma sai dai dauko Littafin daidai yake da tunkarar Kofar mutuwa domin irin masifu da bala'oin dake tare da shi da kuma dazukan da za a...