II

1.1K 186 8
                                    


UWARGIDAN BAHAUSHE

II

✍️ AYSHATUUU

Ammi na makaranta Bata ma San wainar da ake toyawa ba a gida, tsam da ranta tana can tana karatu with the high hopes of ta gama karatun ta  ta Zama abinda a karamin garin su zata Zama abinda kowa zaiyi alfahari da ita, musamman dake girl child education is not that rampant a wañnan lokacin.

Idan da zaa tambayeni Zan iya cewa worst feeling shi ne kaga an Yi maka katsalandan a cikin rayuwarka, duk da dai ya halatta ka zabawa yarka Miji but ba wai kayi forcing dinta cikin auren Wanda Bata taba gani ba. Bayan auren seda aka Kara sati har bakwai kafin akai ma su Ammina hutu, irin wannan farin cikin da kake ji cikin rayuwarka, daga wannan term din zakai waec shi kenan ka Gama secondary School gaba ki daya! Tunda ta shigo gida taji ta so different ba kamar ko da yaushe ba, ta Saba idan ta dawo Babu inda mahaifiyar ta ke zuwa, zasu kule daki suyi ta hira musamman idan Bata da girki ranar, Amma wannan Karan Kam tunda Suka gaisa se mahaifiyar ta ta fice zuwa tsakar gida tana kirkiro ayyuka duk Dan kada su kadaice balle ta Mata wata tambaya.

Can yamma Ammi ta samu Mahaifiyar ta a tsakar gida tana zaune Babu abinda take se kallon yaran gidan dake shige da fice da kuma wasanni a tsakar gida, dan Babu karya suna da yawa a gidan ita dai kadai ce a gurin mahaifiyar ta! Gefen ta ta zauna tace

" Baba ya Kika zo nan Kika zauna kuma? Kin barni ni daya kawai a daki"

Kallonta tayi da murmushi tace

" Dakin ne zafi"

Da mamaki Ammi ta kalleta jin amsar data Bata amma se Bata Kara magana ba kuma, Daga nan Suka fara hira sosae kowa Yana wucewa Yana kallon su masu dariya suna dariya, masu yada magana nayi, idan da sabo sun riga da sun Saba shiyasa Ammi Bata kawo komai ba. Wajen sallar maghrib gidan ya sarara da hayaniya kowa ya koma daki, Ammi ta dakko fitilar kwai ta kunna sannan tayi sallah,

" Baba shiru har yanzun Alhaji Bai dawo ba"

Yace Mata

" Zai shigo yanzun inshallah, yi kokari kiyi wanka dai"

Ta mike ta zo tsakar gida ta ja ruwa a rijiya ta Kara da Wanda Baba ta Bata na zafi, tun tana bandaki take jin maganar Alhaji, ta dinga murna har ta fito sede baya tsakar gida Yana can dakin innah uwar gidan su. Dakin taje ta tarar Baba ta fito Mata da wata atamfa me kyau, se kanshi kayan sukeyi. Kallon kayan tayi da alamar tambaya tace

" Baba wannan kayan Zan saka? To nida zanyi bacci ma"

Da yake dakin Babu yalwar haske sosae shiyasa Bata ga yanayin dake fuskar Babar tata ba, tace

" Ki saka kawai"

Bata Kara cewa komai ba ta saka kayan ta zauna gefen gado, Bata Jima ba taji sallamar Alhaji, cikeda murna ta Mike tana ta murmushi yace

" Alhaji sannu da dawowa"

Shima murnar yake yace

" Uwata ta kaina, ya makaranta?"

Suka zauna tana ta bashi labarin extra couching da ake musu na waec, seda ta gama sannan Shima ya fara Mata nashi bayanin, tunda ya fara Mata maganar yarda da kaddara taji kawai atmosphere ta Zama dull, gabanta Yana ta faduwa, seda ya gama sannan ya fada Mata ya Mata aure. Dukkansu tunani suke irin ihun da zatai Amma se tayi murmushi kawai tace

" To Alhaji nagode Amma Zan karasa secondary Dina?"

A farko baiyi wannan tunanin ba, dan shi numfin shi ta kammalla karatu kenan, Amma ganin yadda ta bashi hadin Kai yasa yace Mata ya Mata alkawari. Ya sanar Mata mijin nata Yana Hanya zai karaso kowanne lokaci Yana faata su sasaanta Allah ya Mata albarka. Daga haka ya fita zuwa masallaci, tabbas a zuciyar ta taji Babu dadi Amma kuma ita dama ba saurayi gare ta ba balle ta damu, wannan lokacin babban burinta karatun ta, to tunda Bai taba Mata karatun ta ba ai komai me sauki ne. Baba ta Mata nasiha itama sannan sukai sallah, baa Jima ba yayanta yazo yace taje Alhaji na Kira ta, anan gabanta ya dinga faduwa tana tunanin yadda zai amshe ta, karfin gwiwar da Baba ke Bata yasa ta yafa mayafin dake kanshi ta fita, a kofar gidan ta same su akan tabarma suna gaida Alhaji, Yana ganin ta ya Mike ya Basu guri tunda waje ne bazai yiwu yayi musu nasiha ba se yace su shiga ciki su same shi. A sitting room din shi Suka zauna yayi musu nasiha sosae sannan ya fita, lokacin ne ta gaishe su tana sunkuyar da Kai. Abokin shi yace

" To Babandi kayi shiru, Amarya ga Angonki na kawo Miki shi"

Batace koami ba, ganin hakan abokin ya fita se lokacin ya samu ya daidaita kanshi ya fara Mata magana, a hankali take amsawa a karshe yace Mata

" Bazan taba manta hallacin da kikai min ba, a gurina Zaki Zama tauraruwa wadda hasken ta bazai taba gushewa ba"

Inaga Ammi ba zata taba manta wannan maganar ba, saboda halfway Baba ya cika alkawarin but along the way se ya karkace, na kan so yiwa Baba uzuri Amma wani lokacin se naji na gagara, zuciyata na kuncin yadda ake yiwa uwata Abu.

Har cikin gida Suka shiga ta raka shi dukka dakuna abokan zaman Baba, ya gaishe su sannan ya dawo dakin Baba ya gaishe ta cikin mutunci da karammawa da kuma bada girma. 

Tunda ya tafi Inna ta tada masifa tsakar gida akan Alhaji ya cuce ta yasan tana da Yara Mata da suka Isa aure Amma ta rasa dawa zai hada auren seda Ammi, ta dinga masifa bayan yasan gidan hutu ne, Babu Wanda ya kulata cikin su Ammi se sauran Yan koronta shikam Alhaji ko kallonta baiyi ba.

Baa dauka lokaci ba aka yanke ranar yini, akai biki sannan suka dauki amaryar su Suka kaita gumel, anan akai biki na gani na fada sannan aka watse taro. A gidan su Baba Ammi ta kwana se da sukai sati daya sannan Suka shirya zata koma katsina inda yake aiki!

Shatttzzzx

UWARGIDAN BAHAUSHEWhere stories live. Discover now