Chapter Ten

1K 178 59
                                    

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Washegari!

NASSARAWA HOSPITAL
KANO

Zaune yake a waiting room din wuraren qarfe Goma na safe.

Bai dade da dawowa daga gida ba inda yayi wanka yayi breakfast... A yanzu haka Hafeez shima ya koma gida don yayi wanka yayi breakfast sannan su dawo tare da Mamy.

Sadiq dai aiki yake yi a macbook dinshi- aikin Bunza Oil & Gas. A gefe kuma I-pad dinshi ce yayi setting yadda zata dinga ganin fuskar shi yayinda suke hira..

A jiya dai sai da Hanan ta nace mishi ya bata labarin abinda ke faruwa.. Sossai ta tausaya ma Hanifa jin ta kwana a cell, dukda ta fahimci bata jin magana but still.. Yanzu haka roqon shi take yi akan ya kira ya ji ko an sake ta

"Chocopie gaskiya baka da human feelings, yanzu fisabilillah ka bar ta a cell sauro suna ta cizon ta?? wallahi I didn't sleep well jiya saboda tunanin halin da take ciki. Please call and confirm idan sunyi releasing dinta"

Yana dariya yace "sannu sarkin tausayi.. duk wulaqanta ni da tayi baki ga laifinta ba?? dagaske Hanan idan kika ga abinda yarinyar nan take yi zata baki haushi.. the sight of her alone disgusts me"

"Allah sarki, qila yarinta ce"

"what??? Yarinta?? I am sure ke da ita age mates ne, haka kike yi?? even Mini-Me thats way younger than her tana irin wawancin da take yi ne? please stop it.. she lacks discipline ne kawai.. Mahaifinta ne ma yake bani tausayi and if not for him I swear sai tayi kwana uku a cikin cell dinnan sannan ta fito.."

"whoa.. Chocopie wallahi kai mugu ne, how comes after all these years yanzu nake ganin this side of you???" ta fada cike da mamaki.

Murmushi kawai yayi yace "Ni ba mugu bane, just accept my proposal and marry me..you will see. I am the most simplest and easy going guy you will find around.."

"Inaaa, ai Chocopie kai gaba daya a dictionary dinka babu soyayya, ni kuma ka ga kowanne page na dictionary dina soyayya ce. ai kai irinka kawai zaka nema, someone with a stone heart wadda zaku zauna without feelings for eachother at all don kuwa idan ka auri macen da ita take sonka amma kai baka sonta I swear sai baqin ciki ya kashe ta.."

Sadiq wanda yake murmushi yace "Ya salaam Hanan.. is there anything I can say in my defence??"

"I doubt" ta fada tana hararar shi.

Dr. Mansoor ne ya shigo da sauri with two nurses trailing behind him.

Sadiq ya miqe yana fadin "lafiya??"

Dr Mansoor yana murmushi yace "he is awake and he looks good.. bari in duba shi tukun, afterwards you can see him"

"Alhamdulillah" Sadiq ya fada yayinda likitan tare da nurses dinshi suka shiga.

Komawa yayi ya zauna sannan ya dauki I-pad din yace "he is awake.. thank God"

"Masha Allah.. toh yanzu can you confirm idan sun sake ta, I believe mahaifin nata zai so ya gan ta now that he is awake.."

Aikuwa tun kafin ta qarasa magana suka jiyo masifa..

Hanifa dai da safen nan aka yi releasing dinta. kiran driver tayi ya zo ya dauke ta. Tana dawowa gida ne ta ji abinda ya faru wanda a dalilin rudewa da tayi ta kasa jiran Mamy ta kammala hada breakfast su je asibitin tare.. instantly tana yin wanka ta garzayo!

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now