Part 3

82 3 0
                                    

Part 3

🇴🇲 🇳🇬 ❤️ AHALIN ABU ZAYYAD🇴🇲🇳🇬❤️

Baba ne ya leko dakin cikin fusata saboda ya koma ne ya samu bacci amma hayaniyarsa yasa suka tashi "wai ke ishrat bakyajin magana ne dan gidanku Gwaggo ba mahaifiyata bace kike daga mata murya" ya karasa magana yana kara bata rai cikin maganar ta mai kama da ta kuka ta bashi amsa '' baba cewa taifa ana sheka ruwan nan na fita na siyo mata fulawa naz... bata karasa ba yace to shine kika ce bazaki mara Kunya Gwaggo tace kaga kaga tsaya
"malam bazaka zo kana yi yarinya fada da safe ba ina ruwanka aiken dai ba nawa bane na fasa ai ba ita na haifa kai na haifa ko dan bakai nace kazo ka siyo min ba waina dai anfasa yi maza tafi dakinka wata kila ma zugoka akayi kazo kayi mata tijara " ta karasa taba huci Hakuri ya shiga bata yana Allah ya baki hakuri Allah ya huci xuciyarki kinji ki yafemin sai a sannan ta sakko tace to Allah yayi maka albarka ya juya yana mamakin halin babartasa  murmushi yayi kawai a ransa yace tsufa kenan ya daga labule ya shga dakinsa an dauke ruwa misalin 11 masu sana'a a gidan sai kokarin hura wuta ake Amarya ta dubi Mama cikin girmamawa tace "ina kwana" mama cikin fara'a ta amsa mata da "lfy lau kintashi lfy" Amarya tace lfy lau Yaya yau kinji mutanen naku ko Mama tai dariya tace inda sabo ai sun saba Allah dai ya cigaba da shiryasu ameen Amarya tace sannan Ta dubi mama cikin kulawa yau to me za adafa   tunda kinga an dauke ruwan mama ta amsa dacewa aikuwa ina da ragowar Garin tuwo a dakina Kawai ayi sabo tunda dumamen ba lallai ya isaba Amarya tace to shknn mama takuma cewa ko ina malam ya shga ne Haqibu dake tskar gda yace yana shagonsa  Mama tace oho to sannan tafara kwala kira Mariya !mariya!!mariya!!! Da gudu tafito tana mama gani ke kuwa me kike ina ta kiranki har sau uku baki amsa ba mariya mama ina hada kayan wankin mu nefa zan fara yi banjiba maria ta bata amsa Mama tace maza kije ki dakko wa amarya wannan garin na kusa da Drawer ta mariya tace to tare da juyawq zuwa dakin maman nata A lokacin Amarya ma har ta dora ruwan tuwon mama tace bara naje na gaida gwaggo Amarya tace nima dazun nashga tana lazimu muka gaisa Mama tace tofah!!! Bara na karasa dai cikin sallama ta dage labulen dakin Gwaggo ta saka kai a ciki gwaggo ce take kokarin boye abu a leda tana turawa kasan gado kira take yi ina zuwa ina zuwa bara... gani nan tace au maman yarace sannu to ai najiki kina ta kwayayato a tskar gida sai kace ba gdan musulmai ba kina kwadawa yarinya kira kamar  gdan yan farauta Mama da dama sun saba da halin gwaggo murmushi tai tace to ayi hakuri gwaggo an dena Ishrat dake gefen gwaggo Zaune tace mama ina kwna antashi lafy ya ruwa Mama cikin fara'a tace Ishrat din gwaggo lfy lau yau ba zuwa makaranta ne sunkuyi dakai tai tace ai ruwa ake Mama tace duk da hakan ai da kin daure kinji kwana nawa ne kema kingama karatun musha bikin ki Gwaggo tace ana makaka uban ruwan nan kike so tafita salon mura takama min ita din yar tilon yarinyar nan kudai wlh baku da