Tunda Paapa ya fara magana Hanifa ta daskare.. shin me Papa yake fadi?? asiri kenan Sadiq yayi mishi?? how can someone steal money from you sannan ga evidence nan and you still try to defend him??

"Toh yau zan fadi muku asali ko waye Sadiq" Paapa ya fada rai a bace.

Sadiq ne yayi saurin fadin "Please Sir, you don't have to.. mu bar maganan haka nan"

"No Son.. I told you tun farko muyi reconciling issue dinnan amma ka qi.. I think lokaci yayi da yakamata kowa ya san abinda yake faruwa"

Gani nayi Sadiq ya dafe kai yayinda yake ji kamar ya tashi ya falle Hanifa da mari..

Su kuwa Heads din sun natsu suna so su ji... Da alama dai su ma basu san komai game da Sadiq ba.. kawai sun wayi gari sun gan shi a matsayin ma'aikacin kamfanin..

Ni kuwa nace balle kuma ni da masu karatu... ah toh!!

"Abubakar Sadiq Bunza is the son of marigayi Abubakar Muhammad Bunza, Former Minister of petroleum na qasa mamallakin Bunza Oil & Gas wanda ya rasu shekaru kusan biyu da suka wuce"

Gaba daya dakin taron sai na ga kowa ya cika da mamaki yayinda ake ta kallon shi ana qus-qus.

Hafeez na ga ya sa ma Sadiq idanuwa shima cike da mamaki.. tabbas ya sani cewar Sadiq comes from a rich and sophisticated family domin kuwa yanayin rayuwar shi says it all.. toh amma bai taba sa ran cewar he is this stinking rich ba.. like he is such a simple, kind-hearted and down to earth kinda guy! Ta ya mutum yana da wannan matsayin a qasar nan zai zama this simple??

Hanifa ma zaro idanuwa tayi, qafafuwanta kuwa sun yi sanyi.. a sanyaye ta zauna kan kujerar ta yayinda ta sa ma Sadiq idanuwa..

Shi kuwa tunda ya dafe kai bai qara dagowa ba saboda takaici.

"da ni da mahaifin shi tare muka yi karatu a Stanford University a qasar America.. dukda a lokacin he was my senior, jinin mu ya hadu and we became best of friends. I studied business administration yayinda shi kuma ya karanci Petroleum Engineering. Bayan ya gama masters dinshi ne ExxonMobil suka bashi aiki and I am sure you all know that it's one of the best Oil & Gas producing Companies not just in America but in the world at large, Ya zauna a qasar America for over twenty years shi da iyalin shi... dukda ba qasa daya muke ba, abokantakar mu ta cigaba har lokacin da ya dawo Nigeria ya zo ya zama Minister of Petroleum na qasa.."

Girgiza kai na ga yayi sannan ya cigaba da fadin "Mahaifin Sadiq shine mamallakin Bunza Oil & Gas wanda nasan gaba dayan ku babu wanda bai san shi ba.. Kun sani cewar his business is beyond this country.. Ya rasu a sanadiyyar hatsarin mota da suka yi shi da matar shi (mahaifiyar Sadiq) akan hanyar su ta dawowa daga airport.."

Ya dan yi shiru tare da kallon Sadiq wanda kanshi yake a duqe har a lokacin sannan na ga ya dafa kafadarshi yace "Allah ya jiqan su da Rahama"

Gaba daya dakin taron suka amsa da "ameen"

"Me Sadiq yake yi a kamfanin nan?? na san dukkanin ku tambayar da kuke yi ma kanku kenan... idan bazaku manta ba wata goma da suka wuce Bugaje Industries yayi sinking wanda har ya kai mu ga shiga bankrupt.. dayawan ku kun sani cewar saboda haka ne aka kasa biyan salary dinku wanda har ya kai ga anyi downsizing ma'aikata.. We all saw it on the newspaper that I was about to sell the company in order to pay our debts until this gentleman showed up.."

Sadiq ya dago kai ya kalli Paapa yace "please Sir, is this necessary??"

"Yes it is son... na gaji da jin qananan maganganun da Baby take yi akan ka da yadda take wulaqanta ka... she needs to know cewar kamfanin nan was in a serious problem lokacin da take karatu a qasar waje and I was here struggling to send her pocket money, She needs to know cewar har ciwon zuciya na ya kusa zama ajali na if not for you that came to my rescue, she needs to know cewar kudaden da ake juyawa a kamfanin nan gaba daya da wadanda take spending naka ne... and yes yakamata ta sani cewar accusations dinta a kanka na ka saci kudi ka biya accomodation ba haka bane, she needs to know cewar you actually spent so much money to save her father's company..."

RAWANIN TSIYA | ✔Where stories live. Discover now