XIX

937 183 10
                                    

UWARGIDAN BAHAUSHE

XIX (19)

✍️ Ayshatuuu 💚

Abu kamar Wasa kwata kwata Baba ya birkice ya canja ma Ammi gaba daya, Abu daya na fahimta dashi, tunda dole aka masa ya dawo da ita, to gashi ya dawo da ita taci uwar da zata ci. Ban taba jin hutu ya isheni ba kamar wannan hutun, naji na tsani komai musamman idan akace Friday tayi se naji bacin Rai nake, saboda nasan he'll be back treating her unfair. Ranar Muna zaune daga ni se Ammi a daki nace

" Ammi!"

Tace

" Ya akai?"

Nace

" Dama kiyi hakuri Ammi, Ina ganin kamar I don't have right na Fadi haka Amma me yasa Baba dake kuke fada. Na zata Kun shirya bayan Kun dawo"

Se tayi murmushi tare da mikewa ta shafan Kai tace

" Kada kiyi tunani da yawa, it's nothing"

Bata ma jira abinda Zan fada ba ta tafi. Nayi shiru Ina kallon yadda tayi murmushi ta fita, jikina Babu dadi na zauna tareda dafe kaina Ina ayyana yadda zanyi, to ya zanyi kuwan tunda iyayena Babu yadda zanyi dasu, da ace Zan iya da Baba Zan samu nayi maganar dashi. A hankali Kuma ranakun suka wuce har hutun ya Kare, Wanda idan muka koma Kuma bana tunanin zamu sake dawowa har se munyi graduation. A day to zamu tafi Ammi tayi bakuwa, Ammah ce tazo daga maiduguri, ita ce mahaifiyar Yaya Fahad. Ita dashi suka zo, Ina zaune na shimfida carpet ina koyawa Rayha construction na maths, se munyi mun Gama idan na samo Mata wani question din kan construction se tace wai ita Bata gane ba, na yaga paper nace

" Ammi Kinga Taki tsayawa ta koya ko?"

Ammi dake gefen mu tana ninke Kaya tace

" To tayi ta Wasa ai, idan akai tambayar a exams ta Fadi"

Ta Bata Rai ta karba set square hannuna ta fara kokarin pointing figures din, na tabe baki Ina lura da ita , Ashe iskanci ne kawai Dan ta wahalar dani, Bata Kai rabi muka ji sallamar Ammah, ta shigo sanye da lafaya tana ta kanshi, matar ta saje da zama da kanuri, dake min Jima bamu ganta ba yasa bamu wani santa ba, bayanta itada Yan Mata ne guda biyu kusan saanin mu dukda daya zata girme mu, Ammi na dagowa ta aje silk din hannunta tareda sakin murmushi tace

" Barka da zuwa. Sannun ku da zuwa"

Itama ta fadada fara'ar ta tace

" Maman Sofy kwana da yawa"

Ammi ta shiga dasu ciki muma se muka Mike muka rufa musu baya, tana kallon mu tace

" Mashaaa Allah ki kalla yadda su Sofy suka girma, banyi tunanin zatai tsayi ba fa"

Ammi tace

" Kinga Sofy nan, wannan Rayha ce"

Ta rike baki tana Murmushin da fadin mashaaa Allah, Ammi tace

" Ba ku santa ba?"

Na gyada kaina ni da Rayha, tace

" Maman Fahad ce!"

Na kalla Rayha Naga tayi saurin sunkuyar da kanta, nayi dariya sauran ma dariya sukai se muka fita zuwa dakin mu , babbar irin sunana ke gareta ana ce Mata Mami, se dayar Amira.

Yaya Mami tace

" Yaya Fahad tunda ya dawo kullum zancen ki yake, duk kin saka ya susuce"

Rayha tayi murmushi ni ce nace

" Itama haka, kullum zancen Yaya Fahad take"

Ta kaimin duka Amira tace

" Kai Yaya Sofy, she's too innocent for that"

Se Yaya Mami tace

" Waya fada Miki akwai anyone innocent akan soyayya? Bana tunanin akwai"

Munata Hira Ina Kara fahimtar Rayha ta gama saa ni ce na rage Kuma. A parlor na Gama kawo abinci da ruwa da lemon Dana bayar aka siyo, Suma na daki na hada Mana a tray kamar yadda yaya Mami yace.