imani mutan gidan nan sai kuwa Gwaggo tasa kuka tana ita dai tagaji da gdan nan komai aka tashi ace ishrat baza a bari yarinya ta huta ba bokon me ana ruwa yarinya aje tsawa ta fado mata (kunji gwaggo da rigima sai kace da ba itace zata aiki ishrat din ba ana ruwa) Gwaggo ta diga fyace majina tana share hawaye ishrat da ranta ya baci saboda kukan gwaggo tace kina kara kuka wlh bazani dake birnin ba in nayi aure kiyi min zaman daki dawo wa kauye zakiyi ki tacin koko babu ke babu cin indomi da kwai da madara ba shiri gwaggo cikin muryar kuka "to nadena" mama dai bata bar dakin ba sai da gwaggo ta hakura sannnan tayi wa  gwaggo alqawarin kwan zabi ta fita. Cikin kasa da murya Ishrat tace "gwaggo zaki rikani zance yau" murmushi gwaggo tayi sannnan tace to yau gun wa zaki gun samarin naki Murmushi ishrat tayi tace gun musa mai kanti mana Gwaggo tace wannan mai idon doddanin nan wlh bazani ba ran da muka hadu dashi a lungun gdan malamai ko taro bai baniba sai cikani yayi da magana ni ban zuwa da dai gun su wannnan yaron nan mai balangu ne da naje Ishrat ta murtuke fuska ta turo baki tace wai muttaka tabdi gwaggo nan ma fuskarsa fa duk tsagu naje na haifi yara munana gwaggon tace au Allah yar  bakinci dan ubanki tinkiyar kakar amaryar kika min bakin ciki nasamu to fah anyi walkiya na ganki to baki isaba mutumin nan in naje siyan nama yana ragemin duk so kike ya daina dan mugun halin irin naki Ishrat ta zunbure baki tayi gaba abunta Gwaggo kira take ishratu ! Ishratu!! Ishratu!!! Ishratu!!! Ko juyowa batai ba dakin mama tayi shigewarta  dan ba sosai take shga dakin Ishrat na shiga dakin mama ta tarar da Rabi da mariya suna karyawa Murmushi tayi musu tace bara na wanko hannu Mariya tace yar gdan Gwaggo kina yanda kike so Ishrat da take wanke hannu ta kofar daki tace kedai bari ina fama wlh gara ma mutum yayi aure ya bar gidan nan ko ya huta da tsohuwar nan Rabi tace kanku akeji ji ni yanzu bayan babbar Sallah na zama ta Isiyaku gaba daya suka saka dariya A dakin mariya ta dubi ishrat tace nifa har yanzu salaha bata gamai min dinki na ba wai rannnan da naje cewa tai landing ne bata samu ba sai taje bichi kuma nan da bichi minti nawa ne kawai dai bata so tagama Min akan lokaci dama ta saba batawa mutane lokaci Rabi tace yo ko ni ya mikai da ita akan ankon yar Gidan malama zaharau ai da uwaka ubaka muka rabu kema maganinki kenan ga Shagon isiya nan ya iya dinki na zamani minti nawa kinkai me ke kinfi son mace tayi miki Ishrat da tagama hadiye loma tace nima dai gun isiya wlh nake kaiwa kinsan sauryain usaina ne ta gidan baba Sani Mariya tace wannan mai kule kulen yan matan jaraba ai ko ni yace yana so fuskace bai gani ba Rabi da ishrat suka tafa ko kuma Ajinki ya raina  Mariya tace shi ya isa yace ya fini aji kallani fa dirarriyar mace yar gayu Haba mai zanyi da wani isiya mai dinki Rabi tace kanki a keji Nan suka gama cin abuncin suka fito suka taya Mariya wanki daga nan itama Ishrat dinta debo nasu suka wanke ana cikin wankin baba ya shgo ya tarar da iyayen yaran suna zaune gu daya suna hira sukuma yaran suna wanki wani dadi ne yake kara ziyartar zuciyar sa yanda yaga kan iyalinsa a hade Murmushi yayi musu yayi musu addua ta alheri ya shga dakinsa ya dakko wasu garin maguna ya fita. Da daddare gwaggo dama tun yamma tayi wanka ta shafa mai ta shrya cikin wata atamfartar Mai ja da yellow ta sha daurin dankwali kafar nan ta mulke ta da man shafawa mai gurguwa Duk abunda take Ishrat na sane da ita banza tayi mata Bayan maghriba Gwaggo ta leka dakin mama tace ishratu zoki rakani inje inyi barkar nan Ishrat dake aikin makaranta tace Gwaggo ki dauki mami mana ko mariya kuje Ni ba aiki nake yi ba Gwaggo tace kunji mu da yarinya shehu !shehu!! Fito to  Ga Ishratu nan nace tazo ta rakani barka tace ita Allahn ta daya bazata ba rakani barka ba to kai zo ka rakani baba dai ransa bai so ba ya fito yace "haba Gwaggo dazu da safe ina wa yarinyar nan magana kikace ga zance ga magana kika tsatssare yanzu kuma taku ta hado ku kinci kaza kince kaza ni ban san ya kike so nayi ba to " Au kaima haka zakace ni naga takaina Mutan gida shehu shehu ashe da raina zanga haka Oh ni cikin kufula baba yace "ke tashi kije ki rakata " ya juya fuuuu yayi dakinsa babu musu Ishrat ta rufe littafinta a zuciyarta tana adduar Allah yasa santsi ya kwashi gwaggo ta zame ta fadi a hanya "Zaki sauri ne ko sai na kira shehun" Gwaggo ta tambaya Hijab kawai tazaro daga jikin Igiyar wanki tace muje Gwaggo na gaba da yar torch light dinta ishrat na binta a baya a hanya suka dinga wuce majalisar mutane dai dai majalisar inda su mai gari suke zama shida mutanensa in dare yayi dayake ana  tada inji dai dai gun Gwaggo tafara sake tafiya tana cillara kafarta a hankali ishrat da dariya takamata tace Gwaggo mene haka kuma Banza gwaggo tayi da ita sai da sukaje barka suka dawo bayan sun wuce majalisar su mai garin  Gwaggo taja hannun Ishrat tace ma a kunne baki ga yanda mai gari take bina da kallo ba Ishrat a ranta tace innalilahi yau kuma meke damun gwaggo mai gari kuma yake kallonta Ishrat ra a bace dayake duhune Gwaggo bata ganin fuskarta sosai Ishrat din tabata amsa da eh inaga sonki yake yi ko wannan wanka da kika sha haka ko matan mai garin sai gaka Gwaggo akai dariya tace dadi na dake yar nan akwai hankali da hangen nesa Maza ga wata Dari nan kije ki kashe Ishrat akai dariya akace Gwaggon mu Gwaggon mu Ina sonki wlh ai wlh kece zaki min yar zaman daki a gidana Gwaggo tace sha kuruminki yar nan sai kinyi haihuwa Goma zan dawo Ishrat tace Goma Gwaggo wlh sati daya Gwaggo tace kin isa ma ga kuguna ga naki Ishrat tace ai bake za'a aura ba ni za a aura Gwaggo tace koma dai mene Gwaggo tace ishrat anya bazmubiya ta gun mai balangun nan baki nasiya ko na dari biyu ne Ishrat tace ni wlh gda zani gara ki aiko su haladu dan yanzu karnukan black wlh suna nan kuma fa kinga garin da sanyi kowa ya dauke kafa ana gida Gwaggo tace to mu tafi dai Allah ya kiyaye ameen ishrat ta amsa suka jera da Gwaggo suka shga gda shgarsu keda wuya baba ya shgo da bread dinsa ya rufe gda suka kwanta bacci.


Fayruz dakinsa ya shiga wanda kyau da tsaruwar Dakinsa har yafi na yareema Azeez na cikin littafin *UWAR SARKI* kyau komai na dakin golden color ne katon bathtub ya shga ya hadawa kansa ruwa wanka yayi ya ya taje kansa ya dakko farar jallabiya ya saka ya fito falon Murmushi yayi tare dacewa AMMI nagama janshi tayi taje ta aje shi akan kujera Shayin Gahwa ta fara bashi yasha sannan ta shga serving dinshi tana bashi abinci a baki cikin so da kauna take kallon yaron nata Murmushi yayi mata yace Ammi wannan kalon fa jan hancinshi tayi tace na So ne Abun kaunata dariya yayi yace A duniya babu mahaifiyar da tafiki cikin harshen larabci duk suke wannan maganar Alh Zayyad ne ya sakko daga bene Ya dubi Fayruz yace Mr president na nemanka yasan zaka dawo da dashi zamuje ma so sai abubuwa suka rikeshu yakamata inka huta kaje ku gaisa Alhj zayyad ya karasa maganar yana gyra hiramin kansa tom yace sannan Alh zayyad yayi  yayi gaba Ammi tace Fayruz kai dawa zauje to dan tunani yayi sannan yace Da Hammad zamuje (cousins dinsa ne hammad baban Hammad kanin Alh zayyad ne wato zaid) Ammi tace ni banma gasa ba bai san kadawo bane Murmushi yayi yace yasani amma baya nan ne yace min yaje lagos amma yana hanya ina jin ma ya karaso tunda flight ne aikuwa bai su gama rufe baki ba sai ga Hammad da gudu ya shgo falon yanacewa "habibi aina habibi"(masoyi ina masoyi) kunsan larabawa ba ruwansu bakamar hausawa ba Fayruz cikin dariya ya mike yana cewa "akii sadiqi habibi "(dan uwa aboki masoyi) nan suka rungume juna suka gaisa sosaii sannnan ya dubi Ammi yace lah ammin mu kina nan dama Murmushi tayi tace dama ina zaka ganni kana ta danuwanka Murmushi yayi yace lah wlh bahakabne ai nafi sonki akanshi Ammi tace ba wani nan da dakazo meysa baka nemeni ba sai shi Fayruz yabata rai cikin wasa alamar kishi wai dukansu Hammad ya rungumo yace ai ina sonku duka (hammad mutum be mai barkwanci da wasa yana da son mutane sosaii ) Shima yayi joining Fayruz gurin cin abinci bayan sun gama ne Fayruz yake gaywa hammad cewa da daddare zasu shiga Aso rock gidan shugaban kasa zai gaidashi Hammad yace "bakomai jiya ma muna tare da Fadeel dansa a The George Lagos Hotel munje wani conference Fayruz yace ayyah sungama cin abinci suka shga dakin Fayruz.
Fayruz ya samu guri ya kwanta shikuma Hammad ya kunna kallo yanayi sai zuwa magriba Fayruz ya tashi suka alwala suka fita massalacin gidan gaba sukai sallah suka dawo daga nan Ko wannensu yayi wanka ya tunkari Aso Rock gidan Shugaban kasar nigeria Wato His excellency Alhaji Bashir Abdulqadir his excellency Alhaji Bashir abdulkadir yana da mata daya hajiya maimuna sai yara biyu Adeel da Khairat shima Allah bai bashi haihuwa da wuri ba sai daga baya Adeel sa'an su Fayruz ne kuma makaranta daya sukai primary da secondary Itakuma khairat itace mai bin adeel din tsirarsu shekara uku ne.
Khairat na mutuwar son Fayruz Khairat ce ke waya tanacewa ina son Fayruz kamar raina  nakuma kudiri aniyar cewa ko sama da kasa zasu hade ko za ayi balbalin bala'i ko za a dinga ruwan masifa wallahi bazan  hakura da Fayruz ba komai zai faru sai dai yafaru haka naji Khairat tana gaywa wata aminiyarta mai suna Hafsat yar gidan sarkin zazzau a waya.

AHALIN ABU-ZAYYAD🏘✈️Where stories live. Discover now