Part 2

104 4 0
                                    

Part 2

🇴🇲 🇳🇬 ❤️ AHALIN ABU ZAYYAD🇴🇲🇳🇬❤️

Bayan wasu shekaru Gidan Abu zayyad ya cika da jama'a duk inda ka duba fararen fata ne keta hada hada a gidan Shi uban gida kuma jagoran wannan Gida Allah yayi masa rasuwa shekara uku da suka wuce inda shima sarkin oman din ya rasu wanda yake rike da sarautar oman din kuwa mijin Arzina ne wato mai martaba sarki bahar wanda yake kani ga sarki mai mutuwa.Arzikin AHALIN ABU ZAYYAD ya kara yawa duk inda ka keta a duniya suna da shares banda companies da wasu abubuwan har ana lissafa su na 6 a family na masu kudin duniya. Yanzu wanda ya kasance yana jagorancin companies din Abu zayyad shine Zayyad bn Abdulrahman bn sulaiman Al kusari bara muji a bangaren kowanne ya iyalinsa suke bara mufara da gidan Alhaji zayyad bn sulaiman Alhaji zayyad Allah ya albarkaceshi da samun yara hudu maza biyu mata biyu inda mai sunan mai haifinsa shine babba wato ABDULRAHMAN suna kiransa ABHI sai MAHRA wacce tayi aure a oman din sai sara wacce take karatu sai kuma dan auta kuma babban tauraro abun so ga duk dan wani AHALIN  ABU ZAYYAD sanyin idaniyar marigayi Abu zayyad  wato FAYRUZ
Yaro farin balarabe kyakkyawa ajin farko yana da saje dogo amma bashi da gemu pink lips kuwa ba a magana indai ana maganar kyawawan idanuwa shiru ake dan idanuwansa daga nesa zaka iya cewa kamar blue eyes ne dashi a tsaye yake ga 6packs suna shirin fitomasa tunda a shekarun samarta yake FAYRUZ bai wuce shekara 23  ba duk wasu shika shikan girma sun fito masa ya gama karatunsa na pharmacy yanzu dai ya zama cikakken pharmacologist. Sai kuma gidan zaid yana da yara biyu mace da namiji akwai mai sunan zaid din sai kuma macen sunan ta Hamra itakuma matar sarki wato Arzina bata haihuwa da wuri ba sai daga baya Allah ya bata ya mace guda daya suna cemata NUR wato hasken iyayenta bata wuce shekara 17 ba saboda har iyayenta sun cire rai da haihuwa Allah ya basu ita babu wani asibiti da basuje ba amma shru sai daga karshe Allah yasa suka haifeta NUR kyayyawace ajin farko wanda indai ana maganar kyauwa ne a matan zamanin nan indai akace NUR anrufe bakin yaro saboda mujjalun duniya ma kansu kara kuranta kyawunta suke itama kusan duk hutunta a nigeria takeyi a abuja inda estate din family din nata yake wato ABU ZAYYAD ESTATES. Sai yan uwan (kannensa) ABU ZAYYAD wato ahmad othamn da khaleed suna nan suma kowa da ya'yansa harda wasu ma harda jikoki kafatanin wadann iyalai suna nan a kiyayence da dokar Mai GIDA ABU ZAYYAD kuma kasancewqrsu a nigeria yasa sunji hausa sosai saboda suna zuwa kano kallon hawan sallah a gidan sarki kuma suna business sosai a kano da wasu sassa na nigeria suna kurdawa kuma ga taimako da suke da shi ta kowanne bangare asibiti ne massalaci da gina makarantu fisabillilah amma dai kam aure ne su auri bqkar fata ko fadar hakan a baki ma sabo ne a gurinsu bare ma mutum ya ce zai yi shysa ko karatu ma oman din ake akaisu suyi bayan sun gama primary da secondary a nigeria kuma duk makarantun na gidan su ne malaman ma rabi larabawa rabi turawa da kuma hausawan mu yazamana cewa private school din tasu itace private school mafi tsada da kyau a west Africa tana da mazauni a Abuja sunan Makarntar OMAN-NIGERIA ACADEMY makarantar tayi shura sai ya'yan manya da attajiran kasa da kusoshin gwamnti dan hardaga wasu kasashen ana kawo yara.

Yau  FAYRUZ zai dawo daga makarantar sa inda ya gama wato IMPERIAL COLLEGE LONDON ko ina ka duba gidan ana ta aikace aikace ma'aikatane ta kowanne bangare babu abunda kake ji dai tashin abincincika kamar su SHUWA DA OMANI BREAD,KEBAB DA SHAYIN GAHWA  kai dama wani kalar abincin da ban san shi ba AMMI sai kai kawo take wato mahaifiyar FAYRUZ kuma mata daya tilo Ga Alhaji ZAYYAD asalin sunanta ARZINA (kuma tana da ya' mai sunanta Arzina babar NUR) itama jinin sarautar Oman ce dan kakanta yayi sarkin oman Mahaifin FAYRUZ dakansa tare da wasu abokansa yan nigeria masu kudi sukaje dakko FAYRUZ daga makaranta anyi graduation lafy Fayruz ya karbi best students sun dakko hanya a jirginsu ta dawo wa gida cikin harshen Turanci ALHAJI ZAYYAD ya dubi FAYRUZ cikin kulawa yace masa yanzu aikin pharmaceutical company da mukeyi a kano ya kusa kammala dan anyi kaso 90 cikin dari  kaga sai kafara shiri cikin murmushinsa mai kara masa kyau yace ABI (babana) Allah ya kaimu to Amma dai duk ansaka mun abunda nake bukata ko yaron ya tambaya cikin yar damuwa Alhaji zayyad ya bashi amsa cikin murmushi yace "duk abunda ka bukata na kowacce bishiya kusan zan ce ansaka maka a company din kai dai aikin ka kayita research kana binciko mana yanda za ayi amfanin da tsirrau gurin kirkiro sabbabin magunguna kaji yaron Kirki" Fayruz yayi murmushi cikin jindadi tareda rungumo mahaifinsa cikik Harshen larabci yace "wallahi anna uhibbuka ya abhi" (wallahi ina sonka ya babana) cikin kauna ta da da mahaifin Alhaji zayyad yace "ana uhibuka kaseeran ya sahibul kalb" (ina sonka da yawa ya ma'abocin zuciyata) cikin bansha'awa wadanda ke cikin jirgin suke dubansu suna mamakin irin wanan kaunar ta da da mahaifinsa.After some hours suna cikin jirgin sukayu landing a gida nigera a babban filin tashi da saukar jirage na babban birnin tarrayar nigeria Wato Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja anan ne inda tarin motocin su da zasuyi musu convoy suke jiransu bayan sakkowarsu daga jirgi aka bude musu kofofin motocin suka shiga Alhaji zayyad da Fayruz mota daya suka shiga kirar Mercedes benz mai suna Maybach s600 suka dauki hanya sai mansion dinsu ana tayi musu jiniya.

AMMI ce da sauran yan gidan A harabar gidan suna jiran karasowar su saboda suna shigowa nigeria Alh zayyad ya kirata ya shaida mata sun iso karasowarsu ke da wuya ammi tayi waje motar dan nata yana fitowa ya fada jikinta ya rungumeta yana shagwaba itakuma sai lallashinsa take cikik harshen larabci tanacewa "yi hakuri autan mamansa yaron da ya gagari yaron kowa balarabe dan larabawa Allah yayi maka Albarka" nan gurin aka amsa da ameen yabi kakkaninsa ya rungume da uncles dinsa da sauran cousins dinsa maza da mata aka gaggaisa ALH ZAYYAD yace to a shga gda bai kamata a tsaya a waje ba cikin salo na bada umarni ba musu suka shiga kamar yanda ya umarta nan ya tsaya harabar gidan sukai sallama da bakinsa da suka rakashi dakko FAYRUZ din gefe na hango wani sanatan yobe ta tsakiya sai kallon matan larabawan nan yake amma ina sun yi masa nisa.Bayan shigar su cikin gida AMMI tace "muje kaci abinci ko " shikuma cikin harshen larabci yace mata 'urid 'an 'astahima alan (ina so ne zanyi wanka yanzu) cikin murmushi tace "bakomai habibi ai angyara maka dakin naka" murmushi kawai yayi mata ya wuce.

KANO STATE BICHI LOCAL GOVERNMENT
Garin  BADUME

MALAM SHEHU MAI MAGANIN GARGAJIYA haka naga an rubuta jikin wani allo an dora saman wani shago jikin wani gida ga dukkan Alamu mai shagon shine mai gidan babu laifi gida ne namasu rufin asiri tunda anfi karfin cin yau dana gobe kuma ana yiwa kai suttura ana biyawa yara kudin makarnta duk da makarantar ta gwamnati ce.Gidan sa babban gida ne matansa guda biyu duka suna zaman lafiya ba ruwansu kuma ko wacce tana sana'a sannan mahaifiyarsa tna gidan itama da nata dakin sai kuma dakin yara maza ALH SHEHU MAI MAGANI yana da yara maza guda  7  uku daga mazan (SANI,AUWAL,SALISU)suna boarding sukuma sauran mazan biyu (MUNTARI SAI HALADU)suna fce bichi biyun(HAQIBU DA RIDWAN) kuma kanana ne sai kuma bangaren yan matan yanada yara mata guda biyar MAIMUNA itace babba sai RABI  sannnan MARIYA sai ISHRAT sannan kuma auta MAMI (asalin sunanta SUWAIBA sunan babar alh shehu)

matan gidan kuma Asma'u itace babba suna ce mata MAMA sai mai bi mata itace Hauwa'u suna cemata AMARYA.

MAMA(wato uwar gidan )yaranta 8 MUNTARI,HALADU,MAIMUNA(tayi aure a kauyen tsaure)RABI,MARIYA,SALISU,AUWAL,RIDWAN.
AMARYA yaranta 4 ISHRAT itace babba sai SANI sannan MAMI sai kuma HAQIBU gidan babu laifi yaran suna da kyau sosaii ko wacce da iya nata kyau amma yaran amarya sunfi kyau dan ita bafullatanace ya aurota ne daga gombe  a wata local government maisuna Balanga.amma a cikin yaran Amarya ISHRAT tafisu kyau sosaii tanada  boyayyaen kyau saboda sai ka kura mata ido zaka gane kyawunta   tana da dara daran idanuwa gashinta babu laifi, tana da yalwar gashin gira amma kuma jikinta mai kyaune sosaii tana da cikar jiki bakinta dan madai daici ammafa ISHRAT "BAKA CE" amma ba sosai ba dan bakin nata bamai duhu bane mai haske ne jikinta dai irin na yan matan ethopia ne su basa layin bakake kuma basu kai a ce musu farare bah shekararta 16 amma saboda jikinta sai kadauka wata yar 17 ce kuma kawayenta ma kusan ba sa'ointa bane sun girmeta ISHRAT akwaita da wayo da iya yi irin na yan mata Akwai dai Lafiyar kwadayi da son cin dadi a dakin kakarta take rayuwa wacce suke cewa Gwaggo.
Yau antashi da ruwan sama a garin gwaggo ce cikin fada na tsofaffi ke ISHRATU bata iya cewa ISHRAT Ba sannnan akwai masu cemata ISHRA.
Ke ishratu ba magana nake miki ba bazaki tashi ba gwaggo ta karasa maganar tana huci ISHRAT da tun kiran farko taji gwaggo banza tayi da ita''
Da taji  kiran yaki ya kare ne yasata bude ido a fusace ke gwaggo nan mutum yana baccin sa zaki tashe sa ke baki san ruwa ake ba kowa yana can yana bacci sai mu dan munfi kowa zamu tashi Gwaggo ta rike baki tana ke yar nan anyi yar kusun uwa yo ina ruwan mu da wasu cikin sassauta murya tace dama wai so nake ki tashi ki siyo fulawo kizo kiyi mana wainar fulawa (gwaggo fa akwai kwadayi) Aikuwa ISHRAT ta dire tace wlh ana ruwan nan bazata fita ba Gwaggo ma ta karbe dacewa wlh sai kin fita nan da shagon lawali da kin leka gaya nan ya fito musu suke tayi da gardama inda sabo dama sun saba kullum cikin rikici suke amma kuma ba damar ka shiga fadansu wani lokacin ne ma baba yake tsawatarwa ISHRAT din kuma ko da yaushe idan ba yan fadan bane zaka gansu suna kuskus komai nasu sirri ne dai sabida idan samarin ISHRAT suka kawo mata abun dadi da gwaggo suke haduwa su cinye ko unguwa Gwaggo zata sai da ISHRAT komai dai gwaggo tasamu ishrat dan tafi son ishrat  a cikin jikokinta tanacewa yarinyar ruwan arziki ne da ita tunda da damuna aka haifeta  ranar kuma ansheka Ruwa.

AHALIN ABU-ZAYYAD🏘✈️Where stories live. Discover now