" Mun Dade bamu hadu ba, Ina tunanin tun haihuwar Anisah rabo na dake"

Ammi tayi murmushi tace

" Aikuwa dai, ni kaina na manta karshe da na ganki"

Ta sauke ajiyar zuciya tace

" Fahad ya fada min, yace Yana son Rayha, da farko dai tun suna Yara na riga na dasa musu kiyayyar dangin mahaifin su, saboda duk yadda nake jin labarin wahalar da kika Sha tawa tafi Taki, Baban Fahad ya aureni ban Kai Sha biyar ba, Dan haka Gwoggo kadai ta Soni, ni lokacin da nayi aure da yawan su basuyi aure ba, Kuma anan gidan su na zauna, bani ba 'ya'yana ma Basu tsira ba, Naga wulakanci kala kala iri iri. Dalilin su yasa ya daukeni ya maida ni maiduguri shiyasa kikaga baki taba haihuwa nazo Miki barka ba, tunda na fahimci rayuwa shikenan na ce sun Gama min rashin mutunci, na fitar harkar su, ko Abu suke na daina zuwa Kuma 'ya'yana ma bazasu zo ba tunda ni na haife su, ba Wanda yayi min nakudar su, na Sha fada musu Babu Wanda ya Isa ya auro min wani daga Gumel, suje ga Yara nan a titi su aura Amma Banda auren cikin gida. Dangin Baban su Babu abinda Basu fada, na Hana Yara zumunci, ni tunda bazan zo ba su Ina turo su, Babu maganar da basuyi ba Amma na maida su banzaye, na nuna masu Basu Isa ba sunyi kadan, to Amma me yasa nayi winning saboda na nemi na kaina, na kafa kaina Ina sanaata, duk wani Hali da kike ciki na sani Kuma Ina hango wautar ki, ya kamata ki tashi kiyi Sanaa ki nema kudin ki, idan Babandi yazo kanshi idan Bai zo ba damuwar shi, dangin shi ki daina shiga sabgar su wallahi Ina tabbatar Miki se sun Mika wuya. Ita Kuma waccan matsiyaciyar da take tunanin ta gama dake, ki rabu da ita, Allah Bai hallatawa kanshi zalunci ga bayin shi ba, balle mu muyi. Allah zai bi maki hakkin ki, Amma Ina son yau ki canja zaman nan. Irin wannan Yana weakening yaran mu, musamman Mata, zasu ga kamar aure haka yake saboda haka suka ga anayi a gidan su, ko kuma suce Suma se sun muzgunawa Wanda suke tare dashi. Ya kamata ki tashi ki Zama strong not for him but for these lovely kids. A gurin Babandi bakida sauran martaba tunda ya iya dakko ki ya dawo dake nan, yanzun ba lokacin ya zaayi a gyara zaman ku bane, bazai gyaru ba mutum Bai Isa ya gyara ba, kiyi addua nasan Allah will not shun you! Amma ki nema naki, kiyi Sanaa tunda Bai barki kinyi karatu ba, idan yaso ni Kuma na Miki alkawarin I'll support you"

Ammi ta Yi ta kuka kamar dama jira take, an Sosa Mata inda yake Mata ciwo, ganin hakan Ammah ta Kama hannunta Suka koma bedroom dinta Dan kada muji, seda ta daina kukan sannan Ammah ta cigaba

" Ki daina kuka, duk wannan ki dauka a da ne. Nayi mamaki da Fahad ya sameni da maganar Amma Yana fada min nayi nazari na karbeta, dama Ina tunanin zuwa muyi magana Sega babban rabo ya Kara hada mu. Allah ya tabbatar musu da alkhairi!"

Ammi ta amsa da Amin sannan Suka koma zancen abinda Ammi zata na siyarwa, da kanta ta saka Ammi ta Bata hundred thousand cikin kudin da Baba ke Bata lokaci zuwa lokaci, ta Mata bayanin cewar zasu dinga zuwa Kano tana siyan atamfofi tana siyarwa maaikata karshen wata ta hada kudin ta, sannan ta fara online business. Ammah har yamma suna gidan mu, Kuma suna daki itada Ammi se dare suka tafi, washegari Yaya Fahad ya dauke mu zuwa Funtua ita Kuma Ammah da Ammi aka sauke su kasuwar kwari Dan a fara.


Naga opinion dinku so nayi deciding saka duka biyun, mutane since Yana refreshing dinsu da tuna musu good olden days, wasu Kuma sunyi complain. So from now on Zan saka duka biyun. Nagode da hakurinku!

Shatttzzzx

UWARGIDAN BAHAUSHEWhere stories live. Discover